Subscribe Our Channel

 ME YA JANYO BULLAR DA'AWAR INTERFAITH?


Muna karatu da Malamina, na yi bayanin ingantattun hanyoyi na raddi ma Kiristoci, sabanin hanyoyin da Mabiya Ilmul Kalam suka bi wajen yi musu raddi, a ciki sai na kawo hanyar tabbatar da Manzancin Annabi Muhammad (saw) ta hanyar labarun da ya bayar, wadanda za su bayyana a gaba. (الإخبار بالمغيبات المستقبلة). A ciki sai na ambaci cewa; Annabi (saw) ya ba da labarin bayyanar Khawarijawa 'Yan Ta'adda, kuma ga shi sun bayyana kamar yadda Annabi (saw) ya fada, har SUN BAYYANA MA KOWA, KOWA YANA IYA SANINSU. Sai Malamina ya ce: A'a, ba kowa ne yake iya saninsu ba, Malamai ne suke iya saninsu.


To na yi mamakin wannar magana, ganin cewa; mu a Nigeria kowa ya ga barnar Boko Haram a fili. Don haka ya kamata a ce yanzu kam kowa zai iya gane Khawarijawa.


To ban tashi ganin hakikanin maganarsa ba sai da na zo nake bayani a kan Sayyid Qutub, inda na tabbatar da abin da Malamai da Manazarta suka tabbatar cewa; Sayyid Qutub shi ne tushen ta'addanci a wannan zamani. Sai ga wadanda mutane suke zaton sun fahimci Sunna amma su ne suka zama sojojin jayayya da kare barnar Sayyid Qutub. Kai, har ya kai ga wani ma shi jayayya yake yi a kan samuwar 'Yan Ta'adda a cikin Musulmai, -wai- kawai makirci ne na Turawa (نظرية المؤامرة).


To gaskiya ne, ba abin mamaki ba ne don mutane ba su san Khawarijanci ba, saboda akwai dalilai masu yawa da za su hana su sani. Saboda hatta a mas'alar Hakikanin Imani, a zahiri Khawarijawa ba su da banbanci da Ahlus Sunna. Shaikh Muhammad bn Ibrahim Alu-Shaikh yana bayanin Akidar Khawarijawa da Mu'utazila sai ya ce:

((وافقوا أهل السنة في أصل الإيمان أنه قول وعمل، لكن خالفوهم فقالوا: لا يتبعض ولا يتجزأ)).

شرح العقيدة الواسطية (ص: 128)


((Sun dace da Ahlus Sunna a tushen ma'anar Imani cewa; Magana ne da Aiki, sai dai suna saba musu inda suke cewa: ba ya rarrabuwa sashe - sashe, yanki - yanki)).


A wani wajen kuma ya ce:

((ويوافقون أهل السنة والجماعة في أنه قول وعمل، ويخالفون أهل السنة في أنه يتبعض ويتجزأ)).

شرح العقيدة الواسطية (ص: 187)


((Suna dacewa da Ahlus Sunnati wal Jama'a a ma'anar Imani cewa; Magana ne da Aiki, suna saba ma Ahlus Sunnan a cewa: Imanin yana rarrabuwa sashe - sashe, yanki - yanki)).


Ka ga a zahiri kamar babu banbanci. Amma inda banbancin yake shi ne wajen cewa: Imani yana rarrabuwa a wajen Ahlus Sunna, amma a wajen Khawarijawa kuma ba ya rarrabuwa. Wannan ya sa Sayyid Qutub ya ce:

((إن الإيمان وحدة لا تتجزأ))

في ظلال القرآن (2/ 798)


((Imani abu ne guda daya a dunkule ba ya rarrabuwa)).


Alhali a Mazhabar Ahlus Sunna Imani yana rarrabuwa, kamar yadda Ibnu Taimiyya ya ce:

((إن الإيمان مما يتبعض ويتجزأ)).

مجموع الفتاوى (12/ 491 - 492)


((Imani abu ne da yake rarrabuwa sashe - sashe, yanki - yanki)).


Don haka cewa; Imani yana rarrabuwa shi ya banbance Akidar Khawarijawa daga Akidar Ahlus Sunna. Idan mutum bai yi zurfi a karatu ba ba zai san wannan ba, musamman saboda rashin samun littatafan su Khawarijawan, sai dan abin da ba za a rasa ba a wajen "Ibadhiyya". Ga maganar babban Malaminsu a wannan zamani al-Khaliliy, a Ta'alikinsa ga wani littafin magabacinsu inda ya ce:

((وإذا اعتقد ما لزمه اعتقاده ولم يحضره فرض قولي أو عملي كان مؤمناً كامل الإيمان، وإذا وجب عليه شيء من الأقوال أو الأفعال وأداه كما وجب عليه ازداد إيمانه وإذا أخل بهذا الواجب انهدم إيمانه كله)).

مشارق الأنوار (ص 35- 36)


((Idan mutum ya kudurce abin da dole ya kudurce shi, kuma a lokacin wani farilla na aiki ko magana bai hau kansa ba, to ya kasance Mumini mai cikakken Imani. Amma idan wani abu na maganganu da aiyuka suka wajaba a kansa, kuma ya aikata shi, to Imaninsa ya karu, amma idan ya bar wannan wajibin to IMANINSA GABA DAYA YA RUSHE)).


To ka auna wannar magana ta wannan mutumi, da kuma maganar Sayyid Qutub inda ya ce:

((والإسلام منهج للحياة كلها. من اتبعه كله فهو مؤمن وفي دين الله. ومن اتبع غيره ولو في حكم واحد فقد رفض الإيمان واعتدى على ألوهية الله، وخرج من دين الله. مهما أعلن أنه يحترم العقيدة وأنه مسلم. فاتباعه شريعة غير شريعة الله، يكذب زعمه ويدمغه بالخروج من دين الله.))

في ظلال القرآن (2/ 972)


((Muslunci tsarin rayuwa ne gaba dayanta, wanda ya bi shi gaba dayansa shi Mumini ne, kuma yana cikin Addinin Allah. Amma wanda ya bi wani abu ba Muslunci ba ko da A HUKUNCI DAYA NE TO YA YI WATSI DA IMANI, ya yi ta'addanci a kan Uluhiyyar Allah, kuma YA FITA DAGA ADDININ ALLAH, duk yadda ya shelanta cewa; yana girmama Akidar Muslunci, kuma shi Musulmi ne. Binsa ga wata Shari'a ba ta Allah ba, yana karyata rayawarsa girmama Akida, kuma yana rusa shi ta hanyar fitarsa daga Addinin Allah)).


Idan ka lura da maganganun mutanen biyu, za ka ga iri daya ne. Kowannensu ya tabbatar da cewa; idan mutum ya yi dukkan wajiban Addini ya zama Mumini, amma idan ya bar wajibi daya to ya fita daga Muslunci.


To abin da nake so na isa gare shi shi ne; babu mai ilimi da zai yi inkarin Khawarijawa a cikin al'umma. Mai inkarin samuwarsu dayan uku ne, imma Jahili ko mabarnaci ne, mai son boye barnar mabarnata, ko kuma Dan "Safsata" ne, mai inkarin hakikanin abubuwa na zahiri.


Don haka abin da ya kamata a sani, su Turawa da Makiya Addinin Muslunci, ba su suka kirkiri Boko Haram da sauran Kungiyoyin Khawarijawa ba, a'a, su Khawarijawan su suka kafa Kungiyoyinsu da nufin yin Jihadi, amma na Bidi'a, saboda mummunar fahimtarsu ga Alkur'ani da guluwwi a Addini. Sai dai kuma su Turawa da Makiya Addinin Musluncin suna farin ciki da murna da bayyanarsu, kuma suna ribatar ta'addancin nasu. Kai, har za su iya taimaka musu su karfafe su, don su isa ga biyan bukatunsu na yakar Addini.


Yanzu ka duba asara da Addinin Muslunci ya yi a dalilin bullar ta'addancin Khawarijawan Boko Haram, harkar da'awa ta yi rauni matuka. An sa ido a kan masu da'awa zuwa ga Muslunci da Sunna. Da ma Ahlus Sunna su ne masu yi, sai kuma aka zo ana tuhumarsu da koyar da ta'addanci, saboda 'Yan Ta'addan suna cewa; -wai- su ma Ahlus Sunna ne. Alhali su masu tuhumar sun san karya suke yi, to amma saboda da shi za su yi amfani su hana Da'awa zuwa ga Muslunci da Sunna shi ya sa suke yada hakan. Alhali kowa ya san Khawarijawa 'Yan Ta'adda ba su da alaka da Mazhabar Ahlus Sunna.


A takaice, harkar Da'awa ta yi rauni, a dalilin matsalar tsaro, saboda ta'addancin Khawarijawa.


Bayan haka, daga cikin ribar da Turawa da Makiya Muslunci suka ci a bayyanar Khawarijawan Boko Haram, sai suka kafa Kungiyoyin Hade Addinai "وحدة الأديان" (Interfaith), da sunan neman zaman lafiya. Abin da a yanzu kasuwarsa take ci, saboda shi ne babban aikin da Ilhadin Duniya ya saka a gaba, a hade Addinai a koma Addini guda daya, wato shi ne Addinin mutumtaka (Humanity), a dena kyamar kafirci da kafirai, Musulmi ya koma kaunar kafirai da soyayya da su.


A takaice, abin da ya janyo bullar irin wadannan Kungiyoyi na hade Addinai shi ne wautar jahilai daga cikin Musulmai, Khawarijawa masu Addini da jahilci, masu barna a bayan kasa, suna barna amma suna zaton kyakkyawan aiki suke yi. Allah ya ce:

{قُلْ هَلْ نُنَبِّئُكُمْ بِالْأَخْسَرِينَ أَعْمَالًا (103) الَّذِينَ ضَلَّ سَعْيُهُمْ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَهُمْ يَحْسَبُونَ أَنَّهُمْ يُحْسِنُونَ صُنْعًا (104)} [الكهف: 103، 104]


((Ka ce: shin ba za mu ba ku labarin masu hasaran aiyukansu ba ne? Wadanda aiyukansu suka bace a rayuwar Duniya, alhali suna zaton su kyautata aiki suke yi)).


Sayyidina Aliyu (ra) ya ce: Wadannan su ne Khawarijawa.


Saboda haka idan ba mu yaki tunanin ta'addancin Khawarijawa da ke cikin al'ummar Musulmi ba, to Turawa da yaransu yanzu suka fara raba Musulmai da Addininsu da Imaninsu, da Mulhidantar da al'ummar da sunan yakar ta'addanci da tsattsauran ra'ayin Addini, da neman hadin kan mabiya Addinai don neman zaman lafiya.


A takaice, mafiya yawan mutane ba sa iya gane banbanci tsakanin Khawarijawa da Ahlus Sunna. Kuma Turawa da Makiya Muslunci suna ribatar wautar Khawarijawa suna yakar Muslunci da Musulmai cikin sauki, ta hanyar fakewa da samar da zaman lafiya.

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter