Subscribe Our Channel

 Adai kan maulidi ne!


Ibn taimiyya a cikin littafinsa 

اقتضاء الصراط المستقيم مخالفة أصحاب الجحيم (252)


- Tabbas yayi batu kan samun lada ga wanda yayi maulidi, yake cewa:


"و الله قد يثيبهم علي هذا المحبة والاجتهد، لا علي البدع"


- Akwai abin lura sosai a cikin wannan batu:


1- Idan muka lura kodai malam yana nufin zasu samu ladar nuna soyyayarsu ta hanyar maulidi ga wanda yake ƙoƙarin neman gaskia ba tare da ilimin kasancewar maulidi bid'a bane ya riske shi, A'a shi dai ya aikata ne abisa shi yana ganin daidai ne, ba tare da wani ya bayyana mai bid'ancin hakan ba ko ya riska.

.

2- ko kuma yana nufin Allah zai basu ladar ne akan sonsu ga Annabi (S.A.W) da ƙoƙarinsu akan hakan amma ba akan ita ainihin bid'ar maulidin ba (Son shi da ya kubuta da ga bid'ar), shiyasa yayi ƙaidi.

.

"Domin babu yadda za'ayi Ibn Taimiyyah yace Maulidi bid'a ne, kuma yace za'a samu lada, kuma dama maganarsa sam bata hukunta hakan"

.

- kuma ni abinda nake cewa bada maganar ibn taimiyya ya kamata ku nemawa maulidi mafaka ba a'a matattarar da shima ibn taimiyyya yake komawa garesu ya kamata (Al-kur'ani da sunnah).


Allah ya kyauta


Ibrahim Yunusa Abu-Ammar

05 Nov. 2019

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter