RIQO DA AL-KUR'ANI DA SUNNAH // 2
.
Allah ta'ala yana cewa: "Wanda yayi da'a ga manzo Hakika yayi wa Allah da'a" [Nisa'i : 80].
— Wannan aya tana nusar damu cewa lallai dukkanin wanda ya riki Al-kur'ani da sunnar manzon Allah wacce ke fassara Al-kur'ani, hakika Allah yayiwa da'a, domin Allah shine ya aiko manzon da littafin sannan ya bawa manzon kwangilar bayani ga bayinsa dake bayan kasa.
.
* Allah yana fada a wata ayar: "kace (dasu ya manzon Allah) in kun kasance kuna son Allah to kubini, Allah zai so ku..." [Ali-Imran : 31].
— Hakika duk wanda yayi da'a ga manzon Allah, Allah zai soshi, wanda kuma Allah zai saka shi wata mashiga da kowa yake fatan shigarta.
.
* A wata ayar Allah yana cewa: "Kace (dasu) kuyi da'a ga Allah, da manzo, Idan kuka juya baya hakika Allah baya son kafurai" [Ali-Imran : 32].
— Yin da'a ga Allah shine riko da Al-kur'ani, yin Da'a da manzon Allah shine yin da'a ga sunnarsa, dukkan wanda ya juya baya daga barin riko dasu to hakika Allah baya son su, domin su ba musulmai ba ne.
.
* Allah ta'ala yana cewa: "Wanda yayi da'a ga Allah da manzonsa, hakika ya rabauci wani rabo mai girma" [Ahzab : 71], kuma yana cewa: "Wanda yayi da'a ga Allah da manzo, kuma wadancen suna tare da wadanda Allah yayi ni'ima akansu..." [Nisa'i 69].
— Kenan duk mai son rabauta, da kuma kyakykyawan rabo duniya da lahira, sannan kuma ya kasance cikin wadanda Allah yayi ni'ima akansu to ya rungumi Al-kur'ani da sunna.
.
* Hadisi ya tabbata a cikin bukhari (2697), da muslum (1718), A hadisin Uwa ga duk Muminai, Matar Dan gatan Allah, Mai gaskiya, diyar mai gaskiya abokin manzon Allah kuma surukinsa, Mafi soyuwa ga manzon Allah, Wacce take matsayin uwa ga nana fadima, Aishatu diyar Abubakar mai gaskiya, matar manzon Allah Allah ya kara yarda a gare ta tace: Mijinta Mai sonta da kaunarta, wanda aka bunne a dakinta, Abul-Kasim yace: "wanda ya kirkiro wani abu a cikin al-amarinmu wannan, wanda baya cikinsa, to an mayar masa" a ruwayar muslum kuma: "wanda ya aikata wani aiki, ba tare da umurnin mu ba to an mayar masa".
— kenan duk wanda ya aikata wani aiki ba tare da Umurnin Allah ko manzonsa ba, lallai wannan aikin ba karbabbe bane.
.
* A wani hadisin kuma wanda Abu-dawood ya fitar hadisi mai lamba (3991), da turmizi (2600) hadisin Abu-Najiih Irbad dan sariyah Allah ya kara yarda dashi yace: ('Manzon Allah SAW yayi mana wa'azi, wazin da yake razana zukata, ya sanya idanu zubar da hawaye, Sai muka ce dashi ya manzon Allah! Wannan kamar wa'azin bankwana? Kayi mana wasiyya, sai yace: "Ina maku wasiyya da jin tsoron Allah SAW, daji da da'a, kuma koda an shugabantar akanku bakin bawa, kuma duk wanda yayi tsawon rayuwa daga cikinku to zaiga sabani mai yawa, To ina maku wasiyya da bin sunnah ta da sunnar khalifofina shiryayyu masu shiryarwa, ku riketa da hakoranku na kurya, kuma na haneku da fararrun abubuwa, domin dukkanin bid'a batace" ').Imamut-tirmizi yace wannan hadisin hasan ne kuma ingantacce, kuma Al-bani ya inganta shi acikin saheehul-Jami'e (2549).
— Wannan hadisi yayi mana bayani baro-baro dangane da bin Al-kur'ani da sunnah, da kuma shiriyar khalifofin Manzon Allah SAW.
.
Ya Allah ka bamu ikon bin gaskiya duk inda take ka bamu damar gujewa karya duk inda take (Akwai cigaba).
.
Abu-Ammar.
21/06/1438H. - 2017M.