*DA MUNGUWAR RAWA GARA KIN TASHI… (4)*
*YAYE SHUBUHOHIN MASU KARE SAYYID QUTUB A KAN AKIDARSA TA KHAWARIJANCI:*
A rubutunmu kashi na (2) da na (3) da suka gabata mun yi raddi ga mai jingina "Hakimiyya" Akidar Khawarijawa ga Shaikh Muhammad bn Ibrahim Alu-Shaikh ta hanyar "Muqarana" tsakaninsa da Sayyid Qutub. Don saboda ba za a fahimci gaskiyar danganta masa "Hakimiyyar" ba sai ta hanyar "Muqarana" tsakanin Akidarsa da ta Sayyid Qutub din, mutumin da ya fi kowa tabbatar da "Hakimiyyar". Wannan ya sa muka bayyana wa mutane Akidar Sayyid Qutub don a banbance matsayarsa a kan mas'alolin Addini, da ta Shaikh Muhammad bn Ibrahim.
To masu kare Sayyid Qutub din sun yi "I'itiradhaat" wadanda suke bukatar a yi jawabi a kansu, don raddin ya zama cikakke. Jawabin zai kasance ne ta hanyar bayanin wasu ka'idoji, da kuma "dabbaqa" su a kan maganganun Sayyid Qutub. Hakan zai kasance ne ta fiskoki biyar - da iznin Allah - kamar haka:
1- DOLE NE LAZIMTAR LAFUZAN SHARI'A DADAI GWARGWADO A BABIN AQIDA:
Yana daga cikin Manhajin Ahlus Sunna a Babin Mas'alolin Akida lazimtar lafuzan Shari'a iya iyawarsu. Saboda lafuzan Shari'a su ne suke rarrabe tsakanin karya da gaskiya. Wannan ya sa Magabata suke sanya Alkur'ani da Sunna a matsayin jagora wajen bayanin gaskiya. Sai su tabbatar da abin da Allah da Manzonsa suka tabbatar su kore abin da suka kore.
Misali daga maganganun Salaf a kan haka:
Imam al-Auza'iy an tambaye shi a kan lafazin "Jabar" sai ya ce:
((ما أعرف للجبر أصلا من القرآن والسنة، فأهاب أن أقول ذلك ولكن القضاء والقدر والخلق والجبل، فهذا يعرف في القرآن والحديث عن رسول الله صلى الله عليه وسلم)).
السنة لأبي بكر بن الخلال (3/ 555)، شرح أصول اعتقاد أهل السنة والجماعة (4/ 775)
((Ban san asalin "Jabar" a Alkur'ani da Sunna ba, don haka ina tsoron fadinsa. Amma na san lafuzan "Qadha'u" da "Qadar" da "Khalq" da "Jabal", wadannan an sansu a Alkur'ani da Hadisi, daga Manzon Allah (saw))).
Ibnu Taimiyya ya nakalto daga gare shi da Imam Ahmad da wasunsu ya ce:
((قال الأوزاعي وأحمد ونحوهما: من قال إنه جبر فقد أخطأ، ومن قال لم يجبر فقد أخطأ، بل يقال: إن الله يهدي من يشاء ويضل من يشاء، ونحو ذلك.
وقالوا: ليس للجبر أصل في الكتاب والسنة، وإنما الذي في السنة لفظ الجبل لا لفظ الجبر)).
درء تعارض العقل والنقل (1/ 255)
Akwai wasu misalan ma a kan haka.
Saboda haka Manhaji ne na Ahlus Sunna yin amfani da lafuza na Shari'a a babin Akida, saboda su lafuza ne da suka kunshi gaskiya tsantsa.
Amma duk da haka idan lafazi ma'anarsa mai kyau ne, ba ya dauke da mummunar ma'ana (ba lafazi ne "Mujmali" ba) suna iya amfani da shi, musamman idan ba su samu lafazi na Shari'a ba.
2- NISANTAR LAFUZAN BIDI'A DA LAFUZA "MUJMALAI" DUNKULALLU:
Kasancewar Ahlus Sunna suna takaituwa ne da lafuza na Shari'a, ko lafuza masu ma'anoni masu kyau, shi ya sa ba sa amfani da lafuza "Majmalai", wadanda suka kunshi ma'anoni masu kyau da kuma munana, balle kuma lafuza na Bidi'a. dalili a kan haka shi ne; saboda Manhajin Ahlus Sunna ya ginu ne a kan "Ittiba'i" (Bin Alkur'ani da Sunna), ba "Ibtida'i" ba (kirkiran Bidi'a).
Ibnu taimiyya ya yi bayanin Manhajin Ahlus Sunna a wannar ka'ida inda ya ce:
((يوجد كثيرا في كلام السلف والأئمة النهي عن إطلاق موارد النزاع بالنفي والإثبات، وليس ذلك لخلو النقيضين عن الحق، ولا قصور، أو تقصير في بيان الحق، ولكن لأن تلك العبارة من الألفاظ المجملة المتشابهة المشتملة علي حق وباطل، ففي إثباتها إثبات حق وباطل، وفي نفيها نفي حق وباطل، فيمنع من كلا الإطلاقين، بخلف النصوص الإلهية فإنها فرقان فرق الله بها بين الحق والباطل، ولهذا كان سلف الأمة وأئمتها يجعلون كلام الله ورسوله هو الإمام والفرقان الذي يجب اتباعه، فيثبتون ما أثبته الله ورسوله، وينفون ما نفاه الله ورسوله، ويجعلون العبارات المحدثة المجملة المتشابهة ممنوعا من إطلاقها: نفيا إثباتا، لا يطلقون اللفظ ولا ينفونه إلا بعد الاستفسار والتفصيل، فإذا تبين المعني أثبت حقه ونفي باطله، بخلاف كلام الله ورسوله، فإنه حق يجب قبوله، وإن لم يفهم معناه، وكلام غير المعصوم لا يجب قبوله حتى يفهم معناه)).
درء تعارض العقل والنقل (1/ 76)
Sai Ibnu Taimiyya ya bayyana cewa; Salaf da A'imma suna hani a kan yin amfani da lafuza da aka yi sabani a kansu, saboda lafuza ne dunkulallu masu rikitarwa, wadanda suka kunshi karya da gaskiya. Idan aka fade su aka tabbatar da su an tabbatar da karyan da ke cikin lafazin, haka idan aka kore shi an kore gaskiyar da ke cikinsa. Don haka Salaf suke sanya Alkur'ani da Sunna a matsayin su ne jagora gare su, saboda su suke rarrabe tsakanin karya da gaskiya.
Wannan lafazi "Mujmali" kenan, ina kuma ga lafazi na bidi'a kirkirarre?!
Saboda haka hanyar Ahlus Sunna a babin Addini, musamman mas'alolin Akida ba sa amfani da lafuza dunkulallu balle kirkirarru na Bidi'a. Kawai suna takaituwa ne a kan lafuza na Shari'a, iya iyawarsu. Sai dai idan babu sai su yi amfani da lafazi mai kyakkyawar ma'ana zalla. Ibnu Taimiyya ya yi bayanin haka inda ya ce:
((طريقة السلف والأئمة أنهم يراعون المعاني الصحيحة المعلومة بالشرع والعقل، ويراعون أيضا الألفاظ الشرعية، فيعبرون بها ما وجدوا إلى ذلك سبيلا، ومن تكلم بما فيه معنى باطل يخالف الكتاب والسنة ردوا عليه، ومن تكلم بلفظ مبتدع يحتمل حقا وباطلا نسبوه إلى البدعة أيضا)).
درء تعارض العقل والنقل (1/ 254)
((Hanyar Salaf da A'imma: suna kiyaye ingantattun ma'anoni da suke sanannu a Shari'a da hankali, kuma suna kiyaye amfani da lafuza na Shari'a, da su suke bayanin Akidarsu dadai gwargwado. Amma wanda ya yi magana da lafazin da a cikinsa akwai mummunar ma'ana, wacce ta saba ma Alkur'ani da Sunna to za su watsar masa kayansa, haka wanda ya yi magana da lafazi na Bidi'a, wanda yake daukar karya da gaskiya to shi ma za su danganta shi ga Bidi'a)).
Wannan shi ne hanyar Ahlus Sunna. Wanda yake yin amfani da lafazi na Bidi'a to ana danganta shi da Bidi'ar kai tsaye, saboda ya fadi magana ta Bidi'a, ya aikata Bidi'a ta magana.
3- MANHAJIN SAYYID QUTUB SHI NE AMFANI DA LAFUZA "MUJMALAI" DA NA BIDI'A:
To idan an fahimci abin da ya gabata, za mu ga cewa: Sayyid Qutub ya yi amfani da lafuzan da Khawarijawa suke amfani da su, wajen bayanin hakikanin Imani da Muslunci da Addini. Ga misalansu kamar haka:
1) Addini abu ne guda daya dunkule ba ya rarrabuwa:
((حقيقة هذا الدين.. إنه وحدة لا تتجزأ)).
في ظلال القرآن (1/ 164)
Ya ce:
((فالدينونة لله كل لا يتجزأ)).
في ظلال القرآن (4/ 2145)
2) Imani abu ne guda daya ba ya rarrabuwa:
Ya ce:
((إن الإيمان وحدة لا تتجزأ))
في ظلال القرآن (2/ 798)
Ya ce:
((العقيدة التي تؤمن بها.. في وحدة لا تتجزأ ولا تفترق عناصرها..))
في ظلال القرآن (2/ 687)
3) Muslunci abu ne guda daya ba ya rarrabuwa:
Ya ce:
((الإسلام يأخذها كلا لا يتجزأ)).
في ظلال القرآن (6/ 3988)
4) Shari'a abu ne guda daya ba ta rarrabuwa:
Ya ce:
((إن شريعة الله كل لا يتجزأ)).
في ظلال القرآن (2/ 841)
Ya ce:
((يصبح المنهج الإلهي وحدة واحدة. لا تتجزأ ولا تتفرق)).
في ظلال القرآن (1/ 177)
To a nan Sayyid Qutub ya yi amfani da lafuza nau'i biyu:
NAU'I NA FARKO:
Sayyid Qutub ya yi amfani da lafazi "Mujmali", (وحدة واحدة), wannan lafazi ne dunkulalle. Bai zo a Shari'a ba, kuma zai iya daukar ma'ana mai kyau, zai dauki mummunar ma'ana. Mummunar ma'anar da zai dauka shi ne ma'anar da 'Yan Bidi'a suke nufi, cewa: Imani abu ne guda daya a dunkule (الإيمان حقيقة واحدة).
Don haka a nan sai mu ce: me ya sa Sayyid Qutub bai yi amfani da lafazi na Shari'a ba? Idan kuma babu, me ya sa bai yi amfani da lafazi mai ingantaccen ma'ana ba? Misali ya ce:
1. ((الدين شامل))، ((الدين متكامل))، ((الدين جامع))، ((الدين عام))
2. ((الإيمان شامل))، ((الإيمان متكامل))، ((الإيمان جامع))، ((الإيمان عام))
3. ((الإسلام شامل))، ((الإسلام متكامل))، ((الإسلام جامع))، ((الإسلام عام))
4. ((الشريعة شاملة))، ((الشريعة متكاملة))، ((الشريعة جامعة))، ((الشريعة عامة))
NAU'I NA BIYU:
Haka kuma Sayyid Qutub ya yi amfani da lafazin Bidi'a, inda ya yi ta yin amfani da lafazin (لا تتجزأ ولا تتفرق). Wannan lafazin 'Yan Bidi'a ne, Wa'eediyya (Khawarijawa da Mu'utazila), da kuma Murji'a (Jahamiyya da Karramiyya da Asha'ira d.s). Su suka kirkiri lafazin don su tabbatar da Bidi'o'insu a babin Imani. Su Murji'a suka ce: Imani ba ya rarrabuwa, don haka idan aka samu sashensa to gaba daya ya tabbata. Mutum ya zama mai cikakken imani.
Su kuma Khawarijawa suka ce: Imani ba ya rarrabuwa, don haka idan aka rasa sashensa to gaba daya an rasa shi. A kan haka Ibnu Taimiyya ya ce:
((قالت الخوارج والمعتزلة قد علمنا يقينا أن الأعمال من الإيمان فمن تركها فقد ترك بعض الإيمان وإذا زال بعضه زال جميعه؛ لأن الإيمان لا يتبعض ولا يكون في العبد إيمان ونفاق فيكون أصحاب الذنوب مخلدين في النار إذ كان ليس معهم من الإيمان شيء)).
مجموع الفتاوى (13/ 48)
Ka ga sai Ibnu Taimiyya ya yi bayanin ra'ayin Khawarijawa da Mu'utazila, a ciki sai ya nuna cewa hujjar ra'ayinsu ita ce:
((لأن الإيمان لا يتبعض)).
((Saboda Imani ba ya rarrabuwa)).
A wani wajen kuma, yana bayanin cewa: shubuhar Murji'a iri daya ce da ta Khawarijawa sai ya ce:
((وإنما أوقع هؤلاء كلهم ما أوقع الخوارج والمعتزلة في ظنهم أن الإيمان لا يتبعض بل إذا ذهب بعضه ذهب كله ومذهب أهل السنة والجماعة أنه يتبعض وأنه ينقص ولا يزول جميعه كما قال النبي صلى الله عليه وسلم: «يخرج من النار من كان في قلبه مثقال ذرة من الإيمان»))
شرح العقيدة الأصفهانية (ص: 197)
Sai Ibnu Taimiyya ya bayyana cewa; Khawarijawa ma – kamar sauran 'yan bidi'a – duka sun tafi ne a kan cewa; Imani abu daya ne ba ya rarrabuwa, ta yadda idan sashensa ya gushe to gaba daya imanin zai gushe, sai mutum ya fita daga Muslunci.
Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya ce:
((المعتزلة والخوارج قالوا: إن الإيمان قول وعمل لكن لا يتبعض ولا يتجزأ، قالوا: إن ترك المعصية وفعل الطاعة إيمان، فإذا فعل الموحد المعصية، أو ترك الطاعة زال عنه الإيمان بالكلية. ثم الخوارج تكفره، والمعتزلة تجعل له منزلة بين منزلتين. وافقوا أهل السنة في أصل الإيمان أنه قول وعمل، لكن خالفوهم فقالوا: لا يتبعض ولا يتجزأ)).
شرح العقيدة الواسطية (ص: 128)
Shi ya sa Ibnu Taimiyyan yana musu raddi sai ya ce:
((قد ثبت في الصحيح عن النبي صلى الله عليه وسلم {إن الله يخرج من النار من كان في قلبه مثقال دينار من إيمان} وفي رواية: {مثقال دينار من خير ثم يخرج من النار من كان في قلبه مثقال حبة من خردل من إيمان} " وفي رواية " من خير " " {ويخرج من النار من كان في قلبه مثقال ذرة من إيمان أو خير} " وهذا وأمثاله من النصوص المستفيضة عن النبي صلى الله عليه وسلم يدل أنه لا يخلد في النار من معه شيء من الإيمان والخير وإن كان قليلا وأن الإيمان مما يتبعض ويتجزأ)).
مجموع الفتاوى (12/ 491 - 492)
Ka ga sai ya nuna cewa: Akwai nassoshi masu yawa da suke nuni a kan cewa:
((إن الإيمان مما يتبعض ويتجزأ)).
((Imani abu ne da yake rarrabuwa bangare – bangare, yanki - yanki)).
Saboda haka wannan lafazi da Sayyid Qutub ya yi amfani da shi (لا تتجزأ ولا تتفرق) lafazi ne na Bidi'a, don haka dole a danganta shi ga Bidi'a, kamar yadda Ibnu Taimiyya ya fada a maganarsa da ta gabata.
Da wannan za mu tabbatar da cewa; da ma fa asali shi Sayyid Qutub ba a bisa Manhajin Ahlus Sunna yake magana ba, bisa Manhaji ne na Bidi'a. Shi ya sa ya zo ya yi ta magana a game da Addini yadda ya ga dama, alhali shi rubutu a Addini ba rubutu a Adabi ba ne.
Haka su ma masu kare shi, asali ba Manhajin Ahlus Sunnan suka sani ba, shi ya sa suka zo suna ta dikake da kame-kame, -wai- su a dole sai sun yi tawili, sun murda maganar Sayyid Qutub, sun wanke shi daga asalin Akidarsa. To ai hakan ba za ta yiwu ba. Saboda mujarradin yin amfani da lafuzan da ya yi amfani da su, ya yi magana a kan Imani, Addini, Muslunci da Shari'a, lafuza ne na Bidi'a. Kuma an tabbatar da cewa; na bidi'ar Khawarijawa ne. Saboda haka babu wanda zai yi inkarin cewa; Akidar Sayyid Qutub Akida ce ta Khawarijawa sai jahili, wanda bai san Akidar Ahlus Sunna da Manhajinsu ba, kuma bai san Akidun Khawarijawa ba. Ko kuma mai son zuciya, wanda zai yi amfani da tawili ya boye sharrin da ke cikin maganarsa, alhali ba zai yi amfani a nan ba, saboda matsalar ba ta ma'ana ba ce kadai, a'a, ta shafi yin amfani da lafuzan kansu.
4- ABUBUWA DA SUKE TABBATAR DA CEWA: AKIDAR SAYYID QUTUB TA KHAWARIJANCI CE:
Da ma ita Akidar Khawarijawa a aikace take bayyana. Bayan sun kudurce cewa; Imani abu daya ne dunkulalle wanda ba ya rarrabuwa, sai kuma su zartas da wadannan aiyuka masu zuwa a aikace:
(1) KAFIRTA AL'UMMA:
Babban abin da manazarta da Malamai har da jagororin Ikhwan suka zargi Sayyid Qutub da shi shi ne cewa; shi ya haifar da tunanin Kafirta Musulmai a wannan zamani. Saboda shi ya yi ta kafirta al'umma a cikin littatafansa, yana cewa; kowa ya yi ridda, an koma Jahiliyya, yanzu babu al'umma Musulma, kai, babu ma Musulmai. Don haka dole mutane su sake sabon shiga Muslunci.
A baya na kawo maganganunsa a kan haka, da maganganun manazarta da malaman, babu bukatar sai na sake maimaitawa.
(2) FITA DAGA JAMA'A:
Fita daga jama'a da kauracewa al'umma yana daga cikin ginshikan Khawarijanci. A fita daga garin kafirci da jahiliyya a koma garin Muslunci. Ya tabbatar da haka a cikin littatafansa a wurare da yawa, daga ciki ya ce:
((فأما اليوم وقد عادت الأرض إلى الجاهلية وارتفع حكم الله- سبحانه- عن حياة الناس في الأرض، وعادت الحاكمية إلى الطاغوت في الأرض كلها، ودخل الناس في عبادة العباد بعد إذ أخرجهم الإسلام منها.. الآن تبدأ جولة جديدة أخرى للإسلام- كالجولة الأولى- تأخذ- في التنظيم- كل أحكامها المرحلية، حتى تنتهي إلى إقامة دار إسلام وهجرة ثم تمتد ظلال الإسلام مرة أخرى- بإذن الله- فلا تعود هجرة ولكن جهاد وعمل كما حدث في الجولة الأولى..
في ظلال القرآن (3/ 1560)
Ya ce:
((إن الجاهلية جاهلية، والإسلام إسلام. والفارق بينهما بعيد. والسبيل هو الخروج عن الجاهلية بجملتها إلى الإسلام بجملته. هو الانسلاخ من الجاهلية بكل ما فيها والهجرة إلى الإسلام بكل ما فيه.
وأول خطوة في الطريق هي تميز الداعية وشعوره بالانعزال التام عن الجاهلية: تصورا ومنهجا وعملا. الانعزال الذي لا يسمح بالالتقاء في منتصف الطريق. والانفصال الذي يستحيل معه التعاون إلا إذا انتقل أهل الجاهلية من جاهليتهم بكليتهم إلى الإسلام.
لا ترقيع. ولا أنصاف حلول. ولا التقاء في منتصف الطريق.. مهما تزيت الجاهلية بزي الإسلام، أو ادعت هذا العنوان! وتميز هذه الصورة في شعور الداعية هو حجر الأساس. شعوره بأنه شيء آخر غير هؤلاء. لهم دينهم وله دينه، لهم طريقهم وله طريقه. لا يملك أن يسايرهم خطوة واحدة في طريقهم. ووظيفته أن يسيرهم في طريقه هو، بلا مداهنة ولا نزول عن قليل من دينه أو كثير! وإلا فهي البراءة الكاملة، والمفاصلة التامة، والحسم الصريح.. «لَكُمْ دِينُكُمْ وَلِيَ دِينِ» ..
وما أحوج الداعين إلى الإسلام اليوم إلى هذه البراءة وهذه المفاصلة وهذا الحسم.. ما أحوجهم إلى الشعور بأنهم ينشئون الإسلام من جديد في بيئة جاهلية منحرفة، وفي أناس سبق لهم أن عرفوا العقيدة، ثم طال عليهم الأمد «فَقَسَتْ قُلُوبُهُمْ وَكَثِيرٌ مِنْهُمْ فاسِقُونَ» .. وأنه ليس هناك أنصاف حلول، ولا التقاء في منتصف الطريق، ولا إصلاح عيوب، ولا ترقيع مناهج.. إنما هي الدعوة إلى الإسلام كالدعوة إليه أول ما كان، الدعوة بين الجاهلية. والتميز الكامل عن الجاهلية.. «لَكُمْ دِينُكُمْ وَلِيَ دِينِ» .. وهذا هو ديني: التوحيد الخالص الذي يتلقى تصوراته وقيمه، وعقيدته وشريعته.. كلها من الله.. دون شريك.. كلها.. في كل نواحي الحياة والسلوك.
وبغير هذه المفاصلة. سيبقى الغبش وتبقى المداهنة ويبقى اللبس ويبقى الترقيع.. والدعوة إلى الإسلام لا تقوم على هذه الأسس المدخولة الواهنة الضعيفة. إنها لا تقوم إلا على الحسم والصراحة والشجاعة والوضوح..
وهذا هو طريق الدعوة الأول: «لَكُمْ دِينُكُمْ وَلِيَ دِينِ» ..)).
في ظلال القرآن (6/ 3992 – 3993)
(3) DAUKAR MAKAMI A KAN AL'UMMA SUNA KASHE MUSULMAI:
Wannan shi ne babbar sifar Khawarijawa wacce Annabi (saw) ya fade ta a Hadisi:
((يقتلون أهل الإسلام ويدعون أهل الأوثان)).
To wannan ne wanda Sayyid bai yi ba. Alhamdu lillahi, saboda don an kama shi, an kulle shi a kurkuku, har daga karshe aka kashe shi. Amma matasan da suka tasirantu da Fikrorinsa su sun dauki makami sun kashe Musulmai. An samu kungiyoyi da yawa a sassan Duniya, har mu ma a Nigeria aka samu Boko Haram.
Da ma Sayyid din ya nuna cewa: ko ya mutu Fikrorinsa ba za su mutu ba, za su wanzu a cikin tunanin mutane, suna aiki da su, zai zama kamar yana raye. Wannan ya sa wani masoyinsa ya rubuta littafi mai suna:
سيد قطب الشهيد الحي – الدكتور صلاح الخالدي.
Ma'ana: Rayayyen Shahidi. Ya mutu amma kamar yana raye, saboda Fikrorinsa suna nan suna tasiri a kan matasa, kuma suna aiki da su, suna kashe Musulmai da sunan Jihadi, saboda sun bar "Hakimiyya". Daga cikin wadanda suka tabbatar da haka akwai Abdallah Azzam, kamar yadda a can baya na yi posting na maganarsa. Da sauransu suna nan da yawa.
5- Na bibiyi rubutun masu "I'itiradhi" daga cikinsu har da wanda nake yi masa raddi, amma abin mamaki sai na ga kwata – kwata ba su ma fahimci inda ni na dosa ba.
Abin da su ba su sani ba shi ne; Magana a kan wannar mas'ala ba magana ce ta ma'ana kadai ba, balle har su tuhume ni da Tadlisi da Talbisi da sauran maganganunsu. A'a, farko magana ce ta LAFAZI. Shi Sayyid Qutub - saboda bai san Manhajin Ahlus Sunna ba - ya zo ya yi ta yin magana da lafuza "Mujmalai" da kuma lafuza na Bidi'a, wajen bayanin "haqa'iq" na Addini. Ya yi magana a kan Addini da irin yaren da ya saba yin rubutu a jaridu da rubutun Adabin Larabci da yake yi, alhali shi Addini ba a masa haka.
Saboda haka ba magana ake yi ta Siyaki ba. A'a, magana ce ta Sayyid ya yi amfani da lafazi "Mujmali" (وحدة), kuma ya yi amfani da lafazin Bidi'a, a inda 'yan Bidi'an suke amfani da shi, wato lafazin (لا يتجزأ ولا يتفرق), wajen bayyana hakikanin Imani. To a nan akwai abubuwa guda biyu:
Na farko: amfani da lafuzan kansu Bidi'a ne.
Na biyu: Duk wanda ya yi amfani da lafazin (لا يتجزأ ولا يتفرق) wajen bayanin hakikanin Imani, kamar yadda Sayyid ya ce:
((إن الإيمان وحدة لا تتجزأ))
في ظلال القرآن (2/ 798)
To dole a jingina shi ga 'Yan Bidi'a a Babin Hakikanin Imani. Sai a duba a gani, a bangaren Murji'a yake ko kuma Khawarijawa da Mu'utazila?
To da muka duba sai muka ga Sayyid Qutub a bangaren Khawarijawa yake, saboda ya nuna cewa: dole ne mutum ya bi Muslunci a dunkulensa, idan ya bi hukunci daya wanda ba na Muslunci ba to ya bar Musluncin, ko da kuwa yana girmama Akida yana cewa: shi Musulmi ne.
Da a ce: Sayyid ba Akidar Khawarijanci yake tabbatarwa ba, da sai ya yi amfani da lafuza masu ma'ana mai kyau, wadanda ba za su nuna Akidar Khawarijanci ba. Kamar ya ce:
((الإيمان شامل))، أو ((الإيمان متكامل))، أو ((الإيمان جامع)) ونحو ذلك.
Amma sai ya karfafa maganarsa da lafazin 'Yan Bidi'a ya ce:
((لا يتجزأ)) ((ولا تتفرق)).
Saboda haka babu wanda ya isa ya wanke Sayyid Qutub daga Akidar Khawarijawa, saboda abin da ya rubuta kenan a cikin littafinsa.
Shi ya sa a baya na kawo maganar Ibnu Taimiyya inda ya ce:
((ومن تكلم بما فيه معنى باطل يخالف الكتاب والسنة ردوا عليه، ومن تكلم بلفظ مبتدع يحتمل حقا وباطلا نسبوه إلى البدعة أيضا)).
درء تعارض العقل والنقل (1/ 254)
((Duk wanda ya yi magana da lafazin da akwai mummunar ma'ana a cikinsa wacce ta saba Alkur'ani da Sunna Salaf suna jefa masa kayansa, haka wanda ya yi magana da lafazin Bidi'a ma, wanda yake dauke da karya da gaskiya, suna JINGINA SHI GA BIDI'A)).
Shi kuma Sayyid Qutub lafuzan da ya yi amfani da su, sun saba ma Alkur'ani da Sunna, saboda Nassoshin Alkur'ani da Sunna sun tabbatar mana cewa; Imani sassa ne daban daban, yana rarrabuwa. Idan sashen ya tafi sauran sashen yana nan bai gushe ba. Annabi (saw) ya ce:
«الإيمان بضع وستون شعبة، والحياء شعبة من الإيمان» وفي رواية: «بضع وسبعون شعبة».
صحيح البخاري (1/ 11) صحيح مسلم (1/ 63)
((Imani rassa sittin da wani abu ne, - ko saba'in da wani abu – kunya reshe ne na imani)).
Kuma Hadisin Jibreel (as) ya tabbatar mana cewa; Addini martabobi uku ne, don haka yana rarrabuwa.
To a hakan ne wani masani Adabin Larabci zai zo ya ce mana Addini: ((وحدة لا تتجزأ)), (Imani abu ne guda daya a dunkule ba ya rarrabuwa), kuma a kyale shi?!
Haba, a ina aka taba yin haka. In haka ne kowane Dan Bidi'a a tsawon Tarihi sai ku zo ku yi tawilin maganganunsu, ku kare su!
Amma su masu kare shi ido rufe, wadanda a dole sai sun wanke mai laifi, matsalarsu ita ce; sun tsoma baki ne a abin ba su da ilimi a kansa. Shi ya sa mai raddi ya zo ya yi dogon rubutu, amma maras ma'ana, saboda bai san abin da ake magana a kansa ba.
A takaice, Sayyid Qutub dan bidi'a ne, mai Akida ta Khawarijawa, saboda dalilan da muka ambata a baya.
✍️ *Dr Aliyu Muh'd Sani (H)*
*31 October, 2021*