SHAWARI GA GOMNATI KAN YAK'AR TUNANIN TA'ADDANCI
A cikin wadannan shekaru kasarmu tana fama da Ta'addancin Khawarijawa da tarzomar Rafidha 'Yan Shi'a, to lallai ya kamata a san cewa; irin wadannan fitinu magance su gaba daya yana da matukar wahala, sai dai a yi kokarin galaba a kansu, da rage illa da hatsarinsu.
Misali abin da ya shafi Ta'addancin Khawarijawa, - kamar Boko Haram -, ba za su gushe suna bayyana ba har karshen Duniya, kamar yadda ya zo a Hadisi:
لا يزالون يخرجون
مسند أحمد ط الرسالة (33/ 44)
"Ba za su gushe suna fitowa ba".
Sai dai duk lokacin da suka fito a datse su, amma hakan ba zai hana sake bayyanarsu a gaba ba. Annabi (s.a.w) ya ce:
"كلما خرج قرن قطع أكثر من عشرين مرة- "حتى يخرج في عراضهم الدجال".
سنن ابن ماجه ت الأرنؤوط (1/ 120)
"Duk lokacin da kahonsu ya fito sai a yanke shi sau fiye da ishirin", - "Har sai Dajjal ya fito a bangarensu".
Don haka daga cikin hanyoyi na kokarin yakar fitinar 'Yan Ta'adda da kuma 'Yan Tarzoma, akwai hanyoyi kamar haka da muke ba da shawara ga Gomnati ta yi aiki da su:
1- Ya kamata Gomnati da al'umma su ba da goyon baya wa Malamai masu karantar da al'umma kyakkyawar Aqida, da kuma bayyana illar munanan Aqidu. Su kuma sai su yi amfani da kwarewa da ilimi da hikima suna koyar da mutane, suna fadakar da su da tsoratar da su munin Aqidun, musamman Aqidu masu kai wa ga Ta'addanci da Tarzoma.
2- Hukuma da jami'an tsaro su bi dabaru na kwantar da tarzoma ba tare da ta rikede ta zama babbar fitina ta koma ta'addanci ba. Lallai muna kyautata zaton da ma jami'an tsaro suna da dabarun kwantar da tarzoma ba tare da ta bunkasa ta haifar da kungiyar ta'addanci ba.
3- Daga cikin hanyoyi masu matukar amfani da ya kamata Gomnati tana bi wajen yakar tunanin ta'addanci da miyagun Aqidu, duka wadanda aka kama aka sanya a kurkuku, to a samu Malamai kwararru, masu ilimi da kwarewa da hikima suna zuwa suna tattaunawa da su, suna yaye musu shubuhohin da suka kai su ga wadannan munanan Aqidu da tunani. Saboda ita shubuha da ra'ayi da Aqida ba a yakarta da karfi sai da ilimi da hujja da bayani.
Wannar babbar hanya ce da kasashe masu yaki da ta'addanci suke amfani da ita -musamman a kasar Saudiyya-, kuma ana cin nasarar raba 'Yan Ta'addan da tunanin ta'addanci da iznin Allah.
A takaice dai, ta'addanci kalubale ne ga al'umma gaba daya, sai kowa ya ba da tasa gudumawa wajen yakar tunanin ta'addanci.
Allah ya yi mana tsari da fitina, ya ba mu zaman lafiya.