WANI MALAMIN DARIQA YA BAYYANA KUSKUREN MALAMAN DARIQA A NIGERIAWasu Malaman Dariqa a Nigeria suna kafa hujja a kan Bidi'o'insu musamman Maulidi, da cewa: Abu ba zai zama Bidi'a ba har sai an samu hani a kansa a Alkur'ani ko a Hadisi. Har ka ji suna cewa; a kawo musu inda aka ce kar a yi abin.Ma'ana dai su ba su yarda da Sunna ta bari ba (السنة التركية). Su ba su yarda wani abu a Addini ya zama Bidi'a ba har sai an samu wata Aya ko wani Hadisi da ya yi hani a kan shi wannan abin da suka kirkira suke aikatawa da sunan Ibada. Wannan ya sa da zaran ka ce musu abu kaza Bidi'a ne, sai su ce maka: Kawo inda aka hana yinsa.To alal hakika wannan jahilci ne, saboda duk wanda ya fahimci ka'idojin Ilimomin Addini - hatta cikin Malaman Dariqa - kamar ilimin "Usul Fiqh" za ka samu suna tabbatar da cewa; duk abin da Annabi (saw) bai yi ba, alhali akwai sababin yin abin a zamaninsa, kuma babu wani uzuri da ya hana yi to wannan abu ya zama Bidi'a.Don haka babu mai jayayya a kan haka sai jahili, wanda da a ce: zai yi shiru da sabani ya ragu.To wannan jahilci da wasu cikin Malaman Dariqa a Nigeria suke yadawa, cewa; abu ba ya zama Bidi'a a Addini har sai an samu dalilin da ya yi hani a kai karara, an samu wani babban Malamin Dariqa inda ya yi magana ta Ilmi, ya yi musu raddi.Haka Malamin ya yi musu raddi a wata maganar da suka makalkale mata, wato ra'ayin nan na kasa Bidi'a zuwa kashi biyu:1- Bidi'a kyakkyawa.2- Bidi'a maras kyau.Wannan Malami da ya yi ma 'yan'uwansa Sufaye raddi shi ne Ibnu Hajar al-Haitamiy al-Makkiy. Ga maganar Malamin kamar haka, inda ya ce:((إن البدعة الشرعية ضلالة كما قال - صلى الله عليه وسلم -. ومن قسمها من العلماء إلى حسن وغير حسن فإنما قسم البدعة اللغوية. ومن قال "كل بدعة ضلالة" فمعناه البدعة الشرعية. ألا ترى أن الصحابة رضي الله عنهم والتابعين لهم بإحسان أنكروا فرضية غير الصلوات الخمس، كالعيدين وإن لم يكن فيه نهي. وكرهوا استلام الركنين الشاميين، والصلاة عقيب السعي بين الصفا والمروة قياسا على الطواف. وكذا ما تركه - صلى الله عليه وسلم - مع قيام المقتضي فيكون تركه سنة وفعله بدعة مذمومة.وخرج بقولنا: "مع قيام المقتضي في حياته" تركه إخراج اليهود من جزيرة العرب، وجمع المصحف. وما تركه لوجود المانع كالاجتماع للتراويح، فإن المقتضى التام يدخل فيه المانع)).الفتاوى الحديثية لابن حجر الهيتمي (ص: 281)((Lallai Bidi'a ta Shari'a bata ce, kamar yadda Annabi (saw) ya fada. Amma cikin Malamai wanda ya kasa Bidi'a zuwa Bidi'a mai kyau da Bidi'a maras kyau, shi fa Bidi'a ta Lugha yake nufi. Amma wanda kuma cikin Malaman ya ce: kowace Bidi'a bata ce, Bidi'a ta Shari'a yake nufi.Shin ba ka ga Sahabbai da Tabi'ai ba ne, sun yi inkarin farlancin duk wata Sallah ba guda biyar din nan ba, kamar Sallolin Eidi biyu, duk da cewa; babu Nassin da ya yi hani a kan haka?Haka kuma suka karhanta shafan rukunai guda biyu da suke jikin dakin Ka'aba, masu kallon setin Shaam, kuma suka karhanta yin Sallar Nafila bayan gama Sa'ayi tsakanin Safa da Marwa, wadanda aka yi kiyasi a kan Nafila bayan dawafi (sun karhanta wadannan duk da cewa; ba wani Nassi aka samu ya yi hani a kai ba).Haka duk abin da Annabi (saw) ya bari bai aikata ba, tare da cewa; akwai sababin aikatawan a zamaninsa, to barin wannan abin ya zama Sunna, aikata shi kuma ya zama Bidi'a abin zargi.Cewa da muka yi: "Tare da samuwar sababin aikata abin a zamanin Annabi (saw)" barinsa ga fitar da Yahudawa daga "Jaziratul Arab", da barinsa ga Tara Mus'hafi a wari daya, da kuma abin da ya bari saboda an samu wani uzuri da ya hana yi, kamar Jam'in Sallar Tarawihi sun fita daga cikinsa. Saboda a kan iya samun wani abu da zai hana samuwar aiki ya shiga cikin cikakken sababi da yake lazimta samuwar aiki sai ya hana samuwar aikin)).Ka ga sai Malamin Dariqar ya yi raddi ga Malaman Dariqa, wadanda ba su san me ake nufi da Bidi'a ba, inda ya nuna musu abubuwa kamar haka:1- Shi fa kasa Bidi'a zuwa kashi biyu; Bidi'a mai kyau da maras kyau, ana fadinsa ne a Bidi'a ta Lugha ba ta Shari'a ba. Wato kirkiran abubuwa da suka shafi al'amuran rayuwa, ba wadanda suka shafi Addini ba.2- Bidi'a ta Shari'a, wato abubuwa na Ibada da Akida wadanda aka kirkira aka shigar da su cikin Addini ita kam bata ce gaba dayanta.3- Wannan ya sa Sahabbai da Tabi'ai suka yi inkari, kuma suka karhanta wasu aiyukan Ibada saboda Shari'a ba ta zo da su ba. Wadanda ya ambaci misalansu, kamar yin Nafila bayan Sa'ayi tsakanin Safa da Marwa.4- Haka kuma duk abin da Annabi (saw) ya bari bai aikata ba, kuma a zamaninsa akwai sababin da zai sa a yi wannan abin, kamar Maulidi, tun da sababin yinsa shi ne Son Annabi (saw), amma duk da haka bai yi ba, kuma babu wani abu da ya hana a yi, wannan shi yake nuna barin Maulidi Sunna ne, yinsa kuma Bidi'a ce abin zargi.5- Amma abubuwa da ba a samu sababin yinsu a zamanin Annabi (saw) ba, kamar koran Yahudawa daga "Jaziratul Arab" da Tara Mus'hafi, ko kuma abubuwan da an samu sababin amma sai kuma aka samu wani dalili da ya hana a yi su, kamar Jam'in Sallar Tarawihi to su kam ba a kiran aikata su da sunan Bidi'a a Shari'a. Kai, wasu daga cikinsu kam Sunna ne ma, kamar koran Yahudawa daga "Jaziratul Arab", da Jam'in Sallar Tarawihi. Sauran kuma sai su zama "Maslaha Mursala".A takaice dai ya bayyana mana cewa; Malaman Dariqa a Nigeria, masu cewa; abu ba zai zama Bidi'a ba har sai an samu Nassi ya yi hani a kan aikata wannan abin maganarsu jahilci ce.Haka masu kasa Bidi'a gida biyu mai kyau da maras kyau, su ma ya kamata su san cewa; wannan ana magana ne a kan Bidi'a ta Lugha ba ta Shari'a ba. Amma Bidi'a ta Shari'a kam, wato kirkiran wata Ibada ko wata Akida a cikin Addini bata ne. Saboda Addini ya cika tun zamanin Annabi (saw). Duk abin da bai zama Addini a wancan lokacin ba, ba zai zama Addini a yau ba. WANI MALAMIN DARIQA YA BAYYANA KUSKUREN MALAMAN DARIQA A NIGERIA Wasu Malaman Dariqa a Nigeria suna kafa hujja a kan Bidi'o'insu mu... Cigaba da karantawa»
A garin Rayyu an yi wani mutum da ake kira Mahmud bn Hassan Al-Himsiy, Malami ne na Rafidha 'Yan Shi'a. Ya kasance yana cewa: -wai- Aliyu (ra) ya fi dukkan Annabawa falala in ban da Annabi Muhammad (saw).Mene dalilinsa?!Sai ya ce: dalinsa shi ne fadin Allah Madaukaki:{فَقُلْ تَعَالَوْا نَدْعُ أَبْنَاءَنَا وَأَبْنَاءَكُمْ وَنِسَاءَنَا وَنِسَاءَكُمْ وَأَنْفُسَنَا وَأَنْفُسَكُمْ ثُمَّ نَبْتَهِلْ فَنَجْعَلْ لَعْنَتَ اللَّهِ عَلَى الْكَاذِبِينَ } [آل عمران: 61]"Ka ce: ku zo mu kira 'ya'yanmu da 'ya'yanku, matanmu da matanku, kawunanmu da kawunanku sai mu kaskantar da kai mu yi addu'a, mu sanya tsinuwar Allah a kan makaryata".Saboda Hassan da Hussain (ra) ake nufi da "أَبْنَاءَنَا", Fatima (ra) kuma ake nufi da "وَنِسَاءَنَا", Aliyu (ra) kuma ake nufi da "وأنفسنا", don haka a ganinsa ba Annabi (saw) ake nufi a cikin "وأنفسنا" ba, don mutum ba ya kiran kansa, don haka wani mutum daban ake nufi, kuma kowa ya san cewa; wanin da ake nufi dole ya zama shi ne Aliyu (ra). Don haka -wai- Ayar ta yi nuni ne a kan cewa; ran Aliyu (ra) ita ce ran Annabi (saw), ma'ana, Aliyu kamar Annabi (saw) yake, su biyun a matsayi daya suke ta kowace fiska. Sai dai kawai Aliyu (ra) ba Annabi ba ne bisa Ijma'i, kuma an yi Ijma'i a kan cewa; Annabi Muh'd (saw) ya fi Aliyu (ra) falala, kuma Ijma'i ya yi nuni a kan cewa; Annabi (saw) ya fi sauran Annabawa, don haka dole ya zama cewa: Aliyu (ra) ya fi sauran Annabawa, Annabi (saw) ne kawai ya fi shi a cikin Annabawa.Amsa:To kamar yadda aka yi Ijma'i a kan cewa; Annabi Muh'd (saw) ya fi Aliyu (ra), to haka aka yi Ijma'i tun kafin a haifi shi wannan Malamin Shi'an a kan cewa: mutum Annabi ya fi mutumin da ba Annabi ba falala. Kuma an yi Ijma'i a kan cewa; Aliyu (ra) ba Annabi ba ne. Don haka dole kowa ya yarda cewa: Duk wani Annabi ya fi Aliyu (ra) falala tun da Aliyun (ra) ba Annabi ba ne.Tafsrin Fakhruddeen Al- Raziy (8/ 248)Wannar mas'ala tana daga cikin mas'alolin da suka sa wani babban Malamin Shi'a a Nigeria ya bar Shi'a, saboda ya ji Zakzakiy ya ce: Ali (as) ya fi kowane Annabi in ban da Annabi Muhammad (saw). A garin Rayyu an yi wani mutum da ake kira Mahmud bn Hassan Al-Himsiy, Malami ne na Rafidha 'Yan Shi'a. Ya kasance yana cewa: -wai-... Cigaba da karantawa»
LABARIN ABU HANIFA DA MULHIDAIWata rana Munazara (Muqabala) ta kasance tsakanin babban Malamin Fiqhun nan Imamu Abu Hanifa da wasu Mulhidai masu kore samuwar Allah.Ana cikin tattaunawa sai Imamu Abu Hanifa ya ce musu:"Me za ku ce game da mutumin da ya ce muku ya ga wani babban jirgin ruwa, yana mak'are da kaya, an cika shi da kayayyaki daban - daban, yana tafiya a cikin Teku, ga igiyar ruwa mai tsanani tana ta juyawa, ga iska mai karfi tana ta kadawa, amma duk da haka jirgin nan yana ta tafiya a seti babu abin da yake kada shi, amma kuma jirgin ruwan ba shi da matuki da yake tuka shi.To shin kuna ganin haka zai yiwu?!".Sai suka zabura suka ce: A'a, wannan kam ba zai yiwu ba!Ai wannan hankali ba zai kama ba!Kai, ko da a mafarki hakan ba zai faru ba!Sai Imam Abu Hanifa ya ce: "Subhanallah!Idan a hankalce ba zai yiwu a samu jirgin ruwa ya yi tafiya a seti ba tare da matuki ba, to ta yaya zai yiwu a hankalce a ce: wannar Duniya da muke gani, mai cike da halittu daban - daban, ma'abociyar halaye da yanayi mabanbanta, ga ta da fadin kasa iya ganinka, amma a ce: -wai- ta faru ne ba tare da Mahalicci ba, kuma babu mai gudanar da ita a yanzu haka?!".Ai nan da nan Mulhidai sai suka rude, suka ce: lallai ka fadi gaskiya.To jama'a, ku duba ku gani fa!Ashe rashin hankali ne mutum ya zo ya rena wa mutane hankula ya ce: babu Allah, babu Mahalicci, babu mai gudanar da Duniya da dukkan abin da ke cikinta na manyan halitu da mutane.Duk mai hankali in ya fadi haka to shi ma ya sani a cikin zuciyarsa cewa; karya kawai yake yi. LABARIN ABU HANIFA DA MULHIDAI Wata rana Munazara (Muqabala) ta kasance tsakanin babban Malamin Fiqhun nan Imamu Abu Hanifa da wasu Mulhida... Cigaba da karantawa»
HABAKAR ILIMIN HADISI A KASAR HAUSAA yau ne al'ummar Hausawa suka kara samun cigaba a bangaren ilimin Addinin Muslunci, inda aka kaddamar da tarjamar babban littafi mai albarka a Addinin Muslunci, wato littafin Muwadd'u ta Imamu Malik, wanda Shaikh Dr. Ahmad Ibrahim Bamba ya tarjama zuwa harshen Hausa. Allah ya saka masa da alheri, tare da wanda ya dauki nauyin fitar da wannan littafi mai albarka insha Allahu.Alal hakika Hadisi shi ne Sunna, wato hanyar Annabi (saw). Mabiya Hadisi kuma su ne Ahlus Sunna. Shi ya sa tun zamanin farko, da aka samu masu inkarin Hadisi, sai al'ummar Musulmi ta rabu gida biyu; aka samu masu Bin Hadisi su ne Ahlus Sunna, da kuma masu inkarin Hadisi, su kuma su ne 'Yan Bidi'a.Wani abu mai muhimmanci da ya kamata a sani, su fa wadannan masu inkarin Hadisi, wadanda aka rada musu suna 'Yan Bidi'a, ba Hadisan Tsarki da Sallah da Azumi da Zakka da Hajji da kasuwanci suke inkari ba, a'a, sun yarda da wadannan Hadisan. Hadisan da suke inkari su ne Hadisan da suka saba ma ra'ayoyinsu na Akida. Don haka ake kiransu 'Yan Bidi'a, Mabiya son zuciya. Saboda da ma son zuciya a Akida ya raba al'umma kashi - kashi, kungiya - kungiya. Sai Khawarijawa suka yi inkarin dukkan Hadisan da suka saba ra'ayoyinsu, kamar Hadisan da suke nuna Imani yana rarrabuwa, da kuma Hadisan tabbatar da Imani ga Musulmi mai sabo, da Hadisan Da'a wa Shugabanni. Haka Rafidha 'Yan Shi'a, suka yi inkarin Hadisan da suka saba Addininsu. Haka Mabiya Ilmul Kalam, suka yi inkarin Hadisan Siffofin Allah da sauransu. Sufaye da Rafidha 'Yan Shi'a suka yi inkarin Hadisan makomar Iyayen Annabi (saw) saboda sun rushe musu Akidarsu a gadon falala. Hadisan sun hana su gadon Shariftaka da Sayyidantaka. Saboda abin da Hadisan suke nunawa shi ne; kusacinka da dangantakarka ta jini da Annabi (saw) ba za ta amfanar da kai da komai ba, matukar ba ka yi Imani da Allah da ka bi Sunnar Manzonsa (saw) da hanyar Sahabbansa ba.To hanyar da wadannan 'Yan Bidi'a suke bi wajen inkarin Hadisan hanyoyi ne guda biyu: Masu tsaurin ido su ne suke karyata Hadisan kai tsaye, wato Rafidha 'Yan Shi'a da Mu'utazila da makamantansu, saboda su a wajensu Sahabban da suka ruwaito Hadisan ma ba mutanen kirki ba ne, balle kuma sauran maruwaita na kasa da Sahabban!Hanya ta biyu ita ce ta galibi 'Yan Bid'ar da suke da alaka da wasu ilmomi na Shari'a, wato cewa: Hadisan "Ahaad" ne. Wato ba Hadisai ne Mutawatirai ba.Alhali akwai mamaki, wanda yake raya cewa; Annabi (saw) mai gaskiya ne, amma kuma ka same shi ba zai gaskata maganar mai gaskiyan ba!Idan har ba za ka gaskata Annabi (saw) a abin da ya tabbata ya fada ba, to miye amfanin fadinka cewa shi mai gaskiya ne?!Idan har ka yarda Annabi (saw) mai gaskiya ne, to me zai hana ka gaskata shi a abin da ya ba ka labari?!Akwai mamaki matuka!Idan har ya tabbata Annabi (saw) ya fadi Hadisi, to kai tsaye gaskiya ne, kuma daga Allah ne!Su kuma Hadisan Sahihul Bukhari da Muslim Malaman Hadisi sun yi ittifaki a kan karbansu. Don haka idan ka hada wannan ittifaki da ingancin Hadisan sai ya kara ma Hadisan karfi, har su isa ga fa'idantar da yakini. Don haka za a yi aiki da su a mas'alolin Akida da Fiqhu, saboda dukkansu suna nuni ga yakini. Imam al-Sam'aniy ya ce:((إن الخبر إذا صح عن رسول الله - صلى الله عليه وسلم - ورواه الثقات والأئمة، وأسندوه خلفهم عن سلفهم إلى رسول الله - صلى الله عليه وسلم - وتلقته الأمة بالقبول، فإنه يوجب العلم فيما سبيله العلم، وهذا قول عامة أهل الحديث والمتقنين من القائمين على السنة.وإنما هذا القول الذي يذكر أن خبر الواحد لا يفيد العلم بحال، ولا بد من نقله بطريق التواتر لوقوع العلم به، شيء اختراعته القدرية والمعتزلة، وكان قصدهم منه رد الأخبار)).الحجة في بيان المحجة (2/ 228)، صون المنطق والكلام عن فني المنطق والكلام (ص: 212)((Lallai idan Hadisi ya inganta daga Manzon Allah (saw), amintattun maruwaita da A'imma suka ruwaito shi da isnadi, na baya suka ruwaito daga magabatansu, har zuwa Manzon Allah (saw), kuma al'umma ta karbi Hadisin (ba ta yi inkarinsa ba), to lallai Hadisin yana nuni ga yakini, a mas'alolin da suke bukatar samun yakini (Manyan mas'alolin Addini). Wannan shi ne ra'ayin gamayyar kwararrun Malaman Hadisi, tsayayyu a kan Sunna.Amma ra'ayin da ake fadin cewa; Hadisi "Ahaad" ba ya nuni ga yakini ta kowane hali, -wai- dole sai ya zama Hadisi Mutawatiri kafin ya yi nuni ga yakini, kawai wani ra'ayi ne da 'Yan Qadariyya da Mu'utazila suka kirkira, kuma manufarsu ita ce: watsi da Hadisan Annabi (saw))).A nan sai Sam'aniy ya nuna cewa; duk Hadisin da al'umma suka karbe shi - kamar Hadisan Sahihul Bukhari da Muslim - suka yi Ittifaki a kansa, to yana nuni ga yakini, cewa; tabbatas Hadisin gaskiya ne, Annabi (saw) ya fade shi.Kuma kar wani ya ce: ai ba duka al'umma ce ta yi Ittifaki da Ijma'i a kan Hadisin ba!A'a Malam, ai Ittifakin da ake la'akari da shi shi ne Ittifakin Malaman Fannin da ake magana a kansa. Kamar yadda Ittikin Malaman Fiqhu shi ne abin lura a Babin Fiqhu, to haka Ittifakin Malaman Hadisi shi ne abin lura a fannin Hadisi.Saboda haka duk Hadisin da ya tabbata Annabi (saw) ya fade shi, to idan da gaske ka yarda Annabi Mai gaskiya ne, to dole ne ka gaskata Hadisin. Idan kuma ka ki gaskatawa, to akwai alamar rauni a yardarka cewa: Annabi (saw) mai gaskiya ne. HABAKAR ILIMIN HADISI A KASAR HAUSA A yau ne al'ummar Hausawa suka kara samun cigaba a bangaren ilimin Addinin Muslunci, inda aka kadda... Cigaba da karantawa»
ME YA JANYO BULLAR DA'AWAR INTERFAITH?Muna karatu da Malamina, na yi bayanin ingantattun hanyoyi na raddi ma Kiristoci, sabanin hanyoyin da Mabiya Ilmul Kalam suka bi wajen yi musu raddi, a ciki sai na kawo hanyar tabbatar da Manzancin Annabi Muhammad (saw) ta hanyar labarun da ya bayar, wadanda za su bayyana a gaba. (الإخبار بالمغيبات المستقبلة). A ciki sai na ambaci cewa; Annabi (saw) ya ba da labarin bayyanar Khawarijawa 'Yan Ta'adda, kuma ga shi sun bayyana kamar yadda Annabi (saw) ya fada, har SUN BAYYANA MA KOWA, KOWA YANA IYA SANINSU. Sai Malamina ya ce: A'a, ba kowa ne yake iya saninsu ba, Malamai ne suke iya saninsu.To na yi mamakin wannar magana, ganin cewa; mu a Nigeria kowa ya ga barnar Boko Haram a fili. Don haka ya kamata a ce yanzu kam kowa zai iya gane Khawarijawa.To ban tashi ganin hakikanin maganarsa ba sai da na zo nake bayani a kan Sayyid Qutub, inda na tabbatar da abin da Malamai da Manazarta suka tabbatar cewa; Sayyid Qutub shi ne tushen ta'addanci a wannan zamani. Sai ga wadanda mutane suke zaton sun fahimci Sunna amma su ne suka zama sojojin jayayya da kare barnar Sayyid Qutub. Kai, har ya kai ga wani ma shi jayayya yake yi a kan samuwar 'Yan Ta'adda a cikin Musulmai, -wai- kawai makirci ne na Turawa (نظرية المؤامرة).To gaskiya ne, ba abin mamaki ba ne don mutane ba su san Khawarijanci ba, saboda akwai dalilai masu yawa da za su hana su sani. Saboda hatta a mas'alar Hakikanin Imani, a zahiri Khawarijawa ba su da banbanci da Ahlus Sunna. Shaikh Muhammad bn Ibrahim Alu-Shaikh yana bayanin Akidar Khawarijawa da Mu'utazila sai ya ce:((وافقوا أهل السنة في أصل الإيمان أنه قول وعمل، لكن خالفوهم فقالوا: لا يتبعض ولا يتجزأ)).شرح العقيدة الواسطية (ص: 128)((Sun dace da Ahlus Sunna a tushen ma'anar Imani cewa; Magana ne da Aiki, sai dai suna saba musu inda suke cewa: ba ya rarrabuwa sashe - sashe, yanki - yanki)).A wani wajen kuma ya ce:((ويوافقون أهل السنة والجماعة في أنه قول وعمل، ويخالفون أهل السنة في أنه يتبعض ويتجزأ)).شرح العقيدة الواسطية (ص: 187)((Suna dacewa da Ahlus Sunnati wal Jama'a a ma'anar Imani cewa; Magana ne da Aiki, suna saba ma Ahlus Sunnan a cewa: Imanin yana rarrabuwa sashe - sashe, yanki - yanki)).Ka ga a zahiri kamar babu banbanci. Amma inda banbancin yake shi ne wajen cewa: Imani yana rarrabuwa a wajen Ahlus Sunna, amma a wajen Khawarijawa kuma ba ya rarrabuwa. Wannan ya sa Sayyid Qutub ya ce:((إن الإيمان وحدة لا تتجزأ))في ظلال القرآن (2/ 798)((Imani abu ne guda daya a dunkule ba ya rarrabuwa)).Alhali a Mazhabar Ahlus Sunna Imani yana rarrabuwa, kamar yadda Ibnu Taimiyya ya ce:((إن الإيمان مما يتبعض ويتجزأ)).مجموع الفتاوى (12/ 491 - 492)((Imani abu ne da yake rarrabuwa sashe - sashe, yanki - yanki)).Don haka cewa; Imani yana rarrabuwa shi ya banbance Akidar Khawarijawa daga Akidar Ahlus Sunna. Idan mutum bai yi zurfi a karatu ba ba zai san wannan ba, musamman saboda rashin samun littatafan su Khawarijawan, sai dan abin da ba za a rasa ba a wajen "Ibadhiyya". Ga maganar babban Malaminsu a wannan zamani al-Khaliliy, a Ta'alikinsa ga wani littafin magabacinsu inda ya ce:((وإذا اعتقد ما لزمه اعتقاده ولم يحضره فرض قولي أو عملي كان مؤمناً كامل الإيمان، وإذا وجب عليه شيء من الأقوال أو الأفعال وأداه كما وجب عليه ازداد إيمانه وإذا أخل بهذا الواجب انهدم إيمانه كله)).مشارق الأنوار (ص 35- 36)((Idan mutum ya kudurce abin da dole ya kudurce shi, kuma a lokacin wani farilla na aiki ko magana bai hau kansa ba, to ya kasance Mumini mai cikakken Imani. Amma idan wani abu na maganganu da aiyuka suka wajaba a kansa, kuma ya aikata shi, to Imaninsa ya karu, amma idan ya bar wannan wajibin to IMANINSA GABA DAYA YA RUSHE)).To ka auna wannar magana ta wannan mutumi, da kuma maganar Sayyid Qutub inda ya ce:((والإسلام منهج للحياة كلها. من اتبعه كله فهو مؤمن وفي دين الله. ومن اتبع غيره ولو في حكم واحد فقد رفض الإيمان واعتدى على ألوهية الله، وخرج من دين الله. مهما أعلن أنه يحترم العقيدة وأنه مسلم. فاتباعه شريعة غير شريعة الله، يكذب زعمه ويدمغه بالخروج من دين الله.))في ظلال القرآن (2/ 972)((Muslunci tsarin rayuwa ne gaba dayanta, wanda ya bi shi gaba dayansa shi Mumini ne, kuma yana cikin Addinin Allah. Amma wanda ya bi wani abu ba Muslunci ba ko da A HUKUNCI DAYA NE TO YA YI WATSI DA IMANI, ya yi ta'addanci a kan Uluhiyyar Allah, kuma YA FITA DAGA ADDININ ALLAH, duk yadda ya shelanta cewa; yana girmama Akidar Muslunci, kuma shi Musulmi ne. Binsa ga wata Shari'a ba ta Allah ba, yana karyata rayawarsa girmama Akida, kuma yana rusa shi ta hanyar fitarsa daga Addinin Allah)).Idan ka lura da maganganun mutanen biyu, za ka ga iri daya ne. Kowannensu ya tabbatar da cewa; idan mutum ya yi dukkan wajiban Addini ya zama Mumini, amma idan ya bar wajibi daya to ya fita daga Muslunci.To abin da nake so na isa gare shi shi ne; babu mai ilimi da zai yi inkarin Khawarijawa a cikin al'umma. Mai inkarin samuwarsu dayan uku ne, imma Jahili ko mabarnaci ne, mai son boye barnar mabarnata, ko kuma Dan "Safsata" ne, mai inkarin hakikanin abubuwa na zahiri.Don haka abin da ya kamata a sani, su Turawa da Makiya Addinin Muslunci, ba su suka kirkiri Boko Haram da sauran Kungiyoyin Khawarijawa ba, a'a, su Khawarijawan su suka kafa Kungiyoyinsu da nufin yin Jihadi, amma na Bidi'a, saboda mummunar fahimtarsu ga Alkur'ani da guluwwi a Addini. Sai dai kuma su Turawa da Makiya Addinin Musluncin suna farin ciki da murna da bayyanarsu, kuma suna ribatar ta'addancin nasu. Kai, har za su iya taimaka musu su karfafe su, don su isa ga biyan bukatunsu na yakar Addini.Yanzu ka duba asara da Addinin Muslunci ya yi a dalilin bullar ta'addancin Khawarijawan Boko Haram, harkar da'awa ta yi rauni matuka. An sa ido a kan masu da'awa zuwa ga Muslunci da Sunna. Da ma Ahlus Sunna su ne masu yi, sai kuma aka zo ana tuhumarsu da koyar da ta'addanci, saboda 'Yan Ta'addan suna cewa; -wai- su ma Ahlus Sunna ne. Alhali su masu tuhumar sun san karya suke yi, to amma saboda da shi za su yi amfani su hana Da'awa zuwa ga Muslunci da Sunna shi ya sa suke yada hakan. Alhali kowa ya san Khawarijawa 'Yan Ta'adda ba su da alaka da Mazhabar Ahlus Sunna.A takaice, harkar Da'awa ta yi rauni, a dalilin matsalar tsaro, saboda ta'addancin Khawarijawa.Bayan haka, daga cikin ribar da Turawa da Makiya Muslunci suka ci a bayyanar Khawarijawan Boko Haram, sai suka kafa Kungiyoyin Hade Addinai "وحدة الأديان" (Interfaith), da sunan neman zaman lafiya. Abin da a yanzu kasuwarsa take ci, saboda shi ne babban aikin da Ilhadin Duniya ya saka a gaba, a hade Addinai a koma Addini guda daya, wato shi ne Addinin mutumtaka (Humanity), a dena kyamar kafirci da kafirai, Musulmi ya koma kaunar kafirai da soyayya da su.A takaice, abin da ya janyo bullar irin wadannan Kungiyoyi na hade Addinai shi ne wautar jahilai daga cikin Musulmai, Khawarijawa masu Addini da jahilci, masu barna a bayan kasa, suna barna amma suna zaton kyakkyawan aiki suke yi. Allah ya ce:{قُلْ هَلْ نُنَبِّئُكُمْ بِالْأَخْسَرِينَ أَعْمَالًا (103) الَّذِينَ ضَلَّ سَعْيُهُمْ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَهُمْ يَحْسَبُونَ أَنَّهُمْ يُحْسِنُونَ صُنْعًا (104)} [الكهف: 103، 104]((Ka ce: shin ba za mu ba ku labarin masu hasaran aiyukansu ba ne? Wadanda aiyukansu suka bace a rayuwar Duniya, alhali suna zaton su kyautata aiki suke yi)).Sayyidina Aliyu (ra) ya ce: Wadannan su ne Khawarijawa.Saboda haka idan ba mu yaki tunanin ta'addancin Khawarijawa da ke cikin al'ummar Musulmi ba, to Turawa da yaransu yanzu suka fara raba Musulmai da Addininsu da Imaninsu, da Mulhidantar da al'ummar da sunan yakar ta'addanci da tsattsauran ra'ayin Addini, da neman hadin kan mabiya Addinai don neman zaman lafiya.A takaice, mafiya yawan mutane ba sa iya gane banbanci tsakanin Khawarijawa da Ahlus Sunna. Kuma Turawa da Makiya Muslunci suna ribatar wautar Khawarijawa suna yakar Muslunci da Musulmai cikin sauki, ta hanyar fakewa da samar da zaman lafiya. ME YA JANYO BULLAR DA'AWAR INTERFAITH? Muna karatu da Malamina, na yi bayanin ingantattun hanyoyi na raddi ma Kiristoci, sabanin hanyoy... Cigaba da karantawa»
BA A KIRAN FITINA TSAKANIN MUSULMAI DA SUNAN TA'ADDANCIBabbar matsalar matasan da suka nada kawunansu a matsayin Malamai, kuma masu Jarhi da Ta'adili da yanke hukunci a kan Malamai Ahlus Sunna da bidi'antar da su tare da Kungiyoyinsu ita ce: rashin "Ta'asili" a ilimi, wato rashin sanin mas'alolin ilimi daga tushensu na dalilan Shari'a; daga Alkur'ani da Sunna.Malamai suna kasa daukar makami da ake samu a cikin al'ummar Musulmai zuwa kashi uku:1- Ta'addancin Khawarijawa, na fita daga al'umma da halasta jinanen Musulmai, da dukkan jinane da Allah ya haramta, kamar jinanen Kafiran Alkawari da makamantansu. Annabi (saw) ya ba da labarinsu inda ya ce:«إن من ضئضئ هذا، قوما يقرءون القرآن، لا يجاوز حناجرهم، يمرقون من الإسلام مروق السهم من الرمية، يقتلون أهل الإسلام، ويدعون أهل الأوثان، لئن أدركتهم لأقتلنهم قتل عاد»صحيح البخاري (9/ 127) صحيح مسلم (2/ 741)"Lallai daga asalin wannan mutumi (Zul Khuwaisirah) akwai wasu mutane za su fito, suna karanta Alkur'ani amma ba ya wuce makogoronsu, suna fita daga Muslunci kamar fitan mashi daga abin da aka jefa, suna kashe Ma'abota Muslunci suna barin Ma'abota bautar gumaka, in na riske su zan kashe su kisan Adawa". Wannan abin da Khawarijawa suke yi, a yau shi ake kira da sunan "TA'ADDANCI", kuma akwai Kungiyoyi na Musamman bisa wannan TA'ADDANCI, tun daga kan Al-Qa'ida, ISIS, Al-Shabab da kuma Boko Haram da makamantansu. A yau in kira Ta'addanci wannan ake nufi.Shi ne abin da muka ce: Sufaye ba sa yin irinsa saboda dalilai da muka ambata a baya.2- "Bagyu" na 'Yan Tawaye, wato shi ne yaki da gomnati, wanda yake kasancewa bisa tawaye wa shugaba, bisa manufofi na Siyasa, kuma babu kafirta juna a cikinsa. Malamai suna banbanta wannan da Ta'addancin Khawarijawa. Suna misali da shi da yakin da ya faru tsakanin Aliyu (ra) da Mu'awiya (ra). Yaki ne da Mu'awiya (ra) yake da Tawili. Shi ya sa Allah ya ce:{ وَإِنْ طَائِفَتَانِ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ اقْتَتَلُوا فَأَصْلِحُوا بَيْنَهُمَا فَإِنْ بَغَتْ إِحْدَاهُمَا عَلَى الْأُخْرَى فَقَاتِلُوا الَّتِي تَبْغِي حَتَّى تَفِيءَ إِلَى أَمْرِ اللَّهِ فَإِنْ فَاءَتْ فَأَصْلِحُوا بَيْنَهُمَا بِالْعَدْلِ } [الحجرات: 9]"In bangarori guda biyu na Muminai sun yi yaki tsakaninsu to ku yi musu Sulhu, amma in daya daga cikinsu ya yi zalunci a kan daya to ku yaki wanda ya yi zaluncin har sai ya dawo ga umurnin Allah, in ya dawo sai ku yi Sulhu tsakaninsu bisa adalci".3- Yakin Fitina da yake kasancewa tsakanin Kungiyoyin Musulmai masu dangantuwa zuwa ga Muslunci. Annabi (saw) ya ce:«إذا التقى المسلمان بسيفيهما فالقاتل والمقتول في النار»صحيح البخاري (1/ 15) صحيح مسلم (4/ 2213)"Idan Musulmai guda biyu suka yi fada da takubansu to wanda ya yi kisa da wanda aka kashen duka suna wuta".Irin wannan shi ne wanda yake kasancewa tsakanin Musulmai a junansu na fada na fitina, har da daukar makami.Shaikhul Islami ya ce:إذا كانت فتنة بين المسلمين، مثل أن يقتتل رجلان أو طائفتان على ملك أو رئاسة أو على أهواء بينهم، كأهواء القبائل والموالي الذين ينتسب كل طائفة إلى رئيس أعتقهم، فيقاتلون على رئاسة سيدهم، وأهواء أهل المدائن الذين يتعصب كل طائفة لأهل مدينتهم، وأهواء أهل المذاهب والطرائق كالفقهاء الذين يتعصب كل قوم لحزبهم ويقتتلون، كما كان يجري في بلاد الأعاجم، ونحو ذلك، فهذا قتال الفتنة ينهى عنه هؤلاء وهؤلاءجامع المسائل لابن تيمية (4/ 231)"Idan Fitina ta kasance tsakanin Musulmai, misali mutum biyu, ko kungiyoyi biyu su yaki juna a kan mulki ko shugabanci ko a kan wani son zuciya tsakaninsu, kamar son zuciyan kabilu da maulaye wadanda kowanne bangare yake dangantuwa zuwa ga shugaban da ya 'yanta su, sai su yi yaki a kan shugabancin uban gidansu, ko kuma son zuciya na 'yan garanci, wanda kowane bangare yake ta'assubanci ga mutanen garinsu, da kuma son rai na Mazhabobi da Darikoki, kamar Malaman Fiqhu wanda kowadanne mutane a cikinsu suke ta'assubanci ga Kungiyarsu har su yi yaki a tsakaninsu, kamar yadda hakan yake faruwa a garuruwan Ajamawa, da makamancin haka, to wannan yaki ne na Fitina, ana hana wadannan da wadannan duka".Don haka fitina da take faruwa tsakanin Musulmai, kamar fada da makami tsakanin 'Yan Darikun Sufaye da Ahlus Sunna a kan Masallaci ko wani abu daban duka yana cikin fitina tsakanin Musulmai, ba a kiransa da sunan TA'ADDANCI wanda aka san Khawarijawa da shi.Haka kuma, Shirka da 'Yan Darikun Sufaye suke yi ba a kiransa da TA'ADDANCI bisa ma'anar TA'ADDANCIN Khawarijawa, abin da ake kiransa shi ne kaskantar da Allah da rena shi da rashin girmama shi.Ibnul Qayyim ya ce:إن الشرك هضم لحق الربوبية، وتنقيص لعظمة الإلهية، وسوء ظن برب العالمينإغاثة اللهفان (1/ 60 – 61)"Lallai shirka tauye hakkin Rububiyya ce, da kaskantar da girman Uluhiyyar Allah, da munana zato ga Ubangijin Talikai".To duk wanda ya tattauna da galibin 'Yan Kungiyar Salafiyyun zai fahimci sun jahilci wadannan banbance - banbance da ke tsakanin wadannan nau'uka na fadace - fadace ko yakukuwa a cikin al'ummar Musulmi, ta yadda za ka same su suna kiran kowanne da sunan KHAWARIJANCI da TA'ADDANCI. Alhali wannan jahilci ne da rashin "Ta'asili" da son kutsawa cikin mas'alolin ilimi ba tare da sani ba, da matukar kwadayin yanke hukunci wa mutane da bidi'antar da su saboda guluwwi.Saboda haka, ta yaya za a yi wanda bai san "Usul" na Masa'il ba, wato dalilai da ake gina mas'alolin nan a kansu, amma kuma ya nada ma kansa rawanin bidi'antarwa, a matsayin "Hamilu liwa'il Jarhi wat Ta'adeel" na Nigeria?!Allah ya yi mana tsari da rudin Shaidan. BA A KIRAN FITINA TSAKANIN MUSULMAI DA SUNAN TA'ADDANCI Babbar matsalar matasan da suka nada kawunansu a matsayin Malamai, kuma masu Ja... Cigaba da karantawa»
Amsa Addu'aWato idan ka ga halin mutanen da suke jayayya a kan cewa halin matsin rayuwa da ake ciki a dalilin zaluncin shugabanni jarabawa ce daga Allah don mu koma gare shi, sai ka fahimci da alama mutane masu yawa ba su shirya neman mafita daga halin da ake ciki ba.Alhali duk wanda ya san Allah, ya san sunayensa da siffofinsa, wato ya san ma'anoninsu, zai san cewa idan muka tashi da gaske muka kira Allah, muka roke shi to zai amsa mana.Imam Ibnul Qayyim ya ce:وهو المجيب يقول من يدعو أجب *** -ه أنا المجيب لكل من نادانيوهو المجيب لدعوة المضطر إذ *** يدعوه في سر وفي إعلانMa'ana Allah mai amsa kiran dukkan wanda ya kira shi ne. Yana amsa kiran kowa, hatta kafirai. Yana kuma amsa kiran kibantattun bayi, kamar wanda ya shiga matsin halin rayuwa, ya shiga tsanani.Allah ya ce:﴿أَمَّن یُجِیبُ ٱلۡمُضۡطَرَّ إِذَا دَعَاهُ وَیَكۡشِفُ ٱلسُّوۤءَ﴾ [النمل: ٦٢]{Waye yake amsa wanda ya shiga matsi idan ya kira shi, kuma yake yaye mummunan abu...?}.Kuma kamar yadda yake amsa addu'ar wanda aka zalunta. Haka yana amsa addu'ar duk wanda ya debe tsammanin samun biyan bukatarsa daga wajen mutane. Misali; mun gwada zaben shugaba wane mai gaskiya, amma ba mu ga canji ba. Mun gwada zaben Muslim - Muslim ticket, amma matsin rayuwan karuwa ya yi, to ya Allah yanzu kam mun yanke tsammani daga kowa sai kai kadai. Ba mu da wata dabara daga gare mu sai neman agajinka.Idan da a ce bayi za su san girman Allah, su san cewa shi mai amsa roko ne, su rataya zukatansu gare shi, su roke shi, su yi masa naci, su nuna ba su da wata sauran dabara sai gare shi, su kira shi ta ko'ina, mutanen kasa daga yankuna da jihohi daban - daban, kabilu daban - daban, da tuni Allah ya amsa addu'arsu, ya karya kashin bayan duk wani azzalumi.Amma kash! Mutane da yawa su mafita a wurinsu ita ce zanga - zanga, da sauran hanyoyin da gurbataccen tunaninsu yake ba su!A gaskiya idan ba mu dawo cikin hayyacinmu, mun yi abin da ya kamata ba, za a dade ana shan wahala.Allah ya sawake. Amsa Addu'a Wato idan ka ga halin mutanen da suke jayayya a kan cewa halin matsin rayuwa da ake ciki a dalilin zaluncin shugabanni jara... Cigaba da karantawa»
TSAKANIN MAULIDI DA MUSABAKAR ALKUR'ANIA kullum in mun ce Maulidi bidi'a ne, sai ka ji wani ya ce; ai ku ma kuna Musabakar karatun Alkur'ani, ai shi ma bidi'a ne.Alhali duk wanda yake da ido a karatun Fiqhu ya san Musabaka tana da asali, Malaman Fiqhu suna kulla babi ko fasali a kan hukuncin Musabaka a cikin babin Jihadi ko bayansa, ko babin "Ju'uli", ko wani wajen daban.Duka Malaman Fiqhu sun yi ittifaqi a kan halascin Musabaka, bisa dalilan Alkur'ani da Sunna da Ijma'i.Sai dai sun yi sabani a kan mas'aloli guda biyu:1- Yin musabaka a kan abin da bai shafi Jihadi ba.2- Sanya kyauta a Musabakar abin da ba doki ko rakumi ko harbi ba.Saboda haka wasu Malaman ba su ambaci Musabaka a fannonin ilimi cikin fagagen Musabakar ba, amma wasu kuma sun sanya Musabaka a fannin ilimi cikin fagagen Musabakar da ta halasta, saboda dalilai kamar haka:1- Hadisin Ibnu Umar (ra) ya ce:قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «إن من الشجر شجرة لا يسقط ورقها، وإنها مثل المسلم، فحدثوني ما هي» فوقع الناس في شجر البوادي قال عبد الله: ووقع في نفسي أنها النخلة، فاستحييت، ثم قالوا: حدثنا ما هي يا رسول الله قال: «هي النخلة»صحيح البخاري (1/ 22) صحيح مسلم (4/ 2164)Annabi (saw) ya ce:"A cikin bishiyoyi akwai bishiyar da ganyenta ba ya zubewa, misalinta kamar Musulmi Mumini ne. KU GAYA MINI, WACE BISHIYA CE?".Sai mutane suna ta ambaton sunayen bishiyoyi daban-daban. Sai Ibnu Umar ya ce: Na ji a raina ita ce bishiyar dabino, amma sai na ji kunyan ba da amsa.Sai Sahabbai suka ce: mun ba ka gari ya Manzon Allah.Sai ya ce: "Ita ce bishiyar dabino".2- Hadisin Gasa da Sayyidina Abubakar (ra) ya yi da Mushrikai a kan yakin Rum da Farisa, wanda Allah ya saukar da:{الم (1) غُلِبَتِ الرُّومُ (2)} [الروم: 1، 2]3- Ba a yi hani a kai ba, don haka yana nan a kan asali na halasci, tun da babin Mu'amala ne ba babin Ibada ba.(البراءة الأصلية)4- Qiyasin Musabaka a fannin ilimi a kan Musabaka na dawaki da rakuma, saboda duka sun yi tarayya cikin illar daukaka Addinin Allah. Kamar yadda ake daukaka Addini a kare shi da Jihadi, haka ake daukaka shi a kare shi da Ilimi, don haka ya halasta a yi Musabaka a ilimin Addini, kamar yadda ya halasta a yi Musabaka a kayan yaki saboda shirin Jihadi. Saboda ka'idar nan ta Usul kamar haka:كل حكم شرعي أمكن تعليله فالقياس جار فيهالمستصفى (ص: 329)Wannan ya sa Malaman Hanafiyya suka Nassanta halascin yin Musabaka a ilimi da Qiyasinsa a kan na dawaki da rakuma.Al-Baldajiy a sharhin littafinsa ya ce:"قال: (وعلى هذا التفصيل إذا اختلف فقيهان في مسألة وأرادا الرجوع إلى شيخ وجعلا على ذلك جعلا) لأنه لما جاز في الأفراس لمعنى يرجع إلى الجهاد يجوز هنا للحث على الجهد في طلب العلم، لأن الدين يقوم بالعلم كما يقوم بالجهاد".الاختيار لتعليل المختار (4/ 169)، تبيين الحقائق شرح كنز الدقائق وحاشية الشلبي (6/ 32)A nan sai ya yi Qiyasin Musabaka a ilimin Addini a kan Musabaka da dawaki da rakuma, saboda sun hadu cikin illar daukaka Addinin Allah da kare shi.Haka cikin Malaman Malikiyya Al-Haddab ya yi ishara ga haka inda ya ce:"لكن لما كانت هذه الأشياء مما يستعان بها على الجهاد في سبيل الله الذي هو طريق إلى إظهار دين الله ونصرته جاز لما فيه من منفعة الدين وما يؤدي إلى عبادة، أو يستعان به في عبادة فهو عبادة".مواهب الجليل في شرح مختصر خليل (3/ 390)Saboda haka Musabaka a ilimin Addinin ya halasta, sawa'un bangaren Alkur'ani ne ko Hadisi ko Fiqhu.Saboda haka Maulidi ba dadai yake da Musabaka ba.Maulidi a babin Ibada yake, don haka dole sai da Aya ko Hadisi kafin a yi shi, ba a Qiyasi a babin Ibada.Sabanin Musabaka, ita kuma Mu'amala ce, matsayinta shi ne halasci. In kana so ka yi, in ba ka so ka bari. Kuma za a iya fitar da hukuncinta daga Qiyasi.Wannan ya sa har yau ba za ka taba samun babin Maulidi a littatafan Fiqhu ba, amma za ka samu babin Musabaka.Don haka kalubalantar maganar Maulidi da maganar Musabaka shubuha ce ba hujja ba, duk mai ilimi ya san hanyar rago daban, hanyar kare daban.Don haka Musabaka halas ce, Maulidi Haram ne, saboda bidi'a ne. TSAKANIN MAULIDI DA MUSABAKAR ALKUR'ANI A kullum in mun ce Maulidi bidi'a ne, sai ka ji wani ya ce; ai ku ma kuna Musabakar karatun... Cigaba da karantawa»
Adai kan maulidi ne!Ibn taimiyya a cikin littafinsa اقتضاء الصراط المستقيم مخالفة أصحاب الجحيم (252)- Tabbas yayi batu kan samun lada ga wanda yayi maulidi, yake cewa:"و الله قد يثيبهم علي هذا المحبة والاجتهد، لا علي البدع"- Akwai abin lura sosai a cikin wannan batu:1- Idan muka lura kodai malam yana nufin zasu samu ladar nuna soyyayarsu ta hanyar maulidi ga wanda yake ƙoƙarin neman gaskia ba tare da ilimin kasancewar maulidi bid'a bane ya riske shi, A'a shi dai ya aikata ne abisa shi yana ganin daidai ne, ba tare da wani ya bayyana mai bid'ancin hakan ba ko ya riska..2- ko kuma yana nufin Allah zai basu ladar ne akan sonsu ga Annabi (S.A.W) da ƙoƙarinsu akan hakan amma ba akan ita ainihin bid'ar maulidin ba (Son shi da ya kubuta da ga bid'ar), shiyasa yayi ƙaidi.."Domin babu yadda za'ayi Ibn Taimiyyah yace Maulidi bid'a ne, kuma yace za'a samu lada, kuma dama maganarsa sam bata hukunta hakan".- kuma ni abinda nake cewa bada maganar ibn taimiyya ya kamata ku nemawa maulidi mafaka ba a'a matattarar da shima ibn taimiyyya yake komawa garesu ya kamata (Al-kur'ani da sunnah).Allah ya kyautaIbrahim Yunusa Abu-Ammar05 Nov. 2019 Adai kan maulidi ne! Ibn taimiyya a cikin littafinsa اقتضاء الصراط المستقيم مخالفة أصحاب الجحيم (252) - Tabbas yayi batu kan samun lada g... Cigaba da karantawa»
TARIHIN BULLAR KUNGIYOYIN TA'ADDANCI A WANNAN ZAMANI (4)A rubutunmu da ya gabata a kan Tarihin Bullar Ta'addanci.., wato a kashi na (3), mun yi bayani a kan "Rundunar Sirri" (التنظيم السري) ta Kungiyar Ikhwan, wacce Hassanul Banna ya kafa ta. Mun ga asalin manufar kafa ta, mun ga yadda ake rantsuwar shiga rundunar, da kuma irin aiyukan Ta'addanci da rundunar ta aikata, wanda a karshe Dr. Mahmud Assaf ya dora alhakin lalacewar matasan Kungiyar ta Ikhwan, da gurbacewan tunaninsu, har suka dulmuya cikin aiyukan ta'addanci a kan Tasirin Fikrorin Sayyid Qutub a kansu, musamman ta hanyar abin da ya rubuta a littafansa guda biyu mafiya hatsari, wato: "Fi Zilalil Qur'an", da kuma "Ma'alim fi al-Dareeq", wanda matasan a cikinsu suka dauki Fikrar kafirta al'umma, da kuma Fikrar "Hakimiyya", har daga karshe kungiyoyin Khawarijawa suka bayyana. Kamar dai yadda Dr. Mahmud Assaf ya bayyana a littafinsa mai suna: (مع الإمام الشهيد حسن البنا).A rubutun da ya gabata mun kawo misalai na irin aiyukan ta'addancin "Rundunar Sirri" ta Kungiyar Ikhwan, to yau ma za mu cigaba da kawo misalan ta'addancin rundunar ne. Misali na karshe na aikin ta'addanci da za mu kawo a yau shi ne ya zama sababin kashe shugaban Kungiyar ta Ikhwan, kuma wanda ya kafa ta, wato Hassanul Banna.KISA NA UKU: KASHE SHUGABAN MINISTOCI (PRIME MINISTER) AHMAD MAHIR:Bayan sauke shugaban Gomnati Mustapha al-Nahhas da aka yi a ranar 8 ga watan Oktoba, a 1944, da nada Ahmad Mahir a matsayin shugaban Gomnati (Prime Minister), ya rushe Majalisar wakilai, a ranar 15 ga watan Nawumba 1944, sai kuma ya ayyana ranar 8 ga watan Janairu 1945 a matsayin ranar zaben sabbin wakilai. Wannan ya sa Hasanul Banna shugaban kungiyar Ikhwan ya daura aniyar tsayawa takara da shiga zaben. Bayan an yi zabe sai bai yi nasaran cin zabe ba, sai Kungiyar Ikhwan ta yi zargin magudi cewa; magudi aka yi masa, shi ya sa bai ci zaben ba.انظر: من قتل حسن البنا ؟ (ص: 74 - 76)A dalilin wannan zargin magudin zabe da aka yi wa Hassanul Banna, har ya fadi a zabe, sai "Rundunar Sirri" ta Ikhwan (التنظيم السري) ta fara shirya kashe Shugaban Misnistoci Ahmad Mahir. Wanda aka ba da aikin ga Ahmad Abdulfattah Daha, amma sai ya tsorita, ya ki karban aikin. Washe gari da yin haka kuwa sai ga Mahmud al-Isawiy ya kashe Ahmad Mahir, a ranar 24 Feb 1945.Shi wannan Mahmud al-Isawiy din Shaikh Sayyid Sabiq ya tabbatar da cewa; dan Ikhwan ne. Amma Mahmud Assaf ya kore kasancewarsa dan Ikhwan, ya ce: darasin Talata na Hasanul Banna yake halarta, wanda yake yi a duk sati. Dalilin da ya sa suka kashe shi, saboda ya kayar da Hassanul Banna a zabe.Amma dai lallai Mahmud Assaf ya tabbatar da cewa; "Rundunar Sirri" (التنظيم السري) tana shirin kashe shugaban Ministoci Ahmad Mahir.انظر: مع الإمام الشهيد حسن البنا (ص: 151 - 153)A dalilin haka shi ma Hasanul Banna an kama shi, an kai shi kurkuku da sauran wadanda ake zargi da hanu a cikin kisan na Shugaban Ministoci.انظر: من قتل حسن البنا ؟ (ص: 74 – 78 - 81)To a nan ma dai akwai tuhuma mai karfi a kan wannar "Runduna ta Sirri" ta Kungiyar Ikhwan, wajen aikata wannan ta'addanci.KISA NA HUDU: KASHE SHUGABAN MINISTOCI (PRIME MINISTER) NAQRASHIY:Idan za a iya tunawa, a baya, a kashi na biyu na wannar silsila na Tarihin Bullar Ta'addanci, mun tabo abin da ya shafi kashe Mahmud Fahmiy al-Naqrashiy Basha, Prime Minister a kasar Misra, a inda muka ambaci bayanin kashe Ustaz Hassanul Banna, shugaban Kungiyar Ikhwan. Wanda ake ganin kashe Naqrashiy shi ne sababin kashe Hassanul Banna.Kashe Naqrashiy ya biyo bayan matakin da ya dauka ne na rushe Kungiyar Ikhwan. Wanda wannan ya zo ne bayan mataki da Gomnatin Ingila ta dauka na kawo karshen yakin Falasdeen, da kokarin tabbatar da kasar Is*ra'ila. Matakin da Hukumar Naqrashiy ta aminta da shi, amma kungiyar Ikhwan ta yi watsi da shi. Wannan ya sa Gomnatin Naqrashi ta kame mayakan Kungiyar Ikhwan a sansanoninsu na soja a Falasdeen.A wannan yanayi da ake ciki, akwai 'yan Ikhwan da yawa a tsare, saboda zargin wasu aiyukan masu alaka da ta'addanci, kamar khadhiyyar motar Jeep, da wasu daban. Kuma suna fiskantar tsanantawa da azabtarwa a kurkuku. Amma kuma akwai adadi na membobin "Rundunar Sirri" ta Ikhwan wadanda ba a kama su ba, saboda jami'an tsaro ba su san da su ba.Bayan kama wadannan 'yan Kungiyar ta Ikhwan, shi ma Hassanul Banna an yi masa daurin talala, an hana shi haduwa da ganawa da mutane. Babu kowa a tare da shi sai mutum daya kawai, wani lauya mai suna Ustaz Abdulkareem Mansur, wanda miji ne ga 'yar'uwarsa. Wanda shi yake tare da Hassanul Banna a lokacin da aka kashe shi.To ana cikin wannan yanayi su kuma membobin "Rundunar Sirri" ta Ikhwan suna can suna ganawa a boye, suna shirya aiyukan daukar fansa, inda suka shirya kashe shugaban Ministoci Naqrashiy.Ahmad Fu'ad shi ne ya tsara yadda za a yi kisan, shi kuma Abdulmajeed Ahmad Hassan ya batar da kama, ya yi shigar 'yan sanda, ya yi nasarar harbin Naqrashiy, ya kashe shi har Lahira, a lokacin yana kokarin shiga lift, zai tafi ofishinsa a Ma'aikatar Cikin Gida. Wannan ya faru ne a ranar 28 ga Desemba 1948.Kamar yadda ya gabata, kashe Naqrashiy shi ne sababin kashe Hassanul Banna, kamar yadda Dr. Mahmud Assaf ya bayyana.انظر: مع الإمام الشهيد حسن البنا - محمود عساف (ص: 162 - 166)To haka dai Tarihin Kungiyar Ikhwan yake cike da rigingimu da tafo-mu-gama da masu mulki, abin ya haifar da tunanin ta'addanci a cikin kwakwalen matasan kungiyar, musamman bayan tasirin da Fikrorin Sayyid Qutub suka yi a kansu, wanda daga karshe aka samu bayyanar Kungiyoyin Khawarijawa daban - daban, masu kafirta Musulmai su halasta jinanensu, su dauki makami suna kashe su. Kamar yadda Dr. Mahmud Assaf ya tabbatar, har ya zayyano sunayen kungiyoyin, wanda bayani a kan hakan ya gabata a rubutunmu na kashi na (3) na wannar silsila.Za mu cigaba da iznin Allah. TARIHIN BULLAR KUNGIYOYIN TA'ADDANCI A WANNAN ZAMANI (4) A rubutunmu da ya gabata a kan Tarihin Bullar Ta'addanci.., wato a kashi n... Cigaba da karantawa»
Tsakaninsu Wa ya fi Wani Cin Zarafin Manzon Allah (saw)?Tambaya, ka faɗi gaskiya tsakaninka da Allah!Tsakanin Macron da Abduljabbar, wa ya fi wani cin zarafin Manzon Allah (saw)?Kar fa ka manta, shi Macron da ma arne ne. Amma shi kuma wannan Abduljabbar ɗin yana amsa sunan Musulmi, amma a kullum ba shi da aiki sai cin zarafi da tozarta Manzon Allah (saw).Na tabbata da a ce a wasu ƙasashen yake, Abduljabbar bai isa ya fito fili yana cin mutuncin Annabi (saw) kuma a zura masa ido ba.Kar fa ya zama an bar jaki ana dukan taiki! Tsakaninsu Wa ya fi Wani Cin Zarafin Manzon Allah (saw)? Tambaya, ka faɗi gaskiya tsakaninka da Allah! Tsakanin Macron da Abduljabbar, wa y... Cigaba da karantawa»
RIKICIN SHI'A DA GOMNATI: MAFARI DA MANUFAWani abu da ya kamata mutane da hukumomi da kungiyoyin kare hakkin bil'adama su sani game da 'Yan Shi'a da suke fada da Gomnatin Nigeria shi ne; asali tafarkin Shi'a ya ginu ne a kan neman mulki, wato a kan Aqidar Imama. Wannan ya sa tun farkonsu da yaki da Gomnati aka sansu, kuma ba za su dena ba har abada. Saboda Aqidarsu ta Addini ta ginu ne a kan neman mulki, in kuwa mulki ba a hanunsu yake ba to sai sun yaki kowace Gomnati. Saboda suna da Aqidar cewa; a yanzu haka ana karkashin Imamancin Mahdi ne, wanda ya shiga gaiba (ya buya), wanda nan gaba suna sa ran fitowarsa da bayyanarsa. Haka lamarin Shi'a ya kasance a tsawon Tarihi. Har zuwa wannan zamani da Khomeini ya ci nasarar kafa Gomnatin Shi'anci a Iran, a karkashin Nazariyyar "Wilayatul Faqeeh", wato shugabancin wakilin Mahdi. Kuma ita wannar Gomnati ta Khomeini mai wannar Nazariyya, tana bin tafarki ne na "Juyin juya hali" (Thaura/ Revolution), wato Gwagwarmayar kifar da Gomnatoci a kafa Gomnatocin Shi'anci masu bin Nazariyyar "Wilayatul Faqeeh" a gurbinsu. Wannan juyin juya hali ya ci nasara a Iran a shekarar 1979, kuma suka dauri aniyar jefa wannan juyin juya hali zuwa ga sauran kasashen Duniya, ta yadda kafin bayyanar Mahdi an gama kafa masa Gomnatoci a kasashen Musulmai gaba daya.Wannan tsari na "Juyin juya hali" (Thaura/ Revolution) sun kafa masa ginshikai a kusan dukkan kasashen Musulmi, tun daga kasashen Larabawa musamman Iraq, Lebanon da Yemen, har zuwa kasashen Afirka, musamman Nigeria, Niger, Ghana da Tanzania da sauran inda suka samu dama.To in an lura za a ga yadda ita wannar harka ta juyin juya hali ta yi karfi a Lebanon da Iraq da Yemen, inda a Iraqi suke da kungiyoyi masu yawa, a Lebanon suke da kungiyar Hizbullah wacce take da rundunar soja da take yaki a kasa da kasa. Haka a Yemen suke da kungiyar Hutsawa (Houthis), wanda a halin yanzu suke gabza bata-kashi da kawance kasashe karkashin jagorancin Saudiyya, saboda yunkurin juyin mulki da kwace Gomnati da suka yi a Yemen din.Haka kuma in an lura da kyau za a ga cewa; salon da Kungiyar Hizbullah ta Lebanon take bi na kokarin kwace Gomnati irinsa ne babu banbanci 'Yan Shi'a mabiya Zakzaky suke bi a Nigeria. Kuma za a ga irin maganganu da furuci da jawabai da Hassan Nasrallah yake yi irinsu ne Zakzaky yake yi, na nuna isa, da nuna sun fi karfin Gomnati, da nuna cewa; a kowane lokaci za su iya kwace Gomnati.To da wannar 'yar takaitacciyar matashiya nake jan hankalin masu ruduwa da tarzoma da 'Yan Shi'ar suke yi, cewa; ya kamata su sani; ko an kashe 'Yan Shi'a a Abuja, ko ba a kashe su ba, ko an kashe su a Zaria, ko ba a kashe su ba, ko an kama Zakzaky ko ba a kama shi ba, to shirinsu shi ne; dole sai sun kifar da Gomnatin Nigeria, sun kafa Gomnatin Shi'anci bisa wancan tsari na Gomnatin Iran ta "Wilayatul Faqeeh", wannan ya sa suke kiran Zakzaky da sunan: Wakilin Mahdi. Wato wanda zai kafa wa Mahdi Gomnati a Nigeria.Don haka wanda bai san manufarsu ba sai ya sani. Kuma wannan ba ya bukatar kawo shaida, saboda kowa ya san irin furucin Zakzaky da mabiyansa a kan Gomnati da jami'an tsaro. Don haka a kwana da shirin cewa; manufar wadannan ita ce: kwace Gomnatin Nigeria da kafa Gomnati mai nuna goyon baya ga Iran, a karkashin jagorancin Zakzaky ko magajinsa. RIKICIN SHI'A DA GOMNATI: MAFARI DA MANUFA Wani abu da ya kamata mutane da hukumomi da kungiyoyin kare hakkin bil'adama su sani gam... Cigaba da karantawa»
SU WAYE MAFI SHARRIN HALITTA?Ma'auni a wajen 'Yan Duniya, 'Yan Dadi Arna 'Yan Boko Aqida shi ne mata'i da kyalkyalin rayuwar Duniya. Wannan ya sa suke fifita Turawa da Yahudawa da Kiristoci a kan Musulmai, saboda kawai su suka fi cigaba a harkar boko da kere-kere da kimiyya da fasaha da gina rayuwar Duniya da samar da kayan jin dadi na zahiri.Wannan shi ne ma'auni a wajensu. Wato rayuwar da manufarta da amfaninta kawai iya Duniyar ce kadai. Wato a rayu rayuwa maras manufa, face a ci a sha a ji dadi, a biya sha'awar jinsi, a yi bacci, kamar dai rayuwar dabbobi, kamar yadda Allah ya ce:{وَالَّذِينَ كَفَرُوا يَتَمَتَّعُونَ وَيَأْكُلُونَ كَمَا تَأْكُلُ الْأَنْعَامُ وَالنَّارُ مَثْوًى لَهُمْ } [محمد: 12]"Wadanda suka kafirta suna jin dadin rayuwa, suna cin abinci kamar yadda dabbobi suke ci, alhali wuta ce makomarsu".Irin wannan cigaba cigaba ne na "madda" (material), ba cigaba ne na gyaran ruhi ba. Shi ya sa za ka ga su suke kira ga Ilhadi, da yada alfasha da bayyana tsiraici, da kira zuwa ga fita daga hankali da dabi'u na fidira (kamar auren jinsi) duka da sunan 'yanci.Alhali ma'auni na hakika shi ne samun sa'ada da rabo da arziki a Duniya da Lahira, sa'adar da take samar da nitsuwar zuciya da rayuwa mai dadi a Duniya, da samun rayuwar ni'ima a Lahira. Rayuwar da ta ginu a kan imani mai raya zukata da samar musu da nitsuwa, da tabbatuwa a kan "qiyam" da kyawawan halaye da dabi'u na fidira, masu gadar da daukaka da izza a cikin rayuwa.Shi ya sa Allah yake rarrashin Muminai, kar su rudu da rayuwa ta "madda" (Material), a'a, rayuwa ta imani bisa kyawawan halaye da dabi'u na fidira su ne ma'aunin daukaka da cigaba, Allah ya ce:{ وَلَا تَهِنُوا وَلَا تَحْزَنُوا وَأَنْتُمُ الْأَعْلَوْنَ إِنْ كُنْتُمْ مُؤْمِنِينَ } [آل عمران: 139]"Kada ku raunana, kada ku yi bakin ciki, ku ne madaukaka in kun kasance Muminai".Saboda haka muke kira ga Musulmai, kar su rudu da wannan cigaban da ake ta yi musu karya da ita, -wai- cigaban Turawa a rayuwar Duniya. Ina amfanin cigaban da bai hana mutum hasara a Lahira da zama mafi sharrin halitta ba?Allah ya ce:{إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ وَالْمُشْرِكِينَ فِي نَارِ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا أُولَئِكَ هُمْ شَرُّ الْبَرِيَّةِ } [البينة: 6]"Lallai wadanda suka kafirta cikin Ahlul Kitabi (Yahudu da Nasara) da Mushrikai, suna cikin wutar Jahannama, za su dawwama a cikinta, wadannan su ne mafi sharrin halitta". SU WAYE MAFI SHARRIN HALITTA? Ma'auni a wajen 'Yan Duniya, 'Yan Dadi Arna 'Yan Boko Aqida shi ne mata'i da kyalkyalin r... Cigaba da karantawa»
ABU RAYYAH YA BAYYANA A NIGERIAAn yi wani Munafuki a Misra, mai suna Mahmud Abu Rayyah, wanda yake ikirarin bincike da nazari da aiki da hankali a lamuran Addini. Wanda ta wannar hanya ya yi ta kai farmaki kan Sunnar Manzon Allah (saw), inda ya fara hakan a littafinsa mai suna:أضواءٌ على السنّةِ المُحمّديّةِA cikin wannan littafin ya isa ga cewa; ba za a yi aiki da Hadisan Annabi (saw) ba. Kuma ya dira kan Sahabban Annabi (saw), yana zaginsu daya bayan daya, musamman wadanda suka fi ruwaito Hadisan Annabi (saw). Wanda har ya isa kan Sahabi Abu Huraira (ra), ya dira a kansa, saboda shi ya fi sauran Sahabbai riwaya daga Annabi (saw), don in ya zubar da kimarsa to ya rushe kaso mai yawan gaske na Sunnar Annabi (saw).Abu Rayya ya dira a kan Sahabi Abu Huraira (ra), ya ci masa mutunci, ya fadi maganganu na batanci a kansa wanda hatta Rafidha 'Yan Shi'a ba su fada a kansa ba - duk da cewa; ya dogara sosai a kan Littafin wani Rafidhiy Dan Shi'a mai suna Abdulhussain Sharafuddeen, mai littafin "Al-Muraja'at"-. Karshe ya tuheme shi da karya, da kirkiran Hadisai. Kai, musamman ya rubuta littafi a kan Sahabi Abu Huraira (ra) yana ci masa zarafi:أبو هريرة شيخ المضيرةA daidai lokacin da yake cin mutuncin Sahabi Abu Huraira (ra), a lokacin ne kuma yake girmma kafirai, yake cewa; Yahudawa da Nasara za su shiga Aljanna, ya tabbatar da haka a cikin littafinsa mai suna:دين الله واحد علی ألسنة الرّسلTo amma duk da hargowa da hayagaga da ya yi ta yi, don karyata Sunna da zagin Sahabbai da ci musu mutunci, haka Tarihi ya yi wurgi da shi cikin bolarsa, bayan ya yi mutuwar wulakanci, ya mutu yana ihu. Aka manta da su shi da littatafan nasa, amma Hadisan Sahabi Abu Huraira (ra) kuwa har gobe ana karanta su, Musulmai suna aiki da su, a dukkan lamuran Addini da rayuwarsu, a kullum ana ta addu'ar neman yarda ga Sahabi Abu Huraira (ra).To kamar wannan Munafuki, a yanzu haka an samu wani mutum a Kano, yana nan yana bin irin wannan salo na Abu Rayyah, yana karyata Hadisai, ya zagin Sahabbai, yana tuhumarsu da karya da kirkiran Hadisai. Yanzu haka ya dira a kan Sahabi Anas bn Malik (ra), yana zaginsa da ci masa mutunc, -wai- shi ma yana so ya rushe Sunnar Annabi ta irin hanyar da Abu Rayyah ya bi, saboda Anas (ra) yana cikin masu yawan Hadisai daga Annabi (saw).Amma shi wannan mutumi, ya hada da bin wata hanya ta Mulhidai, masu cin zarafin Annabi (saw). Ta yadda yake daukan Hadisan da suka shafi mu'amalar Annabi (saw) da mata yana fassara su fassara ta batsa, yana nuna Annabi (saw) a matsayin mai lalata da mata. Alhali duk cikin Musulmai, tun farkon al'umma har yau, babu wanda ya taba fahimtar hakan daga Hadisan sai shi da sauran Munafukai masu sukar Manzon Allah (saw) da yakar Sunnarsa.To ala ayyi halin, wannan abin da yake yi aikin banza ne kawai. Kafin ya yi an samu daruruwa sun yi, tun daga kan Munafukai har zuwa cikin "Mustashriqun" (Orientalists) da Kafirai da Mulhidai, amma hakan babu abin da ya canza, al'umma ba su dena karanta Hadisan Abu Hurara (ra) da Anas bn Malik (ra) ba, ba su dena aiki da su ba, kuma a kullum aka kira sunayensu sai sun yi musu addu'ar neman yarda a wajen Allah an ce:رضيَ اللهُ عنهُ ABU RAYYAH YA BAYYANA A NIGERIA An yi wani Munafuki a Misra, mai suna Mahmud Abu Rayyah, wanda yake ikirarin bincike da nazari da aiki da h... Cigaba da karantawa»
SHAWARI GA GOMNATI KAN YAK'AR TUNANIN TA'ADDANCIA cikin wadannan shekaru kasarmu tana fama da Ta'addancin Khawarijawa da tarzomar Rafidha 'Yan Shi'a, to lallai ya kamata a san cewa; irin wadannan fitinu magance su gaba daya yana da matukar wahala, sai dai a yi kokarin galaba a kansu, da rage illa da hatsarinsu.Misali abin da ya shafi Ta'addancin Khawarijawa, - kamar Boko Haram -, ba za su gushe suna bayyana ba har karshen Duniya, kamar yadda ya zo a Hadisi:لا يزالون يخرجونمسند أحمد ط الرسالة (33/ 44)"Ba za su gushe suna fitowa ba".Sai dai duk lokacin da suka fito a datse su, amma hakan ba zai hana sake bayyanarsu a gaba ba. Annabi (s.a.w) ya ce:"كلما خرج قرن قطع أكثر من عشرين مرة- "حتى يخرج في عراضهم الدجال".سنن ابن ماجه ت الأرنؤوط (1/ 120)"Duk lokacin da kahonsu ya fito sai a yanke shi sau fiye da ishirin", - "Har sai Dajjal ya fito a bangarensu".Don haka daga cikin hanyoyi na kokarin yakar fitinar 'Yan Ta'adda da kuma 'Yan Tarzoma, akwai hanyoyi kamar haka da muke ba da shawara ga Gomnati ta yi aiki da su:1- Ya kamata Gomnati da al'umma su ba da goyon baya wa Malamai masu karantar da al'umma kyakkyawar Aqida, da kuma bayyana illar munanan Aqidu. Su kuma sai su yi amfani da kwarewa da ilimi da hikima suna koyar da mutane, suna fadakar da su da tsoratar da su munin Aqidun, musamman Aqidu masu kai wa ga Ta'addanci da Tarzoma.2- Hukuma da jami'an tsaro su bi dabaru na kwantar da tarzoma ba tare da ta rikede ta zama babbar fitina ta koma ta'addanci ba. Lallai muna kyautata zaton da ma jami'an tsaro suna da dabarun kwantar da tarzoma ba tare da ta bunkasa ta haifar da kungiyar ta'addanci ba.3- Daga cikin hanyoyi masu matukar amfani da ya kamata Gomnati tana bi wajen yakar tunanin ta'addanci da miyagun Aqidu, duka wadanda aka kama aka sanya a kurkuku, to a samu Malamai kwararru, masu ilimi da kwarewa da hikima suna zuwa suna tattaunawa da su, suna yaye musu shubuhohin da suka kai su ga wadannan munanan Aqidu da tunani. Saboda ita shubuha da ra'ayi da Aqida ba a yakarta da karfi sai da ilimi da hujja da bayani.Wannar babbar hanya ce da kasashe masu yaki da ta'addanci suke amfani da ita -musamman a kasar Saudiyya-, kuma ana cin nasarar raba 'Yan Ta'addan da tunanin ta'addanci da iznin Allah.A takaice dai, ta'addanci kalubale ne ga al'umma gaba daya, sai kowa ya ba da tasa gudumawa wajen yakar tunanin ta'addanci.Allah ya yi mana tsari da fitina, ya ba mu zaman lafiya. SHAWARI GA GOMNATI KAN YAK'AR TUNANIN TA'ADDANCI A cikin wadannan shekaru kasarmu tana fama da Ta'addancin Khawarijawa da tarz... Cigaba da karantawa»
*DA MUNGUWAR RAWA GARA KIN TASHI… (4)**YAYE SHUBUHOHIN MASU KARE SAYYID QUTUB A KAN AKIDARSA TA KHAWARIJANCI:*A rubutunmu kashi na (2) da na (3) da suka gabata mun yi raddi ga mai jingina "Hakimiyya" Akidar Khawarijawa ga Shaikh Muhammad bn Ibrahim Alu-Shaikh ta hanyar "Muqarana" tsakaninsa da Sayyid Qutub. Don saboda ba za a fahimci gaskiyar danganta masa "Hakimiyyar" ba sai ta hanyar "Muqarana" tsakanin Akidarsa da ta Sayyid Qutub din, mutumin da ya fi kowa tabbatar da "Hakimiyyar". Wannan ya sa muka bayyana wa mutane Akidar Sayyid Qutub don a banbance matsayarsa a kan mas'alolin Addini, da ta Shaikh Muhammad bn Ibrahim.To masu kare Sayyid Qutub din sun yi "I'itiradhaat" wadanda suke bukatar a yi jawabi a kansu, don raddin ya zama cikakke. Jawabin zai kasance ne ta hanyar bayanin wasu ka'idoji, da kuma "dabbaqa" su a kan maganganun Sayyid Qutub. Hakan zai kasance ne ta fiskoki biyar - da iznin Allah - kamar haka:1- DOLE NE LAZIMTAR LAFUZAN SHARI'A DADAI GWARGWADO A BABIN AQIDA:Yana daga cikin Manhajin Ahlus Sunna a Babin Mas'alolin Akida lazimtar lafuzan Shari'a iya iyawarsu. Saboda lafuzan Shari'a su ne suke rarrabe tsakanin karya da gaskiya. Wannan ya sa Magabata suke sanya Alkur'ani da Sunna a matsayin jagora wajen bayanin gaskiya. Sai su tabbatar da abin da Allah da Manzonsa suka tabbatar su kore abin da suka kore.Misali daga maganganun Salaf a kan haka:Imam al-Auza'iy an tambaye shi a kan lafazin "Jabar" sai ya ce:((ما أعرف للجبر أصلا من القرآن والسنة، فأهاب أن أقول ذلك ولكن القضاء والقدر والخلق والجبل، فهذا يعرف في القرآن والحديث عن رسول الله صلى الله عليه وسلم)).السنة لأبي بكر بن الخلال (3/ 555)، شرح أصول اعتقاد أهل السنة والجماعة (4/ 775)((Ban san asalin "Jabar" a Alkur'ani da Sunna ba, don haka ina tsoron fadinsa. Amma na san lafuzan "Qadha'u" da "Qadar" da "Khalq" da "Jabal", wadannan an sansu a Alkur'ani da Hadisi, daga Manzon Allah (saw))).Ibnu Taimiyya ya nakalto daga gare shi da Imam Ahmad da wasunsu ya ce:((قال الأوزاعي وأحمد ونحوهما: من قال إنه جبر فقد أخطأ، ومن قال لم يجبر فقد أخطأ، بل يقال: إن الله يهدي من يشاء ويضل من يشاء، ونحو ذلك.وقالوا: ليس للجبر أصل في الكتاب والسنة، وإنما الذي في السنة لفظ الجبل لا لفظ الجبر)).درء تعارض العقل والنقل (1/ 255)Akwai wasu misalan ma a kan haka.Saboda haka Manhaji ne na Ahlus Sunna yin amfani da lafuza na Shari'a a babin Akida, saboda su lafuza ne da suka kunshi gaskiya tsantsa.Amma duk da haka idan lafazi ma'anarsa mai kyau ne, ba ya dauke da mummunar ma'ana (ba lafazi ne "Mujmali" ba) suna iya amfani da shi, musamman idan ba su samu lafazi na Shari'a ba.2- NISANTAR LAFUZAN BIDI'A DA LAFUZA "MUJMALAI" DUNKULALLU:Kasancewar Ahlus Sunna suna takaituwa ne da lafuza na Shari'a, ko lafuza masu ma'anoni masu kyau, shi ya sa ba sa amfani da lafuza "Majmalai", wadanda suka kunshi ma'anoni masu kyau da kuma munana, balle kuma lafuza na Bidi'a. dalili a kan haka shi ne; saboda Manhajin Ahlus Sunna ya ginu ne a kan "Ittiba'i" (Bin Alkur'ani da Sunna), ba "Ibtida'i" ba (kirkiran Bidi'a).Ibnu taimiyya ya yi bayanin Manhajin Ahlus Sunna a wannar ka'ida inda ya ce:((يوجد كثيرا في كلام السلف والأئمة النهي عن إطلاق موارد النزاع بالنفي والإثبات، وليس ذلك لخلو النقيضين عن الحق، ولا قصور، أو تقصير في بيان الحق، ولكن لأن تلك العبارة من الألفاظ المجملة المتشابهة المشتملة علي حق وباطل، ففي إثباتها إثبات حق وباطل، وفي نفيها نفي حق وباطل، فيمنع من كلا الإطلاقين، بخلف النصوص الإلهية فإنها فرقان فرق الله بها بين الحق والباطل، ولهذا كان سلف الأمة وأئمتها يجعلون كلام الله ورسوله هو الإمام والفرقان الذي يجب اتباعه، فيثبتون ما أثبته الله ورسوله، وينفون ما نفاه الله ورسوله، ويجعلون العبارات المحدثة المجملة المتشابهة ممنوعا من إطلاقها: نفيا إثباتا، لا يطلقون اللفظ ولا ينفونه إلا بعد الاستفسار والتفصيل، فإذا تبين المعني أثبت حقه ونفي باطله، بخلاف كلام الله ورسوله، فإنه حق يجب قبوله، وإن لم يفهم معناه، وكلام غير المعصوم لا يجب قبوله حتى يفهم معناه)).درء تعارض العقل والنقل (1/ 76)Sai Ibnu Taimiyya ya bayyana cewa; Salaf da A'imma suna hani a kan yin amfani da lafuza da aka yi sabani a kansu, saboda lafuza ne dunkulallu masu rikitarwa, wadanda suka kunshi karya da gaskiya. Idan aka fade su aka tabbatar da su an tabbatar da karyan da ke cikin lafazin, haka idan aka kore shi an kore gaskiyar da ke cikinsa. Don haka Salaf suke sanya Alkur'ani da Sunna a matsayin su ne jagora gare su, saboda su suke rarrabe tsakanin karya da gaskiya.Wannan lafazi "Mujmali" kenan, ina kuma ga lafazi na bidi'a kirkirarre?!Saboda haka hanyar Ahlus Sunna a babin Addini, musamman mas'alolin Akida ba sa amfani da lafuza dunkulallu balle kirkirarru na Bidi'a. Kawai suna takaituwa ne a kan lafuza na Shari'a, iya iyawarsu. Sai dai idan babu sai su yi amfani da lafazi mai kyakkyawar ma'ana zalla. Ibnu Taimiyya ya yi bayanin haka inda ya ce:((طريقة السلف والأئمة أنهم يراعون المعاني الصحيحة المعلومة بالشرع والعقل، ويراعون أيضا الألفاظ الشرعية، فيعبرون بها ما وجدوا إلى ذلك سبيلا، ومن تكلم بما فيه معنى باطل يخالف الكتاب والسنة ردوا عليه، ومن تكلم بلفظ مبتدع يحتمل حقا وباطلا نسبوه إلى البدعة أيضا)).درء تعارض العقل والنقل (1/ 254)((Hanyar Salaf da A'imma: suna kiyaye ingantattun ma'anoni da suke sanannu a Shari'a da hankali, kuma suna kiyaye amfani da lafuza na Shari'a, da su suke bayanin Akidarsu dadai gwargwado. Amma wanda ya yi magana da lafazin da a cikinsa akwai mummunar ma'ana, wacce ta saba ma Alkur'ani da Sunna to za su watsar masa kayansa, haka wanda ya yi magana da lafazi na Bidi'a, wanda yake daukar karya da gaskiya to shi ma za su danganta shi ga Bidi'a)).Wannan shi ne hanyar Ahlus Sunna. Wanda yake yin amfani da lafazi na Bidi'a to ana danganta shi da Bidi'ar kai tsaye, saboda ya fadi magana ta Bidi'a, ya aikata Bidi'a ta magana.3- MANHAJIN SAYYID QUTUB SHI NE AMFANI DA LAFUZA "MUJMALAI" DA NA BIDI'A:To idan an fahimci abin da ya gabata, za mu ga cewa: Sayyid Qutub ya yi amfani da lafuzan da Khawarijawa suke amfani da su, wajen bayanin hakikanin Imani da Muslunci da Addini. Ga misalansu kamar haka:1) Addini abu ne guda daya dunkule ba ya rarrabuwa:((حقيقة هذا الدين.. إنه وحدة لا تتجزأ)).في ظلال القرآن (1/ 164)Ya ce:((فالدينونة لله كل لا يتجزأ)).في ظلال القرآن (4/ 2145)2) Imani abu ne guda daya ba ya rarrabuwa:Ya ce:((إن الإيمان وحدة لا تتجزأ))في ظلال القرآن (2/ 798)Ya ce:((العقيدة التي تؤمن بها.. في وحدة لا تتجزأ ولا تفترق عناصرها..))في ظلال القرآن (2/ 687)3) Muslunci abu ne guda daya ba ya rarrabuwa:Ya ce:((الإسلام يأخذها كلا لا يتجزأ)).في ظلال القرآن (6/ 3988)4) Shari'a abu ne guda daya ba ta rarrabuwa:Ya ce:((إن شريعة الله كل لا يتجزأ)).في ظلال القرآن (2/ 841)Ya ce:((يصبح المنهج الإلهي وحدة واحدة. لا تتجزأ ولا تتفرق)).في ظلال القرآن (1/ 177)To a nan Sayyid Qutub ya yi amfani da lafuza nau'i biyu:NAU'I NA FARKO:Sayyid Qutub ya yi amfani da lafazi "Mujmali", (وحدة واحدة), wannan lafazi ne dunkulalle. Bai zo a Shari'a ba, kuma zai iya daukar ma'ana mai kyau, zai dauki mummunar ma'ana. Mummunar ma'anar da zai dauka shi ne ma'anar da 'Yan Bidi'a suke nufi, cewa: Imani abu ne guda daya a dunkule (الإيمان حقيقة واحدة).Don haka a nan sai mu ce: me ya sa Sayyid Qutub bai yi amfani da lafazi na Shari'a ba? Idan kuma babu, me ya sa bai yi amfani da lafazi mai ingantaccen ma'ana ba? Misali ya ce:1. ((الدين شامل))، ((الدين متكامل))، ((الدين جامع))، ((الدين عام))2. ((الإيمان شامل))، ((الإيمان متكامل))، ((الإيمان جامع))، ((الإيمان عام))3. ((الإسلام شامل))، ((الإسلام متكامل))، ((الإسلام جامع))، ((الإسلام عام))4. ((الشريعة شاملة))، ((الشريعة متكاملة))، ((الشريعة جامعة))، ((الشريعة عامة))NAU'I NA BIYU:Haka kuma Sayyid Qutub ya yi amfani da lafazin Bidi'a, inda ya yi ta yin amfani da lafazin (لا تتجزأ ولا تتفرق). Wannan lafazin 'Yan Bidi'a ne, Wa'eediyya (Khawarijawa da Mu'utazila), da kuma Murji'a (Jahamiyya da Karramiyya da Asha'ira d.s). Su suka kirkiri lafazin don su tabbatar da Bidi'o'insu a babin Imani. Su Murji'a suka ce: Imani ba ya rarrabuwa, don haka idan aka samu sashensa to gaba daya ya tabbata. Mutum ya zama mai cikakken imani.Su kuma Khawarijawa suka ce: Imani ba ya rarrabuwa, don haka idan aka rasa sashensa to gaba daya an rasa shi. A kan haka Ibnu Taimiyya ya ce:((قالت الخوارج والمعتزلة قد علمنا يقينا أن الأعمال من الإيمان فمن تركها فقد ترك بعض الإيمان وإذا زال بعضه زال جميعه؛ لأن الإيمان لا يتبعض ولا يكون في العبد إيمان ونفاق فيكون أصحاب الذنوب مخلدين في النار إذ كان ليس معهم من الإيمان شيء)).مجموع الفتاوى (13/ 48)Ka ga sai Ibnu Taimiyya ya yi bayanin ra'ayin Khawarijawa da Mu'utazila, a ciki sai ya nuna cewa hujjar ra'ayinsu ita ce:((لأن الإيمان لا يتبعض)).((Saboda Imani ba ya rarrabuwa)).A wani wajen kuma, yana bayanin cewa: shubuhar Murji'a iri daya ce da ta Khawarijawa sai ya ce:((وإنما أوقع هؤلاء كلهم ما أوقع الخوارج والمعتزلة في ظنهم أن الإيمان لا يتبعض بل إذا ذهب بعضه ذهب كله ومذهب أهل السنة والجماعة أنه يتبعض وأنه ينقص ولا يزول جميعه كما قال النبي صلى الله عليه وسلم: «يخرج من النار من كان في قلبه مثقال ذرة من الإيمان»))شرح العقيدة الأصفهانية (ص: 197)Sai Ibnu Taimiyya ya bayyana cewa; Khawarijawa ma – kamar sauran 'yan bidi'a – duka sun tafi ne a kan cewa; Imani abu daya ne ba ya rarrabuwa, ta yadda idan sashensa ya gushe to gaba daya imanin zai gushe, sai mutum ya fita daga Muslunci.Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya ce:((المعتزلة والخوارج قالوا: إن الإيمان قول وعمل لكن لا يتبعض ولا يتجزأ، قالوا: إن ترك المعصية وفعل الطاعة إيمان، فإذا فعل الموحد المعصية، أو ترك الطاعة زال عنه الإيمان بالكلية. ثم الخوارج تكفره، والمعتزلة تجعل له منزلة بين منزلتين. وافقوا أهل السنة في أصل الإيمان أنه قول وعمل، لكن خالفوهم فقالوا: لا يتبعض ولا يتجزأ)).شرح العقيدة الواسطية (ص: 128)Shi ya sa Ibnu Taimiyyan yana musu raddi sai ya ce:((قد ثبت في الصحيح عن النبي صلى الله عليه وسلم {إن الله يخرج من النار من كان في قلبه مثقال دينار من إيمان} وفي رواية: {مثقال دينار من خير ثم يخرج من النار من كان في قلبه مثقال حبة من خردل من إيمان} " وفي رواية " من خير " " {ويخرج من النار من كان في قلبه مثقال ذرة من إيمان أو خير} " وهذا وأمثاله من النصوص المستفيضة عن النبي صلى الله عليه وسلم يدل أنه لا يخلد في النار من معه شيء من الإيمان والخير وإن كان قليلا وأن الإيمان مما يتبعض ويتجزأ)).مجموع الفتاوى (12/ 491 - 492)Ka ga sai ya nuna cewa: Akwai nassoshi masu yawa da suke nuni a kan cewa:((إن الإيمان مما يتبعض ويتجزأ)).((Imani abu ne da yake rarrabuwa bangare – bangare, yanki - yanki)).Saboda haka wannan lafazi da Sayyid Qutub ya yi amfani da shi (لا تتجزأ ولا تتفرق) lafazi ne na Bidi'a, don haka dole a danganta shi ga Bidi'a, kamar yadda Ibnu Taimiyya ya fada a maganarsa da ta gabata.Da wannan za mu tabbatar da cewa; da ma fa asali shi Sayyid Qutub ba a bisa Manhajin Ahlus Sunna yake magana ba, bisa Manhaji ne na Bidi'a. Shi ya sa ya zo ya yi ta magana a game da Addini yadda ya ga dama, alhali shi rubutu a Addini ba rubutu a Adabi ba ne.Haka su ma masu kare shi, asali ba Manhajin Ahlus Sunnan suka sani ba, shi ya sa suka zo suna ta dikake da kame-kame, -wai- su a dole sai sun yi tawili, sun murda maganar Sayyid Qutub, sun wanke shi daga asalin Akidarsa. To ai hakan ba za ta yiwu ba. Saboda mujarradin yin amfani da lafuzan da ya yi amfani da su, ya yi magana a kan Imani, Addini, Muslunci da Shari'a, lafuza ne na Bidi'a. Kuma an tabbatar da cewa; na bidi'ar Khawarijawa ne. Saboda haka babu wanda zai yi inkarin cewa; Akidar Sayyid Qutub Akida ce ta Khawarijawa sai jahili, wanda bai san Akidar Ahlus Sunna da Manhajinsu ba, kuma bai san Akidun Khawarijawa ba. Ko kuma mai son zuciya, wanda zai yi amfani da tawili ya boye sharrin da ke cikin maganarsa, alhali ba zai yi amfani a nan ba, saboda matsalar ba ta ma'ana ba ce kadai, a'a, ta shafi yin amfani da lafuzan kansu.4- ABUBUWA DA SUKE TABBATAR DA CEWA: AKIDAR SAYYID QUTUB TA KHAWARIJANCI CE:Da ma ita Akidar Khawarijawa a aikace take bayyana. Bayan sun kudurce cewa; Imani abu daya ne dunkulalle wanda ba ya rarrabuwa, sai kuma su zartas da wadannan aiyuka masu zuwa a aikace:(1) KAFIRTA AL'UMMA:Babban abin da manazarta da Malamai har da jagororin Ikhwan suka zargi Sayyid Qutub da shi shi ne cewa; shi ya haifar da tunanin Kafirta Musulmai a wannan zamani. Saboda shi ya yi ta kafirta al'umma a cikin littatafansa, yana cewa; kowa ya yi ridda, an koma Jahiliyya, yanzu babu al'umma Musulma, kai, babu ma Musulmai. Don haka dole mutane su sake sabon shiga Muslunci.A baya na kawo maganganunsa a kan haka, da maganganun manazarta da malaman, babu bukatar sai na sake maimaitawa.(2) FITA DAGA JAMA'A:Fita daga jama'a da kauracewa al'umma yana daga cikin ginshikan Khawarijanci. A fita daga garin kafirci da jahiliyya a koma garin Muslunci. Ya tabbatar da haka a cikin littatafansa a wurare da yawa, daga ciki ya ce:((فأما اليوم وقد عادت الأرض إلى الجاهلية وارتفع حكم الله- سبحانه- عن حياة الناس في الأرض، وعادت الحاكمية إلى الطاغوت في الأرض كلها، ودخل الناس في عبادة العباد بعد إذ أخرجهم الإسلام منها.. الآن تبدأ جولة جديدة أخرى للإسلام- كالجولة الأولى- تأخذ- في التنظيم- كل أحكامها المرحلية، حتى تنتهي إلى إقامة دار إسلام وهجرة ثم تمتد ظلال الإسلام مرة أخرى- بإذن الله- فلا تعود هجرة ولكن جهاد وعمل كما حدث في الجولة الأولى.. في ظلال القرآن (3/ 1560)Ya ce:((إن الجاهلية جاهلية، والإسلام إسلام. والفارق بينهما بعيد. والسبيل هو الخروج عن الجاهلية بجملتها إلى الإسلام بجملته. هو الانسلاخ من الجاهلية بكل ما فيها والهجرة إلى الإسلام بكل ما فيه.وأول خطوة في الطريق هي تميز الداعية وشعوره بالانعزال التام عن الجاهلية: تصورا ومنهجا وعملا. الانعزال الذي لا يسمح بالالتقاء في منتصف الطريق. والانفصال الذي يستحيل معه التعاون إلا إذا انتقل أهل الجاهلية من جاهليتهم بكليتهم إلى الإسلام.لا ترقيع. ولا أنصاف حلول. ولا التقاء في منتصف الطريق.. مهما تزيت الجاهلية بزي الإسلام، أو ادعت هذا العنوان! وتميز هذه الصورة في شعور الداعية هو حجر الأساس. شعوره بأنه شيء آخر غير هؤلاء. لهم دينهم وله دينه، لهم طريقهم وله طريقه. لا يملك أن يسايرهم خطوة واحدة في طريقهم. ووظيفته أن يسيرهم في طريقه هو، بلا مداهنة ولا نزول عن قليل من دينه أو كثير! وإلا فهي البراءة الكاملة، والمفاصلة التامة، والحسم الصريح.. «لَكُمْ دِينُكُمْ وَلِيَ دِينِ» ..وما أحوج الداعين إلى الإسلام اليوم إلى هذه البراءة وهذه المفاصلة وهذا الحسم.. ما أحوجهم إلى الشعور بأنهم ينشئون الإسلام من جديد في بيئة جاهلية منحرفة، وفي أناس سبق لهم أن عرفوا العقيدة، ثم طال عليهم الأمد «فَقَسَتْ قُلُوبُهُمْ وَكَثِيرٌ مِنْهُمْ فاسِقُونَ» .. وأنه ليس هناك أنصاف حلول، ولا التقاء في منتصف الطريق، ولا إصلاح عيوب، ولا ترقيع مناهج.. إنما هي الدعوة إلى الإسلام كالدعوة إليه أول ما كان، الدعوة بين الجاهلية. والتميز الكامل عن الجاهلية.. «لَكُمْ دِينُكُمْ وَلِيَ دِينِ» .. وهذا هو ديني: التوحيد الخالص الذي يتلقى تصوراته وقيمه، وعقيدته وشريعته.. كلها من الله.. دون شريك.. كلها.. في كل نواحي الحياة والسلوك.وبغير هذه المفاصلة. سيبقى الغبش وتبقى المداهنة ويبقى اللبس ويبقى الترقيع.. والدعوة إلى الإسلام لا تقوم على هذه الأسس المدخولة الواهنة الضعيفة. إنها لا تقوم إلا على الحسم والصراحة والشجاعة والوضوح..وهذا هو طريق الدعوة الأول: «لَكُمْ دِينُكُمْ وَلِيَ دِينِ» ..)).في ظلال القرآن (6/ 3992 – 3993)(3) DAUKAR MAKAMI A KAN AL'UMMA SUNA KASHE MUSULMAI:Wannan shi ne babbar sifar Khawarijawa wacce Annabi (saw) ya fade ta a Hadisi:((يقتلون أهل الإسلام ويدعون أهل الأوثان)).To wannan ne wanda Sayyid bai yi ba. Alhamdu lillahi, saboda don an kama shi, an kulle shi a kurkuku, har daga karshe aka kashe shi. Amma matasan da suka tasirantu da Fikrorinsa su sun dauki makami sun kashe Musulmai. An samu kungiyoyi da yawa a sassan Duniya, har mu ma a Nigeria aka samu Boko Haram.Da ma Sayyid din ya nuna cewa: ko ya mutu Fikrorinsa ba za su mutu ba, za su wanzu a cikin tunanin mutane, suna aiki da su, zai zama kamar yana raye. Wannan ya sa wani masoyinsa ya rubuta littafi mai suna:سيد قطب الشهيد الحي – الدكتور صلاح الخالدي.Ma'ana: Rayayyen Shahidi. Ya mutu amma kamar yana raye, saboda Fikrorinsa suna nan suna tasiri a kan matasa, kuma suna aiki da su, suna kashe Musulmai da sunan Jihadi, saboda sun bar "Hakimiyya". Daga cikin wadanda suka tabbatar da haka akwai Abdallah Azzam, kamar yadda a can baya na yi posting na maganarsa. Da sauransu suna nan da yawa.5- Na bibiyi rubutun masu "I'itiradhi" daga cikinsu har da wanda nake yi masa raddi, amma abin mamaki sai na ga kwata – kwata ba su ma fahimci inda ni na dosa ba.Abin da su ba su sani ba shi ne; Magana a kan wannar mas'ala ba magana ce ta ma'ana kadai ba, balle har su tuhume ni da Tadlisi da Talbisi da sauran maganganunsu. A'a, farko magana ce ta LAFAZI. Shi Sayyid Qutub - saboda bai san Manhajin Ahlus Sunna ba - ya zo ya yi ta yin magana da lafuza "Mujmalai" da kuma lafuza na Bidi'a, wajen bayanin "haqa'iq" na Addini. Ya yi magana a kan Addini da irin yaren da ya saba yin rubutu a jaridu da rubutun Adabin Larabci da yake yi, alhali shi Addini ba a masa haka.Saboda haka ba magana ake yi ta Siyaki ba. A'a, magana ce ta Sayyid ya yi amfani da lafazi "Mujmali" (وحدة), kuma ya yi amfani da lafazin Bidi'a, a inda 'yan Bidi'an suke amfani da shi, wato lafazin (لا يتجزأ ولا يتفرق), wajen bayyana hakikanin Imani. To a nan akwai abubuwa guda biyu:Na farko: amfani da lafuzan kansu Bidi'a ne.Na biyu: Duk wanda ya yi amfani da lafazin (لا يتجزأ ولا يتفرق) wajen bayanin hakikanin Imani, kamar yadda Sayyid ya ce:((إن الإيمان وحدة لا تتجزأ))في ظلال القرآن (2/ 798)To dole a jingina shi ga 'Yan Bidi'a a Babin Hakikanin Imani. Sai a duba a gani, a bangaren Murji'a yake ko kuma Khawarijawa da Mu'utazila?To da muka duba sai muka ga Sayyid Qutub a bangaren Khawarijawa yake, saboda ya nuna cewa: dole ne mutum ya bi Muslunci a dunkulensa, idan ya bi hukunci daya wanda ba na Muslunci ba to ya bar Musluncin, ko da kuwa yana girmama Akida yana cewa: shi Musulmi ne.Da a ce: Sayyid ba Akidar Khawarijanci yake tabbatarwa ba, da sai ya yi amfani da lafuza masu ma'ana mai kyau, wadanda ba za su nuna Akidar Khawarijanci ba. Kamar ya ce:((الإيمان شامل))، أو ((الإيمان متكامل))، أو ((الإيمان جامع)) ونحو ذلك.Amma sai ya karfafa maganarsa da lafazin 'Yan Bidi'a ya ce:((لا يتجزأ)) ((ولا تتفرق)).Saboda haka babu wanda ya isa ya wanke Sayyid Qutub daga Akidar Khawarijawa, saboda abin da ya rubuta kenan a cikin littafinsa.Shi ya sa a baya na kawo maganar Ibnu Taimiyya inda ya ce:((ومن تكلم بما فيه معنى باطل يخالف الكتاب والسنة ردوا عليه، ومن تكلم بلفظ مبتدع يحتمل حقا وباطلا نسبوه إلى البدعة أيضا)).درء تعارض العقل والنقل (1/ 254)((Duk wanda ya yi magana da lafazin da akwai mummunar ma'ana a cikinsa wacce ta saba Alkur'ani da Sunna Salaf suna jefa masa kayansa, haka wanda ya yi magana da lafazin Bidi'a ma, wanda yake dauke da karya da gaskiya, suna JINGINA SHI GA BIDI'A)).Shi kuma Sayyid Qutub lafuzan da ya yi amfani da su, sun saba ma Alkur'ani da Sunna, saboda Nassoshin Alkur'ani da Sunna sun tabbatar mana cewa; Imani sassa ne daban daban, yana rarrabuwa. Idan sashen ya tafi sauran sashen yana nan bai gushe ba. Annabi (saw) ya ce:«الإيمان بضع وستون شعبة، والحياء شعبة من الإيمان» وفي رواية: «بضع وسبعون شعبة».صحيح البخاري (1/ 11) صحيح مسلم (1/ 63)((Imani rassa sittin da wani abu ne, - ko saba'in da wani abu – kunya reshe ne na imani)).Kuma Hadisin Jibreel (as) ya tabbatar mana cewa; Addini martabobi uku ne, don haka yana rarrabuwa.To a hakan ne wani masani Adabin Larabci zai zo ya ce mana Addini: ((وحدة لا تتجزأ)), (Imani abu ne guda daya a dunkule ba ya rarrabuwa), kuma a kyale shi?!Haba, a ina aka taba yin haka. In haka ne kowane Dan Bidi'a a tsawon Tarihi sai ku zo ku yi tawilin maganganunsu, ku kare su!Amma su masu kare shi ido rufe, wadanda a dole sai sun wanke mai laifi, matsalarsu ita ce; sun tsoma baki ne a abin ba su da ilimi a kansa. Shi ya sa mai raddi ya zo ya yi dogon rubutu, amma maras ma'ana, saboda bai san abin da ake magana a kansa ba.A takaice, Sayyid Qutub dan bidi'a ne, mai Akida ta Khawarijawa, saboda dalilan da muka ambata a baya.✍️ *Dr Aliyu Muh'd Sani (H)* *31 October, 2021* *DA MUNGUWAR RAWA GARA KIN TASHI… (4)* *YAYE SHUBUHOHIN MASU KARE SAYYID QUTUB A KAN AKIDARSA TA KHAWARIJANCI:* A rubutunmu kashi na (2) da... Cigaba da karantawa»
*DA MUNGUWAR RAWA GARA KIN TASHI… (3)*HAKIMIYYA TSAKANIN MUFTIY SHAIKH MUH'D BN IBRAHIM ALU-SHAIKH, DA SAYYID QUTUB (B ):RADDI A FASSALE:A rubutunmu na jiya mun bayyana wa jama'a banbanci tsakanin Akidar Shaikh Muhammad bn Ibrahim da Akidar Sayyid Qutub a Babin "Hakikanin Addini da Imani da Muslunci", inda muka ga cewa; Akidar Shaikh Muhammad bn Ibrahim Akidar Ahlus Sunna ce, shi kuma Sayyid Qutub Akidarsa irin ta Khawarijawa ce. Da wannan za mu san Alkiblar kowanne daga cikinsa idan zai yi magana a kan kowace mas'ala ta Akida.Sa'annan kuma mun ga cewa; Lafazin "Hakimiyya" lafazi ne "Mujmali" dunkulalle, wanda ya kunshi karya da gaskiya. Su kuma Ahlus Sunna ba sa amfani da lafazi "Mujmali" sai bayan an fayyace ma'anarsa, aka san cewa; bai saba ma Shari'a ba. Wannan ya sa ba a samu inda Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya yi amfani da lafazin ba, musamman saboda ba lafazi ne sananne a wajen Malamai ba. A wajen Maududiy lafazin ya fara bayyana, Sayyid Qutub kuma ya dauke shi ya yi ta yada shi, bayan ya kirkiri wasu Bidi'o'in khawarijawa, na kafirta al'umma ya kara a kan na Maududiy.Don haka "Hakimiyya" a wajen Sayyid Qutub tana da wani Mafhumi daban, ta yadda ya bayyana mana cewa; ma'anarta ita ce: Ra'ayin Khawarijawan farko, wadanda ake kiransu da "Muhakkimah", wadanda suka balle daga Sayyidina Aliyu (ra) bisa kadhiyyar "Tahkimi" (nada masu hukunci guda biyu), wanda hakan ya sa aka kira su Khawarijawan da sunan: "Muhakkimah".Saboda haka Shaikh Muhammad bn Ibrahim ba shi da alaka da "Hakimiyya", saboda ba shi da alaka da Khawarijanci, kuma bai taba amfani da lafazin ba, kuma bai taba kafirta al'ummar Musulmi ba, bai taba siffanta al'umma da Jahiliyya ba, bai taba cewa: a yanzu babu al'ummar Musulmi ba, alhali mun ga Sayyid Qutub ya fadi wadannan duka a dalilin "Hakimiyya".Saboda haka cigaba raddinmu zai kasance ne kashi biyu kamar haka:(A) AKIDAR SHAIKH MUHAMMAD BN IBRAHIM A BABIN "IMAMA" DA SHUGABANCI:Daga cikin abubuwan da za su kara tabbatar maka cewa: Shaikh Muhammad bn Ibrahim ba shi da alaka da "Hakimiyya" akwai mas'alolin Babin " Imama" da Shugabanci. Idan ka duba maganganunsa a Babin za ka ga ya tabbatar da mas'alolin ne bisa Akida da Manhajin Ahlus Sunna, sabanin yadda lamarin yake a wajen Sayyid Qutub, wanda shi yake ganin kwata-kwata babu ma shugaba da ya wajaba a yi masa da'a a bayan kasa. Hasali ma babu wata hukuma, kai, babu ma al'ummar Musulmi, duka a cikin Jahiliyya ake, irin Jahiliyyar Larabawa kafin zuwan Muslunci.Don haka lura da bayanan da Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya yi a kan mas'alolin babin na Imama da shugabanci, wadanda Sayyid Qutub ya saba ma Ahlus Sunna a cikinsu, zai kara tabbatar mana da barrantarsa daga "Hakimiyyar" da su Sayyid Qutub din suka kirkira, suka kafirta al'umma da ita. Ga mas'alolin kamar haka:1) HANYOYIN NADA SHUGABA:Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya tabbatar da cewa: daga cikin hanyoyin nada shugaba a Shari'a akwai GALABA (juyin mulki), da kuma NADI, (ولاية العهد), kamar yadda tsarin shugabanci yake a Kasar Saudiyya. Ya ce:((نصب الإمام ضروري يسمع له ويطاع. ثم نعلم أن الولاية تثبت بأمور:منها: نصب أهل الحل والعقد، وهو الذي نص هنا.ومنها: أن يأخذها قهرا بسيفه ومن معه، ويكون فيه الأمر الكافي، ويقهر غيره لا يرجع إلى أحد فإنه يثبت له حكم الولاية.الثالث: أن يعهد إليه ممن قبله.والكل والمدار هو إقامة الشرع وحفظ كيان الأمة والقيام بحقوقهم))فتاوى ورسائل سماحة الشيخ محمد بن إبراهيم بن عبد اللطيف آل الشيخ (12/ 173)To ka ga a nan sai ya tabbatar da hanyoyi uku na kafa shugaba a Shari'a: Zabe ta hanyar shura, juyin mulki, da kuma ta hanyar shugaba ya nada wanda zai gaje shi.Hanya ta ukun ita ake bi a Saudiyya, wannan ya sa 'Yan Ikhwan suke tsananin adawa da Saudiyya, saboda a bisa wannan tsari babu yadda za a yi su cimma mafarkinsu, na kafa Daula da Khilafa karkashin Murshidin Ikhwan, kamar yadda a yanzu Iran take karkashin Khamenei. Saboda sun san duk wata Khilafa ko Daula da sunan Muslunci ba za ta yiwu ba matukar Makka da Madina ba sa karkashin ikonsu. Wannan ya sa suke bakar adawa da kasar ta Saudiyya, saboda babu hanyar da Ikhwan za ta yi mulki a kasar.2) DA'A MA SHUGABA:Manhajin Shaikh Muhammad bn Ibrahim a mas'alar da'a ma shugabanni irin Manhajin Ahlus Sunna ne, wato wajabcin yi musu da'a. Sabanin Sayyid Qutub da ya kafirta shugabannin da talakawan da kowa da kowa, ya ce: duka an koma Jahiliyya, dole a sake sabon samar da Musulmai daga zero, don babu Musulmai a Duniya. Duka ya fadi wannan ne saboda Akidar "Hakimiyya".Ga maganar Shaikh Muhammad bn Ibrahim yana umurtan wasu mutane da yin da'a ma shugaba, su je wajensa su ba shi goyon baya da hadin kai:(3870 - طلبه من بعض (الإخوان) القدوم إلى الإمام لاجتماع الكلمة ومناقشة المشاكل مع العلماء.)Sai ya ce: ((فاعلموا وفقكم الله أن عقيدتي التي أنا عليها أنى أدين الله بالنصح والمحبة لكم ولجميع إخواننا المسلمين إلى أن ألقى الله عز وجل, وأهم شيء أناصحكم فيه وأعظمه إجابة داعي الشرع وأن لا تلتفتوا عنه يمنه أو يسره, ومن ذلك إجابه داعي إمام المسلمين ما لم يدع إلى الاجتماع على المعصية , وإنما دعا إلى الاجتماع على طاعة الله وعدم التفرق والاختلاف , وجميع المشائخ يرون ذلك ويفتون به , وعدم قدومكم على أمامكم وعلمائكم من الأمور التي لا يرضى بها لكم من في قلبه أدنى محبة لكم أعنى المحبة الدينية , وهو من أعظم الأمور التي يفرح بها عليكم وعلى جميع المسلمين أعداء الدين من الكفار والمنافقين , ومن أعظم أسباب شق العصا , وهذا كتاب الله ونفا ير الأئمة له , وسنة رسول الله صلى الله وعليه وسلام مدونة بشروحها المبينة للمقصود منها , وفى ذلك كله حل المشكل , وكشف الاشباه , والشفاء لكل داء , والكفالة بالفلاح والهدى , والنجاة من المهالك والردى...والمقصود بيان وجوب القدوم على أمام المسلمين وفرضيته عليكم, وليس لكم عذر في التخلف ولا حجة. فان ذلك من السمع والطاعة التي أوجبها الله ورسوله, لاسيما وهو يدعوكم إلى الشريعة والرجوع فيما يشكل إلى حملتها))فتاوى ورسائل سماحة الشيخ محمد بن إبراهيم بن عبد اللطيف آل الشيخ (12/ 170 - 171)A nan sai ya bayyana cewa; Akidarsa ita ce son Musulmai, kuma 'yan'uwansa ne, da yi musu Nasiha a kan amsa kiran shugaban Musulmai da yi masa da'a.3) HANI A KAN TAWAYE DA KHURUJI WA SHUGABANNI:((لأحاديث طافحة بالمنع من الخروج على الأئمة وأن بغوا وظالموا. هذا ما لم يروا منهم كفرا بواحا كما في الحديث وقوله: (عندكم من الله فيه برهان) على أنه كفر، وفي حديث أخر (ما صلوا) المعني ما داموا بصفه الإسلام ما فيه إلا كبائر ومعاصي وجور وظلم هذه لا تمنع ولأيته)).فتاوى ورسائل سماحة الشيخ محمد بن إبراهيم بن عبد اللطيف آل الشيخ (12/ 169)A nan sai ya tabbatar da abin da Hadisai suka zo da shi, cewa; ba a tawaye wa shugaba matukar dai yana amsa sunan Musulmi. Sai idan ya kafirta, bisa hujja tabbatacciya kamar rana a tsakiyar sama.Don haka a fili yake Shaikh Muhammad bn Ibrahim Akidarsa da Manhajinsa na Ahlus Sunna ne a babin Imama da shugabanci. Ba ya kafirta al'umma, ya ce: babu al'ummar Musulmi, ko ya ce: an koma Jahiliyya, da makamancin haka cikin abin da Sayyid Qutub ya yi ta fada, saboda Akidarsa ta "Hakimiyya".Saboda haka, idan lamarin haka yake, ta yaya mai ilimi, kuma mai adalci zai jingina "Hakimiyya" ga Shaikh Muhammad bn Ibrahim?!Kuma Akidar Shaikh Muhammad bn Ibrahim a wannan babi raddi ne ga 'Yan Kungiyar Ikhwan tare da Qutubawansu, ta yadda muka ga Shaikh Muhammad bn Ibrahim a kan Manhajin Ahlus Sunna yake a wannan babin, sabanin su da suke kan Manhajin Khawarijawa, amma suke fakewa da maganganunsa, suke tallata bataccen Manhajinsu. Saboda haka kasancewar sun saba masa a wannan babi, ba za mu yarda su fake da Shaikh Muhammad bn Ibrahim a mas'alar "Hukunci da abin da Allah ya saukar" ba, don kawai su tallata Bidi'ar "Hakimiyya".(B ) MAZHABAR SHAIKH MUHAMMAD BN IBRAHIM A MAS'ALAR HUKUNCI DA SABANIN ABIN DA ALLAH YA SAUKAR:Asali abin da Malamai suka sani shi ne wajabcin yin hukunci da Shari'ar da Allah ya saukar ma bayi. Duka Malamai sun yi Ijma'i a kan haka, saboda Allah ya yi hani a kan yin hukunci da sabanin abin da ya saukar. Shi ya sa suke kiran mas'alar da sunan: "Yin hukunci da abin da ba Allah ne ya saukar ba" (الحكم بغير ما أنزل الله).To amma kasancewar Manhaji ne na 'Yan Bidi'a, ba sa takaituwa da lafuzan Shari'a, sai su yi amfani da wasu lafuza "Mujmalai", wadanda suke iya daukar karya da gaskiya, don su kunsa Bidi'o'in da suka kirkira a cikin lafazin. To haka shi ma lafazin "Hakimiyya", kamar yadda ya gabata ba lafazi ne na Shari'a ba, Malamai ba su yi amfani da shi ba, Maududiy ne ya fito da shi, shi kuma Sayyid Qutub ya kunsa Bidi'o'in Khawarijawa a ciki, na kafirta al'umma da kiranta da Jahiliyya. Wanda har wadanda suka zo daga baya suka tasirantu da shi, suka zo suka cikata aikin, suka dauki makami a kan al'ummar Musulmi suna kashe su, bisa hujjar "Hakimiyya".To idan muka duba rubutun da a cikinsa aka jingina ma Shaikh Muhammad bn Ibrahim "Hakimiyya" da farko mai rubutun bayan ya yi shimfida ya dauko maganganun Shaikh Muhammad bn Ibrahim wadanda ya yi su a kan haramcin sanya Dokokin tsarin mulki da suka saba ma Shari'ar Allah, inda ya tabbatar da cewa; hakan kafirci ne.Lallai ko shakka babu wannan gaskiya ne. Canza hukuncin Allah gaba dayansa, da musanya shi da wani hukuncin daban wanda ya saba masa kafirci ne. Saboda dalilai masu yawa, wadanda duka Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya ambace su a cikin littatafansa, daga ciki:a) Allah ya kore imani ga wanda bai yi hukunci da abin da Allah ya saukar ba, inda ya ce:{فَلَا وَرَبِّكَ لَا يُؤْمِنُونَ حَتَّى يُحَكِّمُوكَ فِيمَا شَجَرَ بَيْنَهُمْ ثُمَّ لَا يَجِدُوا فِي أَنْفُسِهِمْ حَرَجًا مِمَّا قَضَيْتَ وَيُسَلِّمُوا تَسْلِيمًا} [النساء: 65]b) Neman hukunci da abin da ba Shari'ar Allah ba ne neman hukunci ne a wajen Dagutu, Allah ya ce:{أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ يَزْعُمُونَ أَنَّهُمْ آمَنُوا بِمَا أُنْزِلَ إِلَيْكَ وَمَا أُنْزِلَ مِنْ قَبْلِكَ يُرِيدُونَ أَنْ يَتَحَاكَمُوا إِلَى الطَّاغُوتِ وَقَدْ أُمِرُوا أَنْ يَكْفُرُوا بِهِ وَيُرِيدُ الشَّيْطَانُ أَنْ يُضِلَّهُمْ ضَلَالًا بَعِيدًا (60) وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ تَعَالَوْا إِلَى مَا أَنْزَلَ اللَّهُ وَإِلَى الرَّسُولِ رَأَيْتَ الْمُنَافِقِينَ يَصُدُّونَ عَنْكَ صُدُودًا (61)} [النساء: 60، 61]c) Allah ya siffanta shi da hukuncin Jahiliyya, inda ya ce:{أَفَحُكْمَ الْجَاهِلِيَّةِ يَبْغُونَ وَمَنْ أَحْسَنُ مِنَ اللَّهِ حُكْمًا لِقَوْمٍ يُوقِنُونَ} [المائدة: 50]d) Allah ya siffanta hakan da kafirci da zalunci da fasikanci, inda ya ce:{وَمَنْ لَمْ يَحْكُمْ بِمَا أَنْزَلَ اللَّهُ فَأُولَئِكَ هُمُ الْكَافِرُونَ} [المائدة: 44]Ya ce:{وَمَنْ لَمْ يَحْكُمْ بِمَا أَنْزَلَ اللَّهُ فَأُولَئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ} [المائدة: 45]Ya ce:{وَمَنْ لَمْ يَحْكُمْ بِمَا أَنْزَلَ اللَّهُ فَأُولَئِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ} [المائدة: 47]Duka wadannan Ayoyi Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya ambace su, kuma ya tabbatar da abin da suka yi nuni gare shi.Masu danganta "Hakimiyya" Akidar Khawarija ga Shaikh Muhammad bn Ibrahim suna kawo maganganunsa da ya yi "Idlaqin" hukuncin aikin ne kawai. To amma sai dai inda matsalar take, ba su lura da cewa; shi Shaikh Muhammad bn Ibrahim "Idlaqin" hukunci yake yi, kamar yadda Allah ya yi, ba tare da Shaikh Ibn Ibrahim ya dora hukuncin a kan al'umma ba. Amma shi kuma Sayyid Qutub fa, kawai zuwa ya yi ya kafirta al'umma, ya ce yanzu duka babu Musulmai, babu al'umma Musulma, an koma Jahiliyya, saboda an bar "Hakimiyya".Matsala kuma ta biyu; Shi Shaikh Muhammad bn Ibrahim din ya yi Tafsilin nau'in kafircin da yake tabbatarwa a wannar mas'alar. Inda ya nuna cewa; kafircin nau'i biyu ne, imma kafirci na aiki (karamin kafirci) ko kuma kafirci na akida (babban kafirci), ga maganarsa a kan haka:(({فإن جاءوك فأحكم بينهم أو أعرض عنهم وإن تعرض عنهم فلن يضروك شيءئا إن حكمت فحكم بينهم بالقسط إن الله يحب المقسطين}. والقسط هو العدل ولا عدل حقا إلا حكم الله ورسوله والحكم بخلافه هو الجور والظلم والضلال والكفر والفسوق ولهذا قال تعالى: {ومن لم يحكم بما أنزل الله فأولئك هم الكافرون} {ومن لم يحكم بما أنزل الله فأولئك هم الظالمون} {ومن لم يحكم بما أنزل الله فأولئك هم الفاسقون}.فانظر كيف سجل الله تعالى على الحاكمين بغير ماأنزل الله بالكفر والظلم والفسوق ومن الممتنع أن يسمى الله سبحانه وتعالى بغير ما أنزل الله (كافرا) ولا يكون كافرا بل هو كافر مطلقا إما كفر عمل وإما كفر اعتقاد)).فتاوى ورسائل سماحة الشيخ محمد بن إبراهيم بن عبد اللطيف آل الشيخ (12/ 287 - 288)Ka ga a karshe sai ya ce maka: "wanda bai yi hukunci da abin da Allah ya saukar ba, ta yaya ba zai zama kafiri ba, a'a, kafiri ne kai tsaye, IMMA KAFIRCI NA AIKI KO NA AKIDA (إما كفر عمل وإما كفر اعتقاد)". KAFIRCI NA AIKI KUWA, SHI NE KARAMIN KAFIRCI WANDA BA YA FITAR DA MUTUM DAGA MUSLUNCI.Kuma Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya yi tafsili da bayani mai tsawo, inda ya nuna cewa; KAFIRCI NA AKIDA (mai fitarwa daga Muslunci) yana da halaye guda shida. Shi kuma KAFIRCI NA AIKI shi ne wanda mutum ya yi hukunci a wata kadhiyya, bayan ya yarda da hukuncin Allah a cikinta, amma sai ya bi son zuciyarsa, kuma yana jin cewa; shi mai sabo ne.Duba:فتاوى ورسائل سماحة الشيخ محمد بن إبراهيم بن عبد اللطيف آل الشيخ (12/ 288 - 291)To ka ga a fili yake cewa; Shaikh Muhammad bn Ibrahim bai fita daga Mazhabar Salaf a mas'alar ba, cewa; kafircin da ya zo a wannan babi nau'i biyu ne; imma ya zama: BABBAN KAFIRCI, ko kuma KARAMIN KAFIRCI. Kamar yadda aka ruwaito daga Salaf kamar haka:1) عن ابن عباس قوله:"ومن لم يحكم بما أنزل الله فأولئك هم الكافرون"، قال: من جحد ما أنزل الله فقد كفر. ومن أقر به ولم يحكم، فهو ظالم فاسق.تفسير الطبري = جامع البيان ت شاكر (10/ 357) تفسير ابن أبي حاتم - محققا (4/ 1142)2) عن بن طاوس عن أبيه قال: سئل ابن عباس في قوله: ومن لم يحكم بما أنزل الله فأولئك هم الكافرون قال: هي كبيرةتفسير ابن أبي حاتم - محققا (4/ 1143)3) عن عطاء قوله:"ومن لم يحكم بما أنزل الله فأولئك هم الكافرون"،"ومن لم يحكم بما أنزل الله فأولئك هم الظالمون"،"ومن لم يحكم بما أنزل الله فأولئك هم الفاسقون"، قال: كفر دون كفر، وفسق دون فسق، وظلم دون ظلم.تفسير الطبري = جامع البيان ت شاكر (10/ 355)4) عن طاوس:"ومن لم يحكم بما أنزل الله فأولئك هم الكافرون"، قال: ليس بكفر ينقل عن الملة.تفسير الطبري = جامع البيان ت شاكر (10/ 355)Shi ya sa Ibnul Qayyim ya ce:((والصحيح أن الحكم بغير ما أنزل الله يتناول الكفرين، الأصغر والأكبر بحسب حال الحاكم، فإنه إن اعتقد وجوب الحكم بما أنزل الله في هذه الواقعة، وعدل عنه عصيانا، مع اعترافه بأنه مستحق للعقوبة، فهذا كفر أصغر، وإن اعتقد أنه غير واجب، وأنه مخير فيه، مع تيقنه أنه حكم الله، فهذا كفر أكبر، وإن جهله وأخطأه فهذا مخطئ، له حكم المخطئين))مدارج السالكين بين منازل إياك نعبد وإياك نستعين (1/ 346)Sai Ibnul Qayyim ya kasa masu hukunci da sabanin abin da Allah ya saukar zuwa kashi 3:(1) Wanda yake ganin wajabcin bin Shari'ar Allah, amma sai ya saba mata, to wannan karamin kafirci ne.(2) Wanda kuma yake ganin halascin saba Shari'ar Allah to wannan babban kafirci ne.(3) Wanda kuma ya saba hukuncin Allah saboda kuskure ko jahilci to hukuncinsa na mai kuskure ne.To ka ga a fili yake Shaikh Ibnu Ibrahim ya gina maganarsa ce a mas'alar bisa Manhajin Salaf, na raba kafircin gida biyu. Sai dai a tafsilin ne za a iya samun sabani tsakanin Malamai, amma asalin kam guda daya ne.To abin tambaya a nan shi ne: Shin haka lamarin yake a wajen Khawarijawa da Sayyid Qutub?Yanzu ka dauki maganar Shaikh Muhammad Ibnu Ibrahim da maganar Ibnul Qayyim, sai ka auna su da wannar magana ta Sayyid Qutub ka gani:((والإسلام منهج للحياة كلها. من اتبعه كله فهو مؤمن وفي دين الله. ومن اتبع غيره ولو في حكم واحد فقد رفض الإيمان واعتدى على ألوهية الله، وخرج من دين الله. مهما أعلن أنه يحترم العقيدة وأنه مسلم. فاتباعه شريعة غير شريعة الله، يكذب زعمه ويدمغه بالخروج من دين الله.))في ظلال القرآن (2/ 972)A nan shi Sayyid Qutub ko hukunci daya mutum ya bari, to ya bar imani, ya fita daga Addinin Allah. Ko da kuwa yana girmama Akida, yana cewa: shi Musulmi ne.To shin Manhajin Sayyid Qutub iri daya ne da na su Shaikh Ibnu Ibrahim?Shin Sayyid Qutub yana kasa kafircin zuwa gida biyu; BABBAN KAFIRCI mai fitarwa a Muslunci, da kuma KARAMIN KAFIRCI, wanda ba ya fitar da mutum a Muslunci?Saboda haka kasa kafirci gida biyu a mas'alar, shi ne abin da ya raba tsakanin Manhajin Ahlus Sunna, da kuma Manhajin Khawarijawa. Shi ya sa Sayyid Qutub ya yi ta amfani da lafazin "Hakimiyya" ya yi ta kafirta al'umma a bisa haka, kamar yadda Khawarijan farko "Muhakkima" suka yi.To sai mu tambayi masu jingana "Hakimiyya" ga Shaikh Muhammad Ibnu Ibrahim mu ce musu:A ina Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya yi amfani da lafazin "Hakimiyya" da har za a danganta masa shi?!Yaushe Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya kafirta al'umma, ya ce: sun koma Jahiliyya, saboda ba sa hukunci da abin da Allah ya saukar, kamar yadda Sayyid Qutub ya yi, da har za a danganta masa "Hakimiyya"?!Saboda haka babu mai ilimi ko mai adalcin da zai yi wannan jafa'in ga Shaikh Muhammad Ibnu Ibrahim!Don haka zuwa yanzu ba mu ga inda Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya tabbatar da "Hakimiyya" ba.Kuma ba mu ga ya kafirta al'umma ya ce: ta koma Jahiliyya ba.Ba mu ga ya kafirta wata "mujtama'a" ta wata kasa ya ce: ta koma Jahiliyya ba.Abin da muka gani a wajensa shi ne bayanin mas'alar "Hukunci da abin da ba Allah ne ya saukar ba" bisa Alkur'ani da fahimtar Salaf da Manhajin Ahlus Sunna. Kuma ita wannar mas'ala duka Malaman Muslunci sun yi magana a kanta, tun daga kan Sahabbai har zuwa yau. Kuma Shaikh Muhammad bn Ibrahim bai fita daga Manhajinsu ba.Khawarijawa ne suka saba a wannar mas'ala, suka kafirta Sayyidina Aliyu (ra), suka nuna: ya saba "Hakimiyya", ya yi "Tahkeem". A kan haka suka yi masa tawaye, suka kafirta shi, suka kafirta sauran Musulmai, daga karshe suka kashe shi. Kuma wannan tunanin shi Sayyid Qutub ya dauko ya yada shi cikin al'umma ta hanyar littatafansa, har wasu matasa jahilai, masu kishin Addini suka tasirantu da shi, suka yi ta kafa kungiyoyi irin Boko Haram, suna ta'addanci a kan al'ummar Musulmi, saboda ta saba "Hakimiyya".Saboda haka Shaikh Muhammad Ibnu Ibrahim ba shi da alaka da Akidar Khawarijawa ta "Hakimiyya".✍️ *Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)* *29 October, 2021* *DA MUNGUWAR RAWA GARA KIN TASHI… (3)* HAKIMIYYA TSAKANIN MUFTIY SHAIKH MUH'D BN IBRAHIM ALU-SHAIKH, DA SAYYID QUTUB (B ): RADDI A FASS... Cigaba da karantawa»
*DA MUNGUWAR RAWA GARA KIN TASHI… (2)*HAKIMIYYA TSAKANIN MUFTIY SHAIKH MUH'D BN IBRAHIM ALU-SHAIKH, DA SAYYID QUTUB (A)"Hakimiyya" wani suna ne da ya bayyana daga Abul A'ala al-Maududiy, Sayyid Qutub kuma ya yada shi, wanda yake nufin wata ma'ana; wacce ta ginu bisa Akidar Khawarijawa, ta kafirta al'umma, wacce Kungiyoyin Ta'addanci irin su Boko Haram suka dauka daga gare su, suna yakar al'ummar Musulmi.To kasancewar ya bayyana wa mutane cewa; wannar Akida ta "Hakimiyya" tushenta Akidar Khawarijawa ne, shi ya sa wasu suke ta kokarin lullube ta, da nema mata goyon baya daga maganganun Malaman al'umma, Ahlus Sunna, wadanda aka sansu da yakar Akidun Khawarijawa.Bayyanan wannan sabon salo, na cakuda tsakanin karya da gaskiya, shi yake lazimta raddi don bayani wa mutane, da barrantar da Malaman da aka jingina musu wannar Bidi'a da barna ta Khawarijawa. Saboda haka wannan rubutu nawa raddi ne ga masu danganta"Hakimiyya" ga Shaikh Muh'd bn Ibrahim Alu-Shaikh, Muftin Saudiyya kafin Shaikh Ibnu Baaz.Don haka raddin zai zo ne kashi biyu; a dunkule da kuma a fassale gaba – gaba da iznin Allah.RADDIN A DUNKULE: ya kunshi bayanin wasu abubuwa kamar haka:- Asalin lafazin "Hakimiyya" da matsayin amfani da shi.- Mecece Akidar Sayyid Qutub?- Mecece Akidar Shaikh Muh'd bn Ibrahim?- "Hakimiyya" a wajen Sayyid Qutub.Mutum ba zai fahimci gaskiyar danganta "Hakimiyya" Akidar Khawarijanci ma Shaikh Muh'd bn Ibrahim ba har sai ya san Asalin "Hakimiyya", da kuma Akidar Shaikh Muh'd bn Ibrahim, da Akidar Sayyid Qutub. Idan mutum ya san haka a nan zai fahimci kowanne a cikinsu a bisa wace Akida ya gina maganarsa. A cikinsu wanda muka same shi bisa Akidar Ahlus Sunna to mun san maganganunsa zai gina su kan Manhajin Sunna. Wanda kuma muka samu Akidarsa ta Khawarijawa ce, to maganganunsa dole zai zama bisa Akida da Manhajin Khwarijawa ne.1- BAYANIN LAFAZIN "HAKIMIYYA":Lafazin "Hakimiyya" (حاكمية) Masdari ne "Sina'iy" (صناعي), wanda aka kirkire shi daga lafazin "Hukm" (حكم), wato hukunci. Wannan lafazi na "Hakimiyya" ba za ka same shi a cikin littatafan Luga da ake dogaro da su ba, balle littatafan Shari'a.Haka wannan lafazi bai zo cikin Alkur'ani ko Sunna ba. Kuma babu wannan lafazi a cikin littatafan Shaikh Muh'd bn Ibrahim, saboda haka ta yaya za a yi a jingina ma Shaikh Muh'd bn Ibrahim Hakimiyya?!Wannan lafazi na "Hakimiyya" lafazi ne "Mujmali" dunkulalle, wanda ya kunshi karya da gaskiya. Wato irin lafuzan da mabarnata suke fakewa da su suna shigar da bidi'o'insu cikin al'umma, kamar yadda da ma Manhaji ne na 'Yan Bidi'a, kunshe bidi'o'insu a cikin dunkulallun lafuza:((الألفاظ المجملة عرضة للمحق والمبطل)).شرح الطحاوية ت الأرناؤوط (1/ 266)((Su lafuza dunkulallu abin amfani ne ga mai gaskiya da mabarnaci)).Don haka a ka'ida ta Ahlus Sunna ba sa amfani da lafuza "Mujmalai" dunkulallu wajen bayanin gaskiya, kawai suna takaita ne a kan lafuza na Shari'a, ko lafuzan da gaskiya kawai suka kunsa. Ibnu Abil Izz ya ce:((التعبير عن الحق بالألفاظ الشرعية النبوية الإلهية هو سبيل أهل السنة والجماعة)).شرح الطحاوية ت الأرناؤوط (1/ 70)((Bayanin gaskiya da lafuzan Shari'ar Annabi ta Allah shi ne hanyar Ahlus Sunna wal Jama'a)).Don haka hanya ce ta 'yan bidi'a su dauko wani lafazi da bai zo a Shari'a ba, kuma wanda ya kunshi karya da gaskiya, sai su dora masa bidi'arsu, sai kuma su cuso cikin Addini, suna kafirta mutane da shi, kamar yadda muka gani a wajen Ustaz Sayyid Qutub a wannan lafazi na "Hakimiyya".Manhajin Ahlus Sunna a irin wadannan lafuza sai a nemi bayani daga wanda ya yi amfani da su. Idan yana nufin ma'ana mai kyau wacce ta dace da Alkur'ani da Sunna sai a karbi ma'anar, amma idan kuma mummunar ma'ana yake nufi sai a yi watsi da ita.Saboda haka, idan suna nufin Allah shi ne mai hukunci, kuma hukunci nasa ne, da wajabcin yin hukunci da Abin da Allah ya saukar, kuma hakan yana karkashin kadaita Allah da bauta, to wannan ma'ana ce mai kyau, wacce ta zo a Shari'a.Amma idan suna nufin "Hakimiyya" bisa ma'anarta a wajen Sayyid Qutub, to sai mu yi watsi da ita, don ma'ana ce ta Khawarijawan farko, "Muhakkima", wadanda suka kafirta Sayyidina Aliyu (ra), suka yake shi, kuma daga karshe suka kashe shi.Saboda haka akwai babban kuskure a cikin jingina ma Shaikh Shaikh Muh'd bn Ibrahim da Jami'ar Madina wannan kirkirarren lafazi, wanda yake dauke da mummunan ma'ana a wajen wadanda suka kirkire shi.2- AKIDAR SAYYID QUTUB:Akwai bukatar mu san Akidar Sayyid Qutub don sanin tushen da a kansa ya gina ma'anar "Hakimiyya". Saboda abu ne sananne cewa: Musulmai sun yi Ijma'i a kan wajabcin yin hukunci da abin da Allah ya saukar. Amma sai Khawarijawa suka saba, suka kara bidi'o'i masu hatsari a kan haka, wanda ya kai su ga fita daga al'umma da halasta jinanenta, da daukar makami a kanta. Wannan ya sa har aka kira Khawarijawan farko da sunan: "Muhakkimah", saboda sabawarsu ga Musulmai a kan wannar mas'ala.A wannar mas'ala dole ne mu san Akidar Sayyid Qutub, don mu san shi Akidarsa irin ta Khawarijawa ce ko kuma irin ta Ahlus Sunna ce?To idan muna so mu san Akidar Sayyid Qutub, shin irin ta Khawarijawa ce ko a'a, sai mun san Akidarsa a "MAS'ALAR HAKIKANIN IMANI DA MUSLUNCI", da abin da ke da alaka da su na Hakikanin Kafirci. Don haka idan muka duba za mu ga cewa: Ma'anar Imani da Muslunci a wajen Sayyid Qutub irin ma'anarsu ce a wajen Khawarijawa, Akidarsu ita ce Akidarsa. Abin da zai tabbatar mana da haka shi ne; Sayyid ya tabbatar da cewa; Imani da Muslunci abu ne guda daya a dunkule, wanda ba ya rarrabuwa, ta yadda idan an rasa wani sashe nasa to an rasa shi gaba daya. Don haka a wajen Sayyid; idan mutum ya rasa wani bangare na Imani ko Muslunci (wato ya bar wani aikin imani), to ya fita daga Muslunci gaba daya, ya zama kafiri. Wannan kuwa ita ce: Akidar Khawarijawa, kamar yadda Ibnu Taimiyya ya ce:((أصل نزاع هذه الفرق في الإيمان من الخوارج والمرجئة والمعتزلة والجهمية وغيرهم أنهم جعلوا الإيمان شيئا واحدا إذا زال بعضه زال جميعه وإذا ثبت بعضه ثبت جميعه فلم يقولوا بذهاب بعضه وبقاء بعضه كما قال النبي صلى الله عليه وسلم {يخرج من النار من كان في قلبه مثقال حبة من الإيمان}.ثم قالت "الخوارج والمعتزلة": الطاعات كلها من الإيمان فإذا ذهب بعضها ذهب بعض الإيمان فذهب سائره فحكموا بأن صاحب الكبيرة ليس معه شيء من الإيمان)).مجموع الفتاوى (7/ 510)Sai Ibnu Taimiyya ya bayyana cewa; Khawarijawa ma – kamar sauran 'yan bidi'a – duka sun tafi ne a kan cewa; Imani abu daya ne ba ya rarrabuwa, ta yadda idan sashensa ya gushe to gaba daya imanin zai gushe mutum ya fita daga Muslunci. Sai ya ambaci ra'ayin Khawarijawan ya ce:((Khawarijawa da Mu'utazila suka ce: aiyukan da'a ma Allah gaba dayansu suna cikin Imani, idan sashen aiyukan da'an ya tafi ya gushe, sashen imanin ya tafi, to sauran imanin ma zai tafi ya gushe daga daya, wannan ya sa suka yi hukunci ma wanda ya aikata babban sabo to zai zama ba shi da sauran imani (ya kafirta))).Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya ce:((المعتزلة والخوارج قالوا: إن الإيمان قول وعمل لكن لا يتبعض ولا يتجزأ، قالوا: إن ترك المعصية وفعل الطاعة إيمان، فإذا فعل الموحد المعصية، أو ترك الطاعة زال عنه الإيمان بالكلية. ثم الخوارج تكفره، والمعتزلة تجعل له منزلة بين منزلتين. وافقوا أهل السنة في أصل الإيمان أنه قول وعمل، لكن خالفوهم فقالوا: لا يتبعض ولا يتجزأ)).شرح العقيدة الواسطية (ص: 128)Sayyid Qutub kuwa wannar Akida ta Khawarijawa ita ce Akidarsa, ya tabbatar da ita a wurare masu yawa a cikin "Fi Zilalil Qur'an", daga ciki ya ce:((وهو اطراد يوجه النظر إلى حقيقة هذا الدين.. إنه وحدة لا تتجزأ))في ظلال القرآن (1/ 164)Ka ga a nan sai Sayyid Qutub ya nuna cewa; hakikanin Addini abu guda ne, ba ya rarrabuwa.Ya ce:((يصبح المنهج الإلهي وحدة واحدة. لا تتجزأ ولا تتفرق. ويصبح ترك جانب منه وإعمال جانب، إيماناً ببعض الكتاب وكفراً ببعض.. فهو الكفر في النهاية)).في ظلال القرآن (1/ 177)Ka ga a nan ma sai Sayyid Qutub ya nuna cewa; Manhajin Allah, wato Addini kenan, abu ne guda daya, ba ya rarrabuwa. Idan mutum ya bar wani bangare nasa to karshensa kafirci ne.Ya ce:((إن الإيمان وحدة لا تتجزأ.. الإيمان بالله إيمان بوحدانيته- سبحانه- ووحدانيته تقتضي وحدة الدين الذي ارتضاه للناس لتقوم حياتهم كلها- كوحدة- على أساسه. ويقتضي وحدة الرسل الذين جاءوا بهذا الدين من عنده- لا من عند أنفسهم ولا في معزل عن إرادته ووحيه- ووحدة الموقف تجاههم جميعاً.. ولا سبيل إلى تفكيك هذه الوحدة. إلا بالكفر المطلق وإن حسب أهله أنهم يؤمنون ببعض ويكفرون ببعض! وكان جزاؤهم عند الله أن أعد لهم العذاب المهين.. أجمعين..))في ظلال القرآن (2/ 798)Ka ga a nan kuma sai Sayyid Qutub ya nuna cewa; hakikanin Imani abu ne guda daya, ba ya rarrabuwa.Ya ce:((والإسلام منهج للحياة كلها. من اتبعه كله فهو مؤمن وفي دين الله. ومن اتبع غيره ولو في حكم واحد فقد رفض الإيمان واعتدى على ألوهية الله، وخرج من دين الله. مهما أعلن أنه يحترم العقيدة وأنه مسلم. فاتباعه شريعة غير شريعة الله، يكذب زعمه ويدمغه بالخروج من دين الله.))في ظلال القرآن (2/ 972)A nan ma sai Sayyid Qutub ya nuna cewa; Muslunci tsarin rayuwa ne gaba dayanta, sai wanda ya bi shi gaba daya ne zai zama Mumini. Wanda kuma ya bi wani abu ba Muslunci ba a rayuwarsa, ko da a hukunci ne guda daya to ya yi watsi da imanin, kuma ya fita daga Addinin Muslunci, ko da ya ce: shi Musulmi ne, kuma yana girmama Akidar Muslunci.Wannan shi yake tabbatar mana cewa; Akidar Sayyid Qutub a Babin Hakikanin Muslunci da Imani iri daya ne da na Khawarijawa, wannan ya sa kafirta Musulmai da yake yi, iri daya ne da na Khawarijawa.Saboda haka maganar da zai yi a kan mas'alar "Hukunci da abin da Allah ya saukar", iri daya ne da na Khawarijawa, irin ra'ayin Khawarijawan Farko, wadanda aka kira su da sunan "Muhakkima", wadanda suka kafirta Sayyidina Aliyu (ra), kuma suka kashe shi.Saboda haka "Hakimiyyar" da Sayyid Qutub ya yada, wacce ya dauko daga Maududiy, matsayinta shi ne "كلمة حق أريد بها الباطل", ma'ana; kura ce da fatar Akuya, kamar yadda za mu ga hakan a nan gaba.3- AKIDAR SHAIKH MUHAMMAD BN IBRAHIM:Shi kuma Shaikh Muhammad bn Ibrahim wanda wasu suke danganta masa "Hakimiyya" Akidar Khawarijawa, - duk da cewa; asali bai taba ambaton kalmar ba – mecece Akidarsa a Babin Hakikanin Muslunci da Imani?Shin Akidarsa irin ta Khawarijawa ce da har za a danganta masa "Hakimiyyarsu", ko irin ta Ahlus Sunna ce?To ga nan inda Shaikh Ibnu Ibrahim ya tabbatar da Akidarsa a kan haka kamar haka:((إن الإسلام والإيمان والإحسان دوائر، أوسعها دائرة الإسلام، ثم يليها في السعة الإيمان، ثم أضيقها الإحسان، وهكذا، مثل الدوائر التي كل واحدة محيطة بالأخرى. فمن المعلوم أن من كان في الدائرة الوسطى – وهي دائرة الإحسان – فهو داخل في الإسلام والإيمان، وإذا خرج عن الوسطى فهو داخل في الثانية وهي الإيمان، وإذا خرج عنهما فهو داخل في الثالثة، وهي الإسلام، وإذا خرج عن هذه الدوائر الثلاث فهو خارج إلى غضب الله وعقابه، وداخل في دوائر الشيطان والعياذ بالله. فنعرف بالتمثيل بهذه الدوائر صحة قول من قال: كل محسن مؤمن مسلم وليس كل مسلم مؤمنا محسنا، فلا يلزم من دخوله في الإسلام أن يكون داخلا في الإحسان والإيمان. وليس المراد أن من لم يكن في الإحسان والإيمان أنه يكون كافرا، فإنه مسلم، لكن لا يكون مؤمنا الإيمان الكامل الذي يستحق أن يثنى عليه به)).شرح الأصول الثلاثة (ص: 213 - 214)To ka ga sai Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya bayyana mana cewa; Addini ba abu daya ne a dunkule ba - kamar yadda Sayyid Qutub ya fada -, ta yadda idan an rasa sashe an rasa shi gaba daya. A'a, Addini matakai ne guda uku, kuma kowane mataki yana da asali da kuma kamala. Akwai matakin Muslunci, Imani da Ihsani. Sai ya misalta mana su da misalin da wani cikin Salaf ya yi, inda ya nuna Addini da'irori (circle) ne guda uku, sun kewaye juna. Da'irar Muslunci ta fi fadi, da'irar Ihsani kuma ita ce mafi karanta.Ga nan da'irar Ihsani 'yar karama, sai da'irar Imani ya kewaye ta. Ita kuma da'irar Imani, sai da'irar Muslunci ya kewaye ta. Don haka da'irar Ihsani tana cikin da'irar Imani, da'irar Imani kuma tana cikin da'irar Muslunci.Idan mutum ya fita daga Ihsani, ya aikata abubuwa da za su fitar da shi daga Ihsanin, ba zai fita daga Muslunci ba, a'a, zai koma cikin da'irar Imani ne. Idan kuma ya fita daga da'irar Imani (ya aikata abubuwan da suka fitar da shi daga Imani), ba zai fita daga Muslunci ba, a'a, zai koma da'irar Muslunci ne. Har sai idan ya aikata abin da zai warware masa Muslunci shi ne zai fitar da shi daga Muslunci gaba daya. Shi ya sa a karshen maganarsa Ibnu Ibrahim din ya ce:((وليس المراد أن من لم يكن في الإحسان والإيمان أنه يكون كافرا، فإنه مسلم، لكن لا يكون مؤمنا الإيمان الكامل الذي يستحق أن يثنى عليه به)).((Ba a nufin cewa; duk wanda ya fita daga da'irar Ihsani da ta Imani ZAI KASANCE KAFIRI, A'A, LALLAI SHI MUSULMI NE. Sai dai ba zai zama Mumini mai Imani cikakke ba, wanda za a yabe shi a kansa (Ma'ana; yana da imanin, amma sai dai ba cikakke ba ne)".To yanzu ka auna wannar magana ta Shaikh Muhammad bn Ibrahim da maganar Sayyid Qutub, inda ya ce:((يصبح المنهج الإلهي وحدة واحدة. لا تتجزأ ولا تتفرق. ويصبح ترك جانب منه وإعمال جانب، إيماناً ببعض الكتاب وكفراً ببعض.. فهو الكفر في النهاية)).Ma'ana; Barin wani janibi na Addini kafirci ne.Za ka ga banbancin Akida a tsakaninsu. Shaikh Muhammad bn Ibrahim Akidarsa ta Ahlus Sunna ce, amma Sayyid Qutub Akidarsa ta Khawarijawa ce.Don haka idan ka karanta wannan za ka san cewa; Akidar Shaikh Muhammad bn Ibrahim Akidar Ahlus Sunna ce ba ta Khawarijawa kamar Akidar Sayyid Qutub ba. Sanin wannan da banbance tsakanin mutanen biyu, shi zai sa mu fahimci banbancin da ke tsakanin maganar Shaikh Muhammad bn Ibrahim a mas'alar "Hukunci da abin da Allah ya saukar", da maganar Sayyid Qutub a "Hakimiyyar" da suka kirkira, wacce ta ginu bisa Akidar Khawarijawa.4- MA'ANAR "HAKIMIYYA" A WAJEN SAYYID QUTUB:Asali Kalmar "Hakimiyya" a wajen Maududiy ta fara bayyana, sai Sayyid Qutub ya dauke ta ya yi ta yada ta a cikin littatafansa, yana kirkira mata hukunce – hukunce iri daban – daban, masu girma masu hatsari, bisa Akidarsa da Manhajinsa na Khawarijawa.Daga cikin irin wadannan hukunce – hukuncen da ya kirkira, akwai fadinsa cewa:1. Ita wannar Hakimiyya ita ce: ma'anar Kalmar Shahada, ta yadda duk wanda ya yarda da wani tsari ko wata Gomnati a wannan zamani, balle har ya yi ta'amuli da ita, to lallai ya kafirce ma Kalmar Shahada, ya zama kafiri. Ga wasu maganganunsa a kan haka. Yana magana game da Larabawa sai ya ce:((قد كانوا يعرفون من لغتهم معنى: «إله» ومعنى: «لا إله إلا الله» .. كانوا يعرفون أن الألوهية تعني الحاكمية العليا.. وكانوا يعرفون أن توحيد الألوهية وإفراد الله - سبحانه - بها، معناه نزع السلطان الذي يزاوله الكهان ومشيخة القبائل والأمراء والحكام، ورده كله إلى الله))في ظلال القرآن (2/ 1005)، معالم في الطريق (ص: 26)-Wai- Larabawa sun san cewa: Ma'anar "Uluhiyya" ita ce: "Hakimiyya".Kuma ya ce:((«لا إله إلا الله» كما كان يدركها العربي العارف بمدلولات لغته: لا حاكمية إلا لله، ولا شريعة إلا من الله، ولا سلطان لأحد على أحد، لأن السلطان كله لله))في ظلال القرآن (2/ 1006)، معالم في الطريق (ص: 28)2. A yau mutane sun koma Jahiliyya, saboda sun bar "Hakimiyya":((أما اليوم وقد عادت الأرض إلى الجاهلية وارتفع حكم الله- سبحانه- عن حياة الناس في الأرض، وعادت الحاكمية إلى الطاغوت في الأرض كلها، ودخل الناس في عبادة العباد بعد إذ أخرجهم الإسلام منها.. الآن تبدأ جولة جديدة أخرى للإسلام- كالجولة الأولى- تأخذ- في التنظيم- كل أحكامها المرحلية، حتى تنتهي إلى إقامة دار إسلام وهجرة ثم تمتد ظلال الإسلام مرة أخرى- بإذن الله- فلا تعود هجرة ولكن جهاد وعمل كما حدث في الجولة الأولى..))في ظلال القرآن (3/ 1560)Ya ce:((إن المجتمع الجاهلي هو كل مجتمع غير المجتمع المسلم! وإذا أردنا التحديد الموضوعي قلنا: إنه هو كل مجتمع لا يخلص عبوديته لله وحده. . متمثلة هذه العبودية في التصور الاعتقادي، وفي الشعائر التعبدية، وفي الشرائع القانونية. .وبهذا التعريف الموضوعي تدخل في إطار " المجتمع الجاهلي " جميع المجتمعات القائمة اليوم في الأرض فعلا!...تملك سلطة التشريع دون الرجوع إلى شريعة الله. . أي أن لها الحاكمية العليا باسم "الشعب" أو باسم "الحزب" أو باسم كائن من كان. . ذلك ان الحاكمية العليا لا تكون إلا لله سبحانه، ولا تزاول إلا بالطريقة التي بلغها عنه رسله)).معالم في الطريق (ص: 86 - 87)3. Duka Musulmai sun yi Ridda sun fita daga Muslunci, saboda sun bar "Hakimiyya":((لقد استدار الزمان كهيئته يوم جاء هذا الدين إلى البشرية بلا إله إلا الله. فقد ارتدت البشرية إلى عبادة العباد، وإلى جور الأديان ونكصت عن لا إله إلا الله، وإن ظل فريق منها يردد على المآذن: «لا إله إلا الله» دون أن يدرك مدلولها، ودون أن يعني هذا المدلول وهو يرددها، ودون أن يرفض شرعية «الحاكمية» التي يدعيها العباد لأنفسهم- وهي مرادف الألوهية- سواء ادعوها كأفراد، أو كتشكيلات تشريعية، أو كشعوب. فالأفراد، كالتشكيلات، كالشعوب، ليست آلهة، فليس لها إذن حق الحاكمية.. إلا أن البشرية عادت إلى الجاهلية، وارتدت عن لا إله إلا الله. فأعطت لهؤلاء العباد خصائص الألوهية. ولم تعد توحد الله، وتخلص له الولاء))في ظلال القرآن (2/ 1057)Wannan shi ne "Mafhumin Hakimiyyar" da su Sayyid Qutub suka kirkira, kuma ya kafirta al'umma gaba daya da ita. Har 'yan ta'adda suka tasirantu da shi, suke ta kashe al'ummar Musulmi.A kan haka ya bayyana cewa: hakikanin "Hakimiyya" a wajen Sayyid Qutub shi ne Akidar Khawarijawan "Muhakkima", masu kashe mutane, a bisa "shi'ar" na "لا حكم إلا لله". (Babu hukuma sai ta Allah). Kalmar da Sayyidina Aliyu (ra) ya kira ta da: "كلمة حق أريد بها الباطل".To ka ga da wannan za mu fahimci banbancin Sayyid Qutub da Shaikh Muh'd bn Ibrahim Alu-Shaikh, cewa; Sayyid Qutub Akidarsa ta Khawarijawa ce. Shi kuma Shaikh Muh'd bn Ibrahim Alu-Shaikh Akidarsa ta Ahlus Sunna ce.Saboda haka duk maganar da Sayyid Qutub zai yi a kan mas'alar "Hukunci da abin da Allah ya saukar" to zai yi ne bisa Akidarsa ta Khawarijanci.Kamar yadda shi kuma Shaikh Muh'd bn Ibrahim Alu-Shaikh zai yi ne bisa Akidarsa ta Ahlus Sunna.Sai ku biyo mu a kashi na 3, inda za mu yi raddi a fassale da iznin Allah.✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani (H) 28 October, 2021 *DA MUNGUWAR RAWA GARA KIN TASHI… (2)* HAKIMIYYA TSAKANIN MUFTIY SHAIKH MUH'D BN IBRAHIM ALU-SHAIKH, DA SAYYID QUTUB (A) "Hakimiyy... Cigaba da karantawa»