BA A KIRAN FITINA TSAKANIN MUSULMAI DA SUNAN TA'ADDANCI
Babbar matsalar matasan da suka nada kawunansu a matsayin Malamai, kuma masu Jarhi da Ta'adili da yanke hukunci a kan Malamai Ahlus Sunna da bidi'antar da su tare da Kungiyoyinsu ita ce: rashin "Ta'asili" a ilimi, wato rashin sanin mas'alolin ilimi daga tushensu na dalilan Shari'a; daga Alkur'ani da Sunna.
Malamai suna kasa daukar makami da ake samu a cikin al'ummar Musulmai zuwa kashi uku:
1- Ta'addancin Khawarijawa, na fita daga al'umma da halasta jinanen Musulmai, da dukkan jinane da Allah ya haramta, kamar jinanen Kafiran Alkawari da makamantansu. Annabi (saw) ya ba da labarinsu inda ya ce:
«إن من ضئضئ هذا، قوما يقرءون القرآن، لا يجاوز حناجرهم، يمرقون من الإسلام مروق السهم من الرمية، يقتلون أهل الإسلام، ويدعون أهل الأوثان، لئن أدركتهم لأقتلنهم قتل عاد»
صحيح البخاري (9/ 127) صحيح مسلم (2/ 741)
"Lallai daga asalin wannan mutumi (Zul Khuwaisirah) akwai wasu mutane za su fito, suna karanta Alkur'ani amma ba ya wuce makogoronsu, suna fita daga Muslunci kamar fitan mashi daga abin da aka jefa, suna kashe Ma'abota Muslunci suna barin Ma'abota bautar gumaka, in na riske su zan kashe su kisan Adawa".
Wannan abin da Khawarijawa suke yi, a yau shi ake kira da sunan "TA'ADDANCI", kuma akwai Kungiyoyi na Musamman bisa wannan TA'ADDANCI, tun daga kan Al-Qa'ida, ISIS, Al-Shabab da kuma Boko Haram da makamantansu. A yau in kira Ta'addanci wannan ake nufi.
Shi ne abin da muka ce: Sufaye ba sa yin irinsa saboda dalilai da muka ambata a baya.
2- "Bagyu" na 'Yan Tawaye, wato shi ne yaki da gomnati, wanda yake kasancewa bisa tawaye wa shugaba, bisa manufofi na Siyasa, kuma babu kafirta juna a cikinsa. Malamai suna banbanta wannan da Ta'addancin Khawarijawa. Suna misali da shi da yakin da ya faru tsakanin Aliyu (ra) da Mu'awiya (ra). Yaki ne da Mu'awiya (ra) yake da Tawili. Shi ya sa Allah ya ce:
{ وَإِنْ طَائِفَتَانِ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ اقْتَتَلُوا فَأَصْلِحُوا بَيْنَهُمَا فَإِنْ بَغَتْ إِحْدَاهُمَا عَلَى الْأُخْرَى فَقَاتِلُوا الَّتِي تَبْغِي حَتَّى تَفِيءَ إِلَى أَمْرِ اللَّهِ فَإِنْ فَاءَتْ فَأَصْلِحُوا بَيْنَهُمَا بِالْعَدْلِ } [الحجرات: 9]
"In bangarori guda biyu na Muminai sun yi yaki tsakaninsu to ku yi musu Sulhu, amma in daya daga cikinsu ya yi zalunci a kan daya to ku yaki wanda ya yi zaluncin har sai ya dawo ga umurnin Allah, in ya dawo sai ku yi Sulhu tsakaninsu bisa adalci".
3- Yakin Fitina da yake kasancewa tsakanin Kungiyoyin Musulmai masu dangantuwa zuwa ga Muslunci. Annabi (saw) ya ce:
«إذا التقى المسلمان بسيفيهما فالقاتل والمقتول في النار»
صحيح البخاري (1/ 15) صحيح مسلم (4/ 2213)
"Idan Musulmai guda biyu suka yi fada da takubansu to wanda ya yi kisa da wanda aka kashen duka suna wuta".
Irin wannan shi ne wanda yake kasancewa tsakanin Musulmai a junansu na fada na fitina, har da daukar makami.
Shaikhul Islami ya ce:
إذا كانت فتنة بين المسلمين، مثل أن يقتتل رجلان أو طائفتان على ملك أو رئاسة أو على أهواء بينهم، كأهواء القبائل والموالي الذين ينتسب كل طائفة إلى رئيس أعتقهم، فيقاتلون على رئاسة سيدهم، وأهواء أهل المدائن الذين يتعصب كل طائفة لأهل مدينتهم، وأهواء أهل المذاهب والطرائق كالفقهاء الذين يتعصب كل قوم لحزبهم ويقتتلون، كما كان يجري في بلاد الأعاجم، ونحو ذلك، فهذا قتال الفتنة ينهى عنه هؤلاء وهؤلاء
جامع المسائل لابن تيمية (4/ 231)
"Idan Fitina ta kasance tsakanin Musulmai, misali mutum biyu, ko kungiyoyi biyu su yaki juna a kan mulki ko shugabanci ko a kan wani son zuciya tsakaninsu, kamar son zuciyan kabilu da maulaye wadanda kowanne bangare yake dangantuwa zuwa ga shugaban da ya 'yanta su, sai su yi yaki a kan shugabancin uban gidansu, ko kuma son zuciya na 'yan garanci, wanda kowane bangare yake ta'assubanci ga mutanen garinsu, da kuma son rai na Mazhabobi da Darikoki, kamar Malaman Fiqhu wanda kowadanne mutane a cikinsu suke ta'assubanci ga Kungiyarsu har su yi yaki a tsakaninsu, kamar yadda hakan yake faruwa a garuruwan Ajamawa, da makamancin haka, to wannan yaki ne na Fitina, ana hana wadannan da wadannan duka".
Don haka fitina da take faruwa tsakanin Musulmai, kamar fada da makami tsakanin 'Yan Darikun Sufaye da Ahlus Sunna a kan Masallaci ko wani abu daban duka yana cikin fitina tsakanin Musulmai, ba a kiransa da sunan TA'ADDANCI wanda aka san Khawarijawa da shi.
Haka kuma, Shirka da 'Yan Darikun Sufaye suke yi ba a kiransa da TA'ADDANCI bisa ma'anar TA'ADDANCIN Khawarijawa, abin da ake kiransa shi ne kaskantar da Allah da rena shi da rashin girmama shi.
Ibnul Qayyim ya ce:
إن الشرك هضم لحق الربوبية، وتنقيص لعظمة الإلهية، وسوء ظن برب العالمين
إغاثة اللهفان (1/ 60 – 61)
"Lallai shirka tauye hakkin Rububiyya ce, da kaskantar da girman Uluhiyyar Allah, da munana zato ga Ubangijin Talikai".
To duk wanda ya tattauna da galibin 'Yan Kungiyar Salafiyyun zai fahimci sun jahilci wadannan banbance - banbance da ke tsakanin wadannan nau'uka na fadace - fadace ko yakukuwa a cikin al'ummar Musulmi, ta yadda za ka same su suna kiran kowanne da sunan KHAWARIJANCI da TA'ADDANCI. Alhali wannan jahilci ne da rashin "Ta'asili" da son kutsawa cikin mas'alolin ilimi ba tare da sani ba, da matukar kwadayin yanke hukunci wa mutane da bidi'antar da su saboda guluwwi.
Saboda haka, ta yaya za a yi wanda bai san "Usul" na Masa'il ba, wato dalilai da ake gina mas'alolin nan a kansu, amma kuma ya nada ma kansa rawanin bidi'antarwa, a matsayin "Hamilu liwa'il Jarhi wat Ta'adeel" na Nigeria?!
Allah ya yi mana tsari da rudin Shaidan.