LABARIN ABU HANIFA DA MULHIDAI
Wata rana Munazara (Muqabala) ta kasance tsakanin babban Malamin Fiqhun nan Imamu Abu Hanifa da wasu Mulhidai masu kore samuwar Allah.
Ana cikin tattaunawa sai Imamu Abu Hanifa ya ce musu:
"Me za ku ce game da mutumin da ya ce muku ya ga wani babban jirgin ruwa, yana mak'are da kaya, an cika shi da kayayyaki daban - daban, yana tafiya a cikin Teku, ga igiyar ruwa mai tsanani tana ta juyawa, ga iska mai karfi tana ta kadawa, amma duk da haka jirgin nan yana ta tafiya a seti babu abin da yake kada shi, amma kuma jirgin ruwan ba shi da matuki da yake tuka shi.
To shin kuna ganin haka zai yiwu?!".
Sai suka zabura suka ce: A'a, wannan kam ba zai yiwu ba!
Ai wannan hankali ba zai kama ba!
Kai, ko da a mafarki hakan ba zai faru ba!
Sai Imam Abu Hanifa ya ce: "Subhanallah!
Idan a hankalce ba zai yiwu a samu jirgin ruwa ya yi tafiya a seti ba tare da matuki ba, to ta yaya zai yiwu a hankalce a ce: wannar Duniya da muke gani, mai cike da halittu daban - daban, ma'abociyar halaye da yanayi mabanbanta, ga ta da fadin kasa iya ganinka, amma a ce: -wai- ta faru ne ba tare da Mahalicci ba, kuma babu mai gudanar da ita a yanzu haka?!".
Ai nan da nan Mulhidai sai suka rude, suka ce: lallai ka fadi gaskiya.
To jama'a, ku duba ku gani fa!
Ashe rashin hankali ne mutum ya zo ya rena wa mutane hankula ya ce: babu Allah, babu Mahalicci, babu mai gudanar da Duniya da dukkan abin da ke cikinta na manyan halitu da mutane.
Duk mai hankali in ya fadi haka to shi ma ya sani a cikin zuciyarsa cewa; karya kawai yake yi.