Subscribe Our Channel

 TARIHIN BULLAR KUNGIYOYIN TA'ADDANCI A WANNAN ZAMANI (4)


A rubutunmu da ya gabata a kan Tarihin Bullar Ta'addanci.., wato a kashi na (3), mun yi bayani a kan "Rundunar Sirri" (التنظيم السري) ta Kungiyar Ikhwan, wacce Hassanul Banna ya kafa ta. Mun ga asalin manufar kafa ta, mun ga yadda ake rantsuwar shiga rundunar, da kuma irin aiyukan Ta'addanci da rundunar ta aikata, wanda a karshe Dr. Mahmud Assaf ya dora alhakin lalacewar matasan Kungiyar ta Ikhwan, da gurbacewan tunaninsu, har suka dulmuya cikin aiyukan ta'addanci a kan Tasirin Fikrorin Sayyid Qutub a kansu, musamman ta hanyar abin da ya rubuta a littafansa guda biyu mafiya hatsari, wato: "Fi Zilalil Qur'an", da kuma "Ma'alim fi al-Dareeq", wanda matasan a cikinsu suka dauki Fikrar kafirta al'umma, da kuma Fikrar "Hakimiyya", har daga karshe kungiyoyin Khawarijawa suka bayyana. Kamar dai yadda Dr. Mahmud Assaf ya bayyana a littafinsa mai suna: (مع الإمام الشهيد حسن البنا).


A rubutun da ya gabata mun kawo misalai na irin aiyukan ta'addancin "Rundunar Sirri" ta Kungiyar Ikhwan, to yau ma za mu cigaba da kawo misalan ta'addancin rundunar ne. Misali na karshe na aikin ta'addanci da za mu kawo a yau shi ne ya zama sababin kashe shugaban Kungiyar ta Ikhwan, kuma wanda ya kafa ta, wato Hassanul Banna.


KISA NA UKU: KASHE SHUGABAN MINISTOCI (PRIME MINISTER) AHMAD MAHIR:


Bayan sauke shugaban Gomnati Mustapha al-Nahhas da aka yi a ranar 8 ga watan Oktoba, a 1944, da nada Ahmad Mahir a matsayin shugaban Gomnati (Prime Minister), ya rushe Majalisar wakilai, a ranar 15 ga watan Nawumba 1944, sai kuma ya ayyana ranar 8 ga watan Janairu 1945 a matsayin ranar zaben sabbin wakilai. Wannan ya sa Hasanul Banna shugaban kungiyar Ikhwan ya daura aniyar tsayawa takara da shiga zaben. Bayan an yi zabe sai bai yi nasaran cin zabe ba, sai Kungiyar Ikhwan ta yi zargin magudi cewa; magudi aka yi masa, shi ya sa bai ci zaben ba.

انظر: من قتل حسن البنا ؟ (ص: 74 - 76)


A dalilin wannan zargin magudin zabe da aka yi wa Hassanul Banna, har ya fadi a zabe, sai "Rundunar Sirri" ta Ikhwan (التنظيم السري) ta fara shirya kashe Shugaban Misnistoci Ahmad Mahir. Wanda aka ba da aikin ga Ahmad Abdulfattah Daha, amma sai ya tsorita, ya ki karban aikin. Washe gari da yin haka kuwa sai ga Mahmud al-Isawiy ya kashe Ahmad Mahir, a ranar 24 Feb 1945.


Shi wannan Mahmud al-Isawiy din Shaikh Sayyid Sabiq ya tabbatar da cewa; dan Ikhwan ne. Amma Mahmud Assaf ya kore kasancewarsa dan Ikhwan, ya ce: darasin Talata na Hasanul Banna yake halarta, wanda yake yi a duk sati. Dalilin da ya sa suka kashe shi, saboda ya kayar da Hassanul Banna a zabe.


Amma dai lallai Mahmud Assaf ya tabbatar da cewa; "Rundunar Sirri" (التنظيم السري) tana shirin kashe shugaban Ministoci Ahmad Mahir.

انظر: مع الإمام الشهيد حسن البنا (ص: 151 - 153)


A dalilin haka shi ma Hasanul Banna an kama shi, an kai shi kurkuku da sauran wadanda ake zargi da hanu a cikin kisan na Shugaban Ministoci.

انظر: من قتل حسن البنا ؟ (ص: 74 – 78 - 81)


To a nan ma dai akwai tuhuma mai karfi a kan wannar "Runduna ta Sirri" ta Kungiyar Ikhwan, wajen aikata wannan ta'addanci.


KISA NA HUDU: KASHE SHUGABAN MINISTOCI (PRIME MINISTER) NAQRASHIY:


Idan za a iya tunawa, a baya, a kashi na biyu na wannar silsila na Tarihin Bullar Ta'addanci, mun tabo abin da ya shafi kashe Mahmud Fahmiy al-Naqrashiy Basha, Prime Minister a kasar Misra, a inda muka ambaci bayanin kashe Ustaz Hassanul Banna, shugaban Kungiyar Ikhwan. Wanda ake ganin kashe Naqrashiy shi ne sababin kashe Hassanul Banna.


Kashe Naqrashiy ya biyo bayan matakin da ya dauka ne na rushe Kungiyar Ikhwan. Wanda wannan ya zo ne bayan mataki da Gomnatin Ingila ta dauka na kawo karshen yakin Falasdeen, da kokarin tabbatar da kasar Is*ra'ila. Matakin da Hukumar Naqrashiy ta aminta da shi, amma kungiyar Ikhwan ta yi watsi da shi. Wannan ya sa Gomnatin Naqrashi ta kame mayakan Kungiyar Ikhwan a sansanoninsu na soja a Falasdeen.


A wannan yanayi da ake ciki, akwai 'yan Ikhwan da yawa a tsare, saboda zargin wasu aiyukan masu alaka da ta'addanci, kamar khadhiyyar motar Jeep, da wasu daban. Kuma suna fiskantar tsanantawa da azabtarwa a kurkuku. Amma kuma akwai adadi na membobin "Rundunar Sirri" ta Ikhwan wadanda ba a kama su ba, saboda jami'an tsaro ba su san da su ba.


Bayan kama wadannan 'yan Kungiyar ta Ikhwan, shi ma Hassanul Banna an yi masa daurin talala, an hana shi haduwa da ganawa da mutane. Babu kowa a tare da shi sai mutum daya kawai, wani lauya mai suna Ustaz Abdulkareem Mansur, wanda miji ne ga 'yar'uwarsa. Wanda shi yake tare da Hassanul Banna a lokacin da aka kashe shi.


To ana cikin wannan yanayi su kuma membobin "Rundunar Sirri" ta Ikhwan suna can suna ganawa a boye, suna shirya aiyukan daukar fansa, inda suka shirya kashe shugaban Ministoci Naqrashiy.


Ahmad Fu'ad shi ne ya tsara yadda za a yi kisan, shi kuma Abdulmajeed Ahmad Hassan ya batar da kama, ya yi shigar 'yan sanda, ya yi nasarar harbin Naqrashiy, ya kashe shi har Lahira, a lokacin yana kokarin shiga lift, zai tafi ofishinsa a Ma'aikatar Cikin Gida. Wannan ya faru ne a ranar 28 ga Desemba 1948.


Kamar yadda ya gabata, kashe Naqrashiy shi ne sababin kashe Hassanul Banna, kamar yadda Dr. Mahmud Assaf ya bayyana.

انظر: مع الإمام الشهيد حسن البنا - محمود عساف (ص: 162 - 166)


To haka dai Tarihin Kungiyar Ikhwan yake cike da rigingimu da tafo-mu-gama da masu mulki, abin ya haifar da tunanin ta'addanci a cikin kwakwalen matasan kungiyar, musamman bayan tasirin da Fikrorin Sayyid Qutub suka yi a kansu, wanda daga karshe aka samu bayyanar Kungiyoyin Khawarijawa daban - daban, masu kafirta Musulmai su halasta jinanensu, su dauki makami suna kashe su. Kamar yadda Dr. Mahmud Assaf ya tabbatar, har ya zayyano sunayen kungiyoyin, wanda bayani a kan hakan ya gabata a rubutunmu na kashi na (3) na wannar silsila.


Za mu cigaba da iznin Allah.

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter