Amsa Addu'a
Wato idan ka ga halin mutanen da suke jayayya a kan cewa halin matsin rayuwa da ake ciki a dalilin zaluncin shugabanni jarabawa ce daga Allah don mu koma gare shi, sai ka fahimci da alama mutane masu yawa ba su shirya neman mafita daga halin da ake ciki ba.
Alhali duk wanda ya san Allah, ya san sunayensa da siffofinsa, wato ya san ma'anoninsu, zai san cewa idan muka tashi da gaske muka kira Allah, muka roke shi to zai amsa mana.
Imam Ibnul Qayyim ya ce:
وهو المجيب يقول من يدعو أجب *** -ه أنا المجيب لكل من ناداني
وهو المجيب لدعوة المضطر إذ *** يدعوه في سر وفي إعلان
Ma'ana Allah mai amsa kiran dukkan wanda ya kira shi ne. Yana amsa kiran kowa, hatta kafirai. Yana kuma amsa kiran kibantattun bayi, kamar wanda ya shiga matsin halin rayuwa, ya shiga tsanani.
Allah ya ce:
﴿أَمَّن یُجِیبُ ٱلۡمُضۡطَرَّ إِذَا دَعَاهُ وَیَكۡشِفُ ٱلسُّوۤءَ﴾ [النمل: ٦٢]
{Waye yake amsa wanda ya shiga matsi idan ya kira shi, kuma yake yaye mummunan abu...?}.
Kuma kamar yadda yake amsa addu'ar wanda aka zalunta. Haka yana amsa addu'ar duk wanda ya debe tsammanin samun biyan bukatarsa daga wajen mutane. Misali; mun gwada zaben shugaba wane mai gaskiya, amma ba mu ga canji ba. Mun gwada zaben Muslim - Muslim ticket, amma matsin rayuwan karuwa ya yi, to ya Allah yanzu kam mun yanke tsammani daga kowa sai kai kadai. Ba mu da wata dabara daga gare mu sai neman agajinka.
Idan da a ce bayi za su san girman Allah, su san cewa shi mai amsa roko ne, su rataya zukatansu gare shi, su roke shi, su yi masa naci, su nuna ba su da wata sauran dabara sai gare shi, su kira shi ta ko'ina, mutanen kasa daga yankuna da jihohi daban - daban, kabilu daban - daban, da tuni Allah ya amsa addu'arsu, ya karya kashin bayan duk wani azzalumi.
Amma kash! Mutane da yawa su mafita a wurinsu ita ce zanga - zanga, da sauran hanyoyin da gurbataccen tunaninsu yake ba su!
A gaskiya idan ba mu dawo cikin hayyacinmu, mun yi abin da ya kamata ba, za a dade ana shan wahala.
Allah ya sawake.