WANI MALAMIN DARIQA YA BAYYANA KUSKUREN MALAMAN DARIQA A NIGERIA
Wasu Malaman Dariqa a Nigeria suna kafa hujja a kan Bidi'o'insu musamman Maulidi, da cewa: Abu ba zai zama Bidi'a ba har sai an samu hani a kansa a Alkur'ani ko a Hadisi. Har ka ji suna cewa; a kawo musu inda aka ce kar a yi abin.
Ma'ana dai su ba su yarda da Sunna ta bari ba (السنة التركية). Su ba su yarda wani abu a Addini ya zama Bidi'a ba har sai an samu wata Aya ko wani Hadisi da ya yi hani a kan shi wannan abin da suka kirkira suke aikatawa da sunan Ibada. Wannan ya sa da zaran ka ce musu abu kaza Bidi'a ne, sai su ce maka: Kawo inda aka hana yinsa.
To alal hakika wannan jahilci ne, saboda duk wanda ya fahimci ka'idojin Ilimomin Addini - hatta cikin Malaman Dariqa - kamar ilimin "Usul Fiqh" za ka samu suna tabbatar da cewa; duk abin da Annabi (saw) bai yi ba, alhali akwai sababin yin abin a zamaninsa, kuma babu wani uzuri da ya hana yi to wannan abu ya zama Bidi'a.
Don haka babu mai jayayya a kan haka sai jahili, wanda da a ce: zai yi shiru da sabani ya ragu.
To wannan jahilci da wasu cikin Malaman Dariqa a Nigeria suke yadawa, cewa; abu ba ya zama Bidi'a a Addini har sai an samu dalilin da ya yi hani a kai karara, an samu wani babban Malamin Dariqa inda ya yi magana ta Ilmi, ya yi musu raddi.
Haka Malamin ya yi musu raddi a wata maganar da suka makalkale mata, wato ra'ayin nan na kasa Bidi'a zuwa kashi biyu:
1- Bidi'a kyakkyawa.
2- Bidi'a maras kyau.
Wannan Malami da ya yi ma 'yan'uwansa Sufaye raddi shi ne Ibnu Hajar al-Haitamiy al-Makkiy. Ga maganar Malamin kamar haka, inda ya ce:
((إن البدعة الشرعية ضلالة كما قال - صلى الله عليه وسلم -. ومن قسمها من العلماء إلى حسن وغير حسن فإنما قسم البدعة اللغوية. ومن قال "كل بدعة ضلالة" فمعناه البدعة الشرعية. ألا ترى أن الصحابة رضي الله عنهم والتابعين لهم بإحسان أنكروا فرضية غير الصلوات الخمس، كالعيدين وإن لم يكن فيه نهي. وكرهوا استلام الركنين الشاميين، والصلاة عقيب السعي بين الصفا والمروة قياسا على الطواف. وكذا ما تركه - صلى الله عليه وسلم - مع قيام المقتضي فيكون تركه سنة وفعله بدعة مذمومة.
وخرج بقولنا: "مع قيام المقتضي في حياته" تركه إخراج اليهود من جزيرة العرب، وجمع المصحف. وما تركه لوجود المانع كالاجتماع للتراويح، فإن المقتضى التام يدخل فيه المانع)).
الفتاوى الحديثية لابن حجر الهيتمي (ص: 281)
((Lallai Bidi'a ta Shari'a bata ce, kamar yadda Annabi (saw) ya fada. Amma cikin Malamai wanda ya kasa Bidi'a zuwa Bidi'a mai kyau da Bidi'a maras kyau, shi fa Bidi'a ta Lugha yake nufi. Amma wanda kuma cikin Malaman ya ce: kowace Bidi'a bata ce, Bidi'a ta Shari'a yake nufi.
Shin ba ka ga Sahabbai da Tabi'ai ba ne, sun yi inkarin farlancin duk wata Sallah ba guda biyar din nan ba, kamar Sallolin Eidi biyu, duk da cewa; babu Nassin da ya yi hani a kan haka?
Haka kuma suka karhanta shafan rukunai guda biyu da suke jikin dakin Ka'aba, masu kallon setin Shaam, kuma suka karhanta yin Sallar Nafila bayan gama Sa'ayi tsakanin Safa da Marwa, wadanda aka yi kiyasi a kan Nafila bayan dawafi (sun karhanta wadannan duk da cewa; ba wani Nassi aka samu ya yi hani a kai ba).
Haka duk abin da Annabi (saw) ya bari bai aikata ba, tare da cewa; akwai sababin aikatawan a zamaninsa, to barin wannan abin ya zama Sunna, aikata shi kuma ya zama Bidi'a abin zargi.
Cewa da muka yi: "Tare da samuwar sababin aikata abin a zamanin Annabi (saw)" barinsa ga fitar da Yahudawa daga "Jaziratul Arab", da barinsa ga Tara Mus'hafi a wari daya, da kuma abin da ya bari saboda an samu wani uzuri da ya hana yi, kamar Jam'in Sallar Tarawihi sun fita daga cikinsa. Saboda a kan iya samun wani abu da zai hana samuwar aiki ya shiga cikin cikakken sababi da yake lazimta samuwar aiki sai ya hana samuwar aikin)).
Ka ga sai Malamin Dariqar ya yi raddi ga Malaman Dariqa, wadanda ba su san me ake nufi da Bidi'a ba, inda ya nuna musu abubuwa kamar haka:
1- Shi fa kasa Bidi'a zuwa kashi biyu; Bidi'a mai kyau da maras kyau, ana fadinsa ne a Bidi'a ta Lugha ba ta Shari'a ba. Wato kirkiran abubuwa da suka shafi al'amuran rayuwa, ba wadanda suka shafi Addini ba.
2- Bidi'a ta Shari'a, wato abubuwa na Ibada da Akida wadanda aka kirkira aka shigar da su cikin Addini ita kam bata ce gaba dayanta.
3- Wannan ya sa Sahabbai da Tabi'ai suka yi inkari, kuma suka karhanta wasu aiyukan Ibada saboda Shari'a ba ta zo da su ba. Wadanda ya ambaci misalansu, kamar yin Nafila bayan Sa'ayi tsakanin Safa da Marwa.
4- Haka kuma duk abin da Annabi (saw) ya bari bai aikata ba, kuma a zamaninsa akwai sababin da zai sa a yi wannan abin, kamar Maulidi, tun da sababin yinsa shi ne Son Annabi (saw), amma duk da haka bai yi ba, kuma babu wani abu da ya hana a yi, wannan shi yake nuna barin Maulidi Sunna ne, yinsa kuma Bidi'a ce abin zargi.
5- Amma abubuwa da ba a samu sababin yinsu a zamanin Annabi (saw) ba, kamar koran Yahudawa daga "Jaziratul Arab" da Tara Mus'hafi, ko kuma abubuwan da an samu sababin amma sai kuma aka samu wani dalili da ya hana a yi su, kamar Jam'in Sallar Tarawihi to su kam ba a kiran aikata su da sunan Bidi'a a Shari'a. Kai, wasu daga cikinsu kam Sunna ne ma, kamar koran Yahudawa daga "Jaziratul Arab", da Jam'in Sallar Tarawihi. Sauran kuma sai su zama "Maslaha Mursala".
A takaice dai ya bayyana mana cewa; Malaman Dariqa a Nigeria, masu cewa; abu ba zai zama Bidi'a ba har sai an samu Nassi ya yi hani a kan aikata wannan abin maganarsu jahilci ce.
Haka masu kasa Bidi'a gida biyu mai kyau da maras kyau, su ma ya kamata su san cewa; wannan ana magana ne a kan Bidi'a ta Lugha ba ta Shari'a ba. Amma Bidi'a ta Shari'a kam, wato kirkiran wata Ibada ko wata Akida a cikin Addini bata ne. Saboda Addini ya cika tun zamanin Annabi (saw). Duk abin da bai zama Addini a wancan lokacin ba, ba zai zama Addini a yau ba.