A garin Rayyu an yi wani mutum da ake kira Mahmud bn Hassan Al-Himsiy, Malami ne na Rafidha 'Yan Shi'a. Ya kasance yana cewa: -wai- Aliyu (ra) ya fi dukkan Annabawa falala in ban da Annabi Muhammad (saw).
Mene dalilinsa?!
Sai ya ce: dalinsa shi ne fadin Allah Madaukaki:
{فَقُلْ تَعَالَوْا نَدْعُ أَبْنَاءَنَا وَأَبْنَاءَكُمْ وَنِسَاءَنَا وَنِسَاءَكُمْ وَأَنْفُسَنَا وَأَنْفُسَكُمْ ثُمَّ نَبْتَهِلْ فَنَجْعَلْ لَعْنَتَ اللَّهِ عَلَى الْكَاذِبِينَ } [آل عمران: 61]
"Ka ce: ku zo mu kira 'ya'yanmu da 'ya'yanku, matanmu da matanku, kawunanmu da kawunanku sai mu kaskantar da kai mu yi addu'a, mu sanya tsinuwar Allah a kan makaryata".
Saboda Hassan da Hussain (ra) ake nufi da "أَبْنَاءَنَا", Fatima (ra) kuma ake nufi da "وَنِسَاءَنَا", Aliyu (ra) kuma ake nufi da "وأنفسنا", don haka a ganinsa ba Annabi (saw) ake nufi a cikin "وأنفسنا" ba, don mutum ba ya kiran kansa, don haka wani mutum daban ake nufi, kuma kowa ya san cewa; wanin da ake nufi dole ya zama shi ne Aliyu (ra).
Don haka -wai- Ayar ta yi nuni ne a kan cewa; ran Aliyu (ra) ita ce ran Annabi (saw), ma'ana, Aliyu kamar Annabi (saw) yake, su biyun a matsayi daya suke ta kowace fiska. Sai dai kawai Aliyu (ra) ba Annabi ba ne bisa Ijma'i, kuma an yi Ijma'i a kan cewa; Annabi Muh'd (saw) ya fi Aliyu (ra) falala, kuma Ijma'i ya yi nuni a kan cewa; Annabi (saw) ya fi sauran Annabawa, don haka dole ya zama cewa: Aliyu (ra) ya fi sauran Annabawa, Annabi (saw) ne kawai ya fi shi a cikin Annabawa.
Amsa:
To kamar yadda aka yi Ijma'i a kan cewa; Annabi Muh'd (saw) ya fi Aliyu (ra), to haka aka yi Ijma'i tun kafin a haifi shi wannan Malamin Shi'an a kan cewa: mutum Annabi ya fi mutumin da ba Annabi ba falala. Kuma an yi Ijma'i a kan cewa; Aliyu (ra) ba Annabi ba ne. Don haka dole kowa ya yarda cewa: Duk wani Annabi ya fi Aliyu (ra) falala tun da Aliyun (ra) ba Annabi ba ne.
Tafsrin Fakhruddeen Al- Raziy (8/ 248)
Wannar mas'ala tana daga cikin mas'alolin da suka sa wani babban Malamin Shi'a a Nigeria ya bar Shi'a, saboda ya ji Zakzakiy ya ce: Ali (as) ya fi kowane Annabi in ban da Annabi Muhammad (saw).