Subscribe Our Channel

MENENE BANBANCIN 'YAN IZALA DA 'YAN SALAFIYYA?

TAMBAYA:
"Shin Izala qungiyace... mene banbancin ixala da salafiyya.. sannan menene matsayin qungiya a musulunci".

AMSA:
Farko ita kalmar "KUNGIYA" ba ta da wata matsala, saboda fassara ce ta kalmomi da lafuza da suka zo a nassoshin Shari'a, wasu sun zo a muhallin yabo, wasu kuma a muhallin zargi. Don haka duk jama'ar da suka dace da Kalmar a muhalli mai kyau to babu laifi, kuma su abin yabo ne, wadanda kuma suka dace da Kalmar a muhalli na zargi to su masu laifi ne, kuma sun zama abin zargi a Shari'a. Ga nan kalmomin kamar haka:
جماعة – فرقة – أمة – حزب – طائفة
Da sauransu.

Sa'annan ma'aunin tabbatar da Kalmar "Kungiya" ga wasu jama'a shi ne; dacewa da ma'anar Kalmar a Shari'a ko kuma a Luga, su ake gabatarwa a kan ma'anar kalmar a bisa al'ada (Urfi). Don haka kuskure ne ace; ba za a kira jama'a ko wata tafiya da sunan Kungiya ba, -wai- don ba ta nada Shugaba da Sakatare da P.R.O ba, alhali sunan "Kungiya" ya dace da jama'ar a Shari'a ko kuma a Luga.

DON HAKA, MATUKAR AN SAMU JAMA'A DA SUKA HADU A KAN WATA MANUFA KO RA'AYI, KUMA SUKE TAFIYA A KANTA, SUKE SOYAYYA SABODA ITA, TO SUN ZAMA KUNGIYA, SAWA'UN SUNA TARE A WURI GUDA KO KUMA A'A. KO SUN NADA SHUGABA DA SAKATARE DA MA'AJI DA P.R.O KO KUMA A'A, KO KUMA SUNA TARUWA SU YI MEETING DA WASU TARUKA KO KUMA A'A, SUN SANYA SUNA KO KUMA A'A, SUN YI RIJISTA KO KUMA A'A.

Saboda haka, lallai Allah ya kaddara cewa; wannar al'umma ta Annabi (saw) za ta rarrabu kashi 73, a cikinsu Kungiya daya ce kawai mai tsira daga wuta, su ne wadanda suke bin Addini a bisa tafarkin Annabi (saw) da Sahabbansa.

Saboda haka, duk wanda yake kan Aqidar Ahlus Sunna, na Imani da Allah da Mala'ikunsa, da Littatafansa da Manzanninsa da Ranar Karshe, da kuma Imani da Qaddara. Da kuma babin Mas'alolin Imani, da Matsayin Sahabbai, da kuma babin Shugabanci to shi yana cikin Kungiyar nan guda daya da za ta tsira daga wuta, wato "Al- Firqatun Najiya".

Kuma ita wannar Kungiya ita ake kira "Ahlus Sunnati wal Jama'a", "Firqatun Najiya", "Da'ifatun Mansura", su ne "Ahlul Hadeesi wal Athar", kuma su ake yi wa lakabi da "Salafiyyun", ma'ana masu bin tafarkin Salaf; Sahabban Annabi (saw) da Tabi'ai da Tabi'ut Tabi'ina.

Don haka, duk wanda ya dauki Qur'ani da Sunna da Ijma'in Salaf a matsayin su ne kawai cibiyar daukar Addininsa, to ya rabu da dukkan Kungiyoyin Bidi'a masu daukar Addini daga hankali, mafarkai, Shehunnai, da Imamai d.s.

Haka kuma in ya yi imani da Allah, to ya rabu da hanyar Mushrikai masu shirka a Uluhiyyar Allah, kuma ya rabu da hanyar "Mu'attila" masu kore siffofin Allah, ko "Mu'awwila" masu tawilinsu, ko "Mushabbiha" masu kamanta Siffofin Allah da na halittarsa. Ma'ana; ya rabu da tafarkin "Quburiyyun" masu bautar Kabari, da kuma Jahamiyya da Mu'utazila da Asha'ira da Maturidiyya; masu kore Siffofin Allah ko tawilinsu, da sauran wadanda suka bata a wannan babi.

Haka babin Imani da Mala'iku, da kuma Imani da Littatafai, da kuma Imani da Manzanni, da Imani da Ranar Lahira. Duk wanda ya kasance a kan bin Sunna a bisa tafarkin Salaf a wadannan babuka, to ya rabu da wadanda suka bata a cikinsu, kamar Jahamiyya da Mu'utazila da Asha'ira a babin Qur'ani, da kuma Maganar Allah, da kuma Sufaye da Rafidha ('Yan Shi'a) a babin Annabawa da Manzanni.

Haka bin tafarkin Salaf a babin Qaddara, zai raba mutum da tafarkin Qadariyya masu kore Qaddara, wato Mu'utazila, da kuma Jabariyya masu guluwwi a tabbatar da Qaddara, wato Jahamiyya da Asha'ira da Sufaye.

Haka bin tafarkin Salaf a babin mas'alolin Imani zai raba mutum da tafarkin masu kafirta mutane da Zunubai, kamar Khawarijawa da Mu'utazila (a hukunci), a daya hanun kuma Murji'ah masu fitar da aiki daga cikin Imani; wato Jahamiyya, Asha'ira, Maturidiyya, Murji'atul Fuqaha'i.

Haka bin tafarkin Salaf a babin Sahabbai zai raba mutum da tafarkin Rafidha masu kafirta Sahabbai, da Nasibawa masu jafa'i wa Ahlul baiti.

Haka bin tafarkin Salaf a babin Da'a ma shugabanni, zai raba mutum da tafarkin masu tawaye wa shugabanni, wato Khawarijawa da sauran masu Khuruji ma shugabanni, kamar Mu'utazila da Shi'a da duk wanda ya dace da su.

Don haka, duk wanda ya bi tafarkin Salaf a wadannan babuka na Addini, ya nisanci tafarkin 'Yan Bidi'a, to shi Ahlus Sunna ne, za a kira shi da dukkan sunaye na Ahlus Sunna da muka ambata, kamar "Ahlus Sunnati wal Jama'a", "Firqatun Najiya", "Da'ifatun Mansura", "Ahlul Hadeesi wal Athar",  "Salafiyyun".

SABODA HAKA, IN 'YAN IZALA SUNA KAN WANNAR AQIDA TO SU MA 'YAN SALAFIYYA NE, IN KUMA A KAN AQIDAR JAHAMIYYA KO MU'UTAZILA, KO ASHA'IRA, KO SUFAYE, KO KHAWARIJAWA KO SHI'A SUKE TO SAI MU JI.

DON HAKA, MA'AUNIN BANBANCE 'YAN SALAFIYYA DAGA WASUNSU SHI NE BIN "AQIDAR SALAF" KAWAI; AQIDAR "AHLUS SUNNATI WAL JAMA'A" BA RASHIN BIN MAZHABAR FIQHU BA, KO RABUWA DA KUNGIYA BA.
DON HAKA DUK WANDA YAKE KAN AQIDAR SALAF TO SHI DAN SALAFIYYA NE, KO DA KUWA YANA BIN WATA MAZHABA TA FIQHU, KO YANA CIKIN KUNGIYA. SABODA DA YAWA SUN DAUKA BIN SALAFIYYA SHI NE BARRANTA DAGA KOWACE MAZHABA DAGA CIKIN MAZHABOBIN FIQHU, DA RASHIN TAQLIDI, DA KUMA FITA DAGA KUNGIYA.

Bayan haka, za ka iya samun mutane dukansu Ahlus Sunna ne, amma kuma sun rarrabu Kungiya – kungiya, jama'a – jama'a, gida – gida, kashi – kashi, alhali kuma duka a kan Aqidar Ahlus Sunna suke, to irin wannan rarrabuwa Allah ya yi hani a kansa. Abin da ya wajaba a kanmu shi ne duka Ahlus Sunna su hada kai su zama jama'a guda daya, kungiya daya, babu rarrabuwa, babu ta'assubanci.

Saboda haka sai mu duba mu ga yadda muke a Nigeria; Izala A, Izala B, 'Yan Salafiyya, 'Yan Salafiyyun, 'Yan Ba kungiya, alhali duka Aqidarsu daya.

TO IRIN WANNAN RARRABUWA SHI NE ABIN ZARGI, KUMA SHI NE "TAHAZZUB" DA ALLAH YA YI HANI A KANSA.

Amma da za su dunkule su zama Kungiya guda daya kawai, a matsayin kishiyar Kungiyoyin Bidi'a; Qadiriyya, Tijjaniya, Shi'a, Boko Haram d.s, to don an kirasu da sunan KUNGIYA babu laifi, saboda KUNGIYA a nan abin yabo ne ba abin zargi ba. Saboda mun san cewa; Kungiyar da take kan Sunna bisa tafarkin Sahabbai (Salaf), su ne wadanda suka saba ma 'Yan bidi'a, kuma su ne:
الفرقة الناجية
Fassararsa: KUNGIYA MAI TSIRA DAGA WUTA.

To ka ga kenan, akwai lokacin da sunan Kungiya yake zama abin zargi, wato in ya zama AHLUS SUNNA SUN RARRABU ZUWA KUNGIYOYI DABAN – DABAN, SUNA TA'ASSUBANCI WA MALAMANSU DA KUNGIYOYINSU. TO WANNAN SHI NE "TAHAZZUB" (KUNGIYANCI ABIN ZARGI).

AMMA IN DUKA SUKA ZAMO A BISA TAFARKI GUDA DAYA NA BIN SUNNA BISA TAFARKIN SAHABBAI (SALAF), BA SU RARRABA KANSU BA, SUNA TAFIYA TARE A MATSAYIN JAMA'A GUDA DAYA, KUNGIYA GUDA DAYA, TO WANNAN BABU LAIFI. KAI, SHI NE MA ABIN DA ALLAH YA WAJABTA MANA.

WALLAHU A'ALAM.

AYI HAKURI NA TSAWAITA.

Naku Aliyu Muh'd Sani
24/4/2016
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter