Subscribe Our Channel

 ABU RAYYAH YA BAYYANA A NIGERIA


An yi wani Munafuki a Misra, mai suna Mahmud Abu Rayyah, wanda yake ikirarin bincike da nazari da aiki da hankali a lamuran Addini. Wanda ta wannar hanya ya yi ta kai farmaki kan Sunnar Manzon Allah (saw), inda ya fara hakan a littafinsa mai suna:

أضواءٌ على السنّةِ المُحمّديّةِ


A cikin wannan littafin ya isa ga cewa; ba za a yi aiki da Hadisan Annabi (saw) ba. Kuma ya dira kan Sahabban Annabi (saw), yana zaginsu daya bayan daya, musamman wadanda suka fi ruwaito Hadisan Annabi (saw). Wanda har ya isa kan Sahabi Abu Huraira (ra), ya dira a kansa, saboda shi ya fi sauran Sahabbai riwaya daga Annabi (saw), don in ya zubar da kimarsa to ya rushe kaso mai yawan gaske na Sunnar Annabi (saw).


Abu Rayya ya dira a kan Sahabi Abu Huraira (ra), ya ci masa mutunci, ya fadi maganganu na batanci a kansa wanda hatta Rafidha 'Yan Shi'a ba su fada a kansa ba - duk da cewa; ya dogara sosai a kan Littafin wani Rafidhiy Dan Shi'a mai suna Abdulhussain Sharafuddeen, mai littafin "Al-Muraja'at"-. Karshe ya tuheme shi da karya, da kirkiran Hadisai. Kai, musamman ya rubuta littafi a kan Sahabi Abu Huraira (ra) yana ci masa zarafi:

أبو هريرة شيخ المضيرة


A daidai lokacin da yake cin mutuncin Sahabi Abu Huraira (ra), a lokacin ne kuma yake girmma kafirai, yake cewa; Yahudawa da Nasara za su shiga Aljanna, ya tabbatar da haka a cikin littafinsa mai suna:

دين الله واحد علی ألسنة الرّسل


To amma duk da hargowa da hayagaga da ya yi ta yi, don karyata Sunna da zagin Sahabbai da ci musu mutunci, haka Tarihi ya yi wurgi da shi cikin bolarsa, bayan ya yi mutuwar wulakanci, ya mutu yana ihu. Aka manta da su shi da littatafan nasa, amma Hadisan Sahabi Abu Huraira (ra) kuwa har gobe ana karanta su, Musulmai suna aiki da su, a dukkan lamuran Addini da rayuwarsu, a kullum ana ta addu'ar neman yarda ga Sahabi Abu Huraira (ra).


To kamar wannan Munafuki, a yanzu haka an samu wani mutum a Kano, yana nan yana bin irin wannan salo na Abu Rayyah, yana karyata Hadisai, ya zagin Sahabbai, yana tuhumarsu da karya da kirkiran Hadisai. Yanzu haka ya dira a kan Sahabi Anas bn Malik (ra), yana zaginsa da ci masa mutunc, -wai- shi ma yana so ya rushe Sunnar Annabi ta irin hanyar da Abu Rayyah ya bi, saboda Anas (ra) yana cikin masu yawan Hadisai daga Annabi (saw).


Amma shi wannan mutumi, ya hada da bin wata hanya ta Mulhidai, masu cin zarafin Annabi (saw). Ta yadda yake daukan Hadisan da suka shafi mu'amalar Annabi (saw) da mata yana fassara su fassara ta batsa, yana nuna Annabi (saw) a matsayin mai lalata da mata. Alhali duk cikin Musulmai, tun farkon al'umma har yau, babu wanda ya taba fahimtar hakan daga Hadisan sai shi da sauran Munafukai masu sukar Manzon Allah (saw) da yakar Sunnarsa.


To ala ayyi halin, wannan abin da yake yi aikin banza ne kawai. Kafin ya yi an samu daruruwa sun yi, tun daga kan Munafukai har zuwa cikin "Mustashriqun" (Orientalists) da Kafirai da Mulhidai, amma hakan babu abin da ya canza, al'umma ba su dena karanta Hadisan Abu Hurara (ra) da Anas bn Malik (ra) ba, ba su dena aiki da su ba, kuma a kullum aka kira sunayensu sai sun yi musu addu'ar neman yarda a wajen Allah an ce:

رضيَ اللهُ عنهُ

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter