HABAKAR ILIMIN HADISI A KASAR HAUSA
A yau ne al'ummar Hausawa suka kara samun cigaba a bangaren ilimin Addinin Muslunci, inda aka kaddamar da tarjamar babban littafi mai albarka a Addinin Muslunci, wato littafin Muwadd'u ta Imamu Malik, wanda Shaikh Dr. Ahmad Ibrahim Bamba ya tarjama zuwa harshen Hausa. Allah ya saka masa da alheri, tare da wanda ya dauki nauyin fitar da wannan littafi mai albarka insha Allahu.
Alal hakika Hadisi shi ne Sunna, wato hanyar Annabi (saw). Mabiya Hadisi kuma su ne Ahlus Sunna. Shi ya sa tun zamanin farko, da aka samu masu inkarin Hadisi, sai al'ummar Musulmi ta rabu gida biyu; aka samu masu Bin Hadisi su ne Ahlus Sunna, da kuma masu inkarin Hadisi, su kuma su ne 'Yan Bidi'a.
Wani abu mai muhimmanci da ya kamata a sani, su fa wadannan masu inkarin Hadisi, wadanda aka rada musu suna 'Yan Bidi'a, ba Hadisan Tsarki da Sallah da Azumi da Zakka da Hajji da kasuwanci suke inkari ba, a'a, sun yarda da wadannan Hadisan. Hadisan da suke inkari su ne Hadisan da suka saba ma ra'ayoyinsu na Akida. Don haka ake kiransu 'Yan Bidi'a, Mabiya son zuciya. Saboda da ma son zuciya a Akida ya raba al'umma kashi - kashi, kungiya - kungiya. Sai Khawarijawa suka yi inkarin dukkan Hadisan da suka saba ra'ayoyinsu, kamar Hadisan da suke nuna Imani yana rarrabuwa, da kuma Hadisan tabbatar da Imani ga Musulmi mai sabo, da Hadisan Da'a wa Shugabanni. Haka Rafidha 'Yan Shi'a, suka yi inkarin Hadisan da suka saba Addininsu. Haka Mabiya Ilmul Kalam, suka yi inkarin Hadisan Siffofin Allah da sauransu. Sufaye da Rafidha 'Yan Shi'a suka yi inkarin Hadisan makomar Iyayen Annabi (saw) saboda sun rushe musu Akidarsu a gadon falala. Hadisan sun hana su gadon Shariftaka da Sayyidantaka. Saboda abin da Hadisan suke nunawa shi ne; kusacinka da dangantakarka ta jini da Annabi (saw) ba za ta amfanar da kai da komai ba, matukar ba ka yi Imani da Allah da ka bi Sunnar Manzonsa (saw) da hanyar Sahabbansa ba.
To hanyar da wadannan 'Yan Bidi'a suke bi wajen inkarin Hadisan hanyoyi ne guda biyu: Masu tsaurin ido su ne suke karyata Hadisan kai tsaye, wato Rafidha 'Yan Shi'a da Mu'utazila da makamantansu, saboda su a wajensu Sahabban da suka ruwaito Hadisan ma ba mutanen kirki ba ne, balle kuma sauran maruwaita na kasa da Sahabban!
Hanya ta biyu ita ce ta galibi 'Yan Bid'ar da suke da alaka da wasu ilmomi na Shari'a, wato cewa: Hadisan "Ahaad" ne. Wato ba Hadisai ne Mutawatirai ba.
Alhali akwai mamaki, wanda yake raya cewa; Annabi (saw) mai gaskiya ne, amma kuma ka same shi ba zai gaskata maganar mai gaskiyan ba!
Idan har ba za ka gaskata Annabi (saw) a abin da ya tabbata ya fada ba, to miye amfanin fadinka cewa shi mai gaskiya ne?!
Idan har ka yarda Annabi (saw) mai gaskiya ne, to me zai hana ka gaskata shi a abin da ya ba ka labari?!
Akwai mamaki matuka!
Idan har ya tabbata Annabi (saw) ya fadi Hadisi, to kai tsaye gaskiya ne, kuma daga Allah ne!
Su kuma Hadisan Sahihul Bukhari da Muslim Malaman Hadisi sun yi ittifaki a kan karbansu. Don haka idan ka hada wannan ittifaki da ingancin Hadisan sai ya kara ma Hadisan karfi, har su isa ga fa'idantar da yakini. Don haka za a yi aiki da su a mas'alolin Akida da Fiqhu, saboda dukkansu suna nuni ga yakini. Imam al-Sam'aniy ya ce:
((إن الخبر إذا صح عن رسول الله - صلى الله عليه وسلم - ورواه الثقات والأئمة، وأسندوه خلفهم عن سلفهم إلى رسول الله - صلى الله عليه وسلم - وتلقته الأمة بالقبول، فإنه يوجب العلم فيما سبيله العلم، وهذا قول عامة أهل الحديث والمتقنين من القائمين على السنة.
وإنما هذا القول الذي يذكر أن خبر الواحد لا يفيد العلم بحال، ولا بد من نقله بطريق التواتر لوقوع العلم به، شيء اختراعته القدرية والمعتزلة، وكان قصدهم منه رد الأخبار)).
الحجة في بيان المحجة (2/ 228)، صون المنطق والكلام عن فني المنطق والكلام (ص: 212)
((Lallai idan Hadisi ya inganta daga Manzon Allah (saw), amintattun maruwaita da A'imma suka ruwaito shi da isnadi, na baya suka ruwaito daga magabatansu, har zuwa Manzon Allah (saw), kuma al'umma ta karbi Hadisin (ba ta yi inkarinsa ba), to lallai Hadisin yana nuni ga yakini, a mas'alolin da suke bukatar samun yakini (Manyan mas'alolin Addini). Wannan shi ne ra'ayin gamayyar kwararrun Malaman Hadisi, tsayayyu a kan Sunna.
Amma ra'ayin da ake fadin cewa; Hadisi "Ahaad" ba ya nuni ga yakini ta kowane hali, -wai- dole sai ya zama Hadisi Mutawatiri kafin ya yi nuni ga yakini, kawai wani ra'ayi ne da 'Yan Qadariyya da Mu'utazila suka kirkira, kuma manufarsu ita ce: watsi da Hadisan Annabi (saw))).
A nan sai Sam'aniy ya nuna cewa; duk Hadisin da al'umma suka karbe shi - kamar Hadisan Sahihul Bukhari da Muslim - suka yi Ittifaki a kansa, to yana nuni ga yakini, cewa; tabbatas Hadisin gaskiya ne, Annabi (saw) ya fade shi.
Kuma kar wani ya ce: ai ba duka al'umma ce ta yi Ittifaki da Ijma'i a kan Hadisin ba!
A'a Malam, ai Ittifakin da ake la'akari da shi shi ne Ittifakin Malaman Fannin da ake magana a kansa. Kamar yadda Ittikin Malaman Fiqhu shi ne abin lura a Babin Fiqhu, to haka Ittifakin Malaman Hadisi shi ne abin lura a fannin Hadisi.
Saboda haka duk Hadisin da ya tabbata Annabi (saw) ya fade shi, to idan da gaske ka yarda Annabi Mai gaskiya ne, to dole ne ka gaskata Hadisin. Idan kuma ka ki gaskatawa, to akwai alamar rauni a yardarka cewa: Annabi (saw) mai gaskiya ne.