TSAKANIN MAULIDI DA MUSABAKAR ALKUR'ANI
A kullum in mun ce Maulidi bidi'a ne, sai ka ji wani ya ce; ai ku ma kuna Musabakar karatun Alkur'ani, ai shi ma bidi'a ne.
Alhali duk wanda yake da ido a karatun Fiqhu ya san Musabaka tana da asali, Malaman Fiqhu suna kulla babi ko fasali a kan hukuncin Musabaka a cikin babin Jihadi ko bayansa, ko babin "Ju'uli", ko wani wajen daban.
Duka Malaman Fiqhu sun yi ittifaqi a kan halascin Musabaka, bisa dalilan Alkur'ani da Sunna da Ijma'i.
Sai dai sun yi sabani a kan mas'aloli guda biyu:
1- Yin musabaka a kan abin da bai shafi Jihadi ba.
2- Sanya kyauta a Musabakar abin da ba doki ko rakumi ko harbi ba.
Saboda haka wasu Malaman ba su ambaci Musabaka a fannonin ilimi cikin fagagen Musabakar ba, amma wasu kuma sun sanya Musabaka a fannin ilimi cikin fagagen Musabakar da ta halasta, saboda dalilai kamar haka:
1- Hadisin Ibnu Umar (ra) ya ce:
قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «إن من الشجر شجرة لا يسقط ورقها، وإنها مثل المسلم، فحدثوني ما هي» فوقع الناس في شجر البوادي قال عبد الله: ووقع في نفسي أنها النخلة، فاستحييت، ثم قالوا: حدثنا ما هي يا رسول الله قال: «هي النخلة»
صحيح البخاري (1/ 22) صحيح مسلم (4/ 2164)
Annabi (saw) ya ce:
"A cikin bishiyoyi akwai bishiyar da ganyenta ba ya zubewa, misalinta kamar Musulmi Mumini ne. KU GAYA MINI, WACE BISHIYA CE?".
Sai mutane suna ta ambaton sunayen bishiyoyi daban-daban. Sai Ibnu Umar ya ce: Na ji a raina ita ce bishiyar dabino, amma sai na ji kunyan ba da amsa.
Sai Sahabbai suka ce: mun ba ka gari ya Manzon Allah.
Sai ya ce: "Ita ce bishiyar dabino".
2- Hadisin Gasa da Sayyidina Abubakar (ra) ya yi da Mushrikai a kan yakin Rum da Farisa, wanda Allah ya saukar da:
{الم (1) غُلِبَتِ الرُّومُ (2)} [الروم: 1، 2]
3- Ba a yi hani a kai ba, don haka yana nan a kan asali na halasci, tun da babin Mu'amala ne ba babin Ibada ba.
(البراءة الأصلية)
4- Qiyasin Musabaka a fannin ilimi a kan Musabaka na dawaki da rakuma, saboda duka sun yi tarayya cikin illar daukaka Addinin Allah. Kamar yadda ake daukaka Addini a kare shi da Jihadi, haka ake daukaka shi a kare shi da Ilimi, don haka ya halasta a yi Musabaka a ilimin Addini, kamar yadda ya halasta a yi Musabaka a kayan yaki saboda shirin Jihadi. Saboda ka'idar nan ta Usul kamar haka:
كل حكم شرعي أمكن تعليله فالقياس جار فيه
المستصفى (ص: 329)
Wannan ya sa Malaman Hanafiyya suka Nassanta halascin yin Musabaka a ilimi da Qiyasinsa a kan na dawaki da rakuma.
Al-Baldajiy a sharhin littafinsa ya ce:
"قال: (وعلى هذا التفصيل إذا اختلف فقيهان في مسألة وأرادا الرجوع إلى شيخ وجعلا على ذلك جعلا) لأنه لما جاز في الأفراس لمعنى يرجع إلى الجهاد يجوز هنا للحث على الجهد في طلب العلم، لأن الدين يقوم بالعلم كما يقوم بالجهاد".
الاختيار لتعليل المختار (4/ 169)، تبيين الحقائق شرح كنز الدقائق وحاشية الشلبي (6/ 32)
A nan sai ya yi Qiyasin Musabaka a ilimin Addini a kan Musabaka da dawaki da rakuma, saboda sun hadu cikin illar daukaka Addinin Allah da kare shi.
Haka cikin Malaman Malikiyya Al-Haddab ya yi ishara ga haka inda ya ce:
"لكن لما كانت هذه الأشياء مما يستعان بها على الجهاد في سبيل الله الذي هو طريق إلى إظهار دين الله ونصرته جاز لما فيه من منفعة الدين وما يؤدي إلى عبادة، أو يستعان به في عبادة فهو عبادة".
مواهب الجليل في شرح مختصر خليل (3/ 390)
Saboda haka Musabaka a ilimin Addinin ya halasta, sawa'un bangaren Alkur'ani ne ko Hadisi ko Fiqhu.
Saboda haka Maulidi ba dadai yake da Musabaka ba.
Maulidi a babin Ibada yake, don haka dole sai da Aya ko Hadisi kafin a yi shi, ba a Qiyasi a babin Ibada.
Sabanin Musabaka, ita kuma Mu'amala ce, matsayinta shi ne halasci. In kana so ka yi, in ba ka so ka bari. Kuma za a iya fitar da hukuncinta daga Qiyasi.
Wannan ya sa har yau ba za ka taba samun babin Maulidi a littatafan Fiqhu ba, amma za ka samu babin Musabaka.
Don haka kalubalantar maganar Maulidi da maganar Musabaka shubuha ce ba hujja ba, duk mai ilimi ya san hanyar rago daban, hanyar kare daban.
Don haka Musabaka halas ce, Maulidi Haram ne, saboda bidi'a ne.