Subscribe Our Channel

 SU WAYE MAFI SHARRIN HALITTA?


Ma'auni a wajen 'Yan Duniya, 'Yan Dadi Arna 'Yan Boko Aqida shi ne mata'i da kyalkyalin rayuwar Duniya. Wannan ya sa suke fifita Turawa da Yahudawa da Kiristoci a kan Musulmai, saboda kawai su suka fi cigaba a harkar boko da kere-kere da kimiyya da fasaha da gina rayuwar Duniya da samar da kayan jin dadi na zahiri.


Wannan shi ne ma'auni a wajensu. Wato rayuwar da manufarta da amfaninta kawai iya Duniyar ce kadai. Wato a rayu rayuwa maras manufa, face a ci a sha a ji dadi, a biya sha'awar jinsi, a yi bacci, kamar dai rayuwar dabbobi, kamar yadda Allah ya ce:

{وَالَّذِينَ كَفَرُوا يَتَمَتَّعُونَ وَيَأْكُلُونَ كَمَا تَأْكُلُ الْأَنْعَامُ وَالنَّارُ مَثْوًى لَهُمْ } [محمد: 12]


"Wadanda suka kafirta suna jin dadin rayuwa, suna cin abinci kamar yadda dabbobi suke ci, alhali wuta ce makomarsu".


Irin wannan cigaba cigaba ne na "madda" (material), ba cigaba ne na gyaran ruhi ba. Shi ya sa za ka ga su suke kira ga Ilhadi, da yada alfasha da bayyana tsiraici, da kira zuwa ga fita daga hankali da dabi'u na fidira (kamar auren jinsi) duka da sunan 'yanci.


Alhali ma'auni na hakika shi ne samun sa'ada da rabo da arziki a Duniya da Lahira, sa'adar da take samar da nitsuwar zuciya da rayuwa mai dadi a Duniya, da samun rayuwar ni'ima a Lahira. Rayuwar da ta ginu a kan imani mai raya zukata da samar musu da nitsuwa, da tabbatuwa a kan "qiyam" da kyawawan halaye da dabi'u na fidira, masu gadar da daukaka da izza a cikin rayuwa.


Shi ya sa Allah yake rarrashin Muminai, kar su rudu da rayuwa ta "madda" (Material), a'a, rayuwa ta imani bisa kyawawan halaye da dabi'u na fidira su ne ma'aunin daukaka da cigaba, Allah ya ce:

{ وَلَا تَهِنُوا وَلَا تَحْزَنُوا وَأَنْتُمُ الْأَعْلَوْنَ إِنْ كُنْتُمْ مُؤْمِنِينَ } [آل عمران: 139]


"Kada ku raunana, kada ku yi bakin ciki, ku ne madaukaka in kun kasance Muminai".


Saboda haka muke kira ga Musulmai, kar su rudu da wannan cigaban da ake ta yi musu karya da ita, -wai- cigaban Turawa a rayuwar Duniya. Ina amfanin cigaban da bai hana mutum hasara a Lahira da zama mafi sharrin halitta ba?

Allah ya ce:

{إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ وَالْمُشْرِكِينَ فِي نَارِ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا أُولَئِكَ هُمْ شَرُّ الْبَرِيَّةِ } [البينة: 6]


"Lallai wadanda suka kafirta cikin Ahlul Kitabi (Yahudu da Nasara) da Mushrikai, suna cikin wutar Jahannama, za su dawwama a cikinta, wadannan su ne mafi sharrin halitta".

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter