Subscribe Our Channel

Ko Kunsan Masu Satar Account Din Facebook??

Ko kun san masu kwace muku facebook account su canja suna da hoton turawa da location lambar wayarka ce babbar makamin da suke amfani wajen wannan aikin?

Duk wadanda wannan batun ya rutsa dasu lambarsu ce password ita suke dauka sai suyi login salum alum abinsu.

Idan ka bude fb da lamba to kayi hiding dinta ya zama kai kadai ne zaka iya ganinta sannan kada ka saka lambarka a matsayin password.

Ina baka shawarar sanyawa account dinka email kuma sama da guda daya sannan suma kayi hiding dinsu.

Sannan ku lura yanzu suna amfani da yaren Hausa shawara anan in baka san mutum ba kada kayi hurda dashi a wannan kafa.

Akwai kuma hanyar da suke kwata ta hanyar yi maka kofar rago ta link gobe idan Allah ya kaimu zanyi bayaninta.

#BasheerSharfadi Sharfadi.com

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter