Subscribe Our Channel

Tushen Aqidun Sufaye

Manazarta Aqidun Addinai da Kungiyoyi sun tabbatar da tasirantuwar Sufanci da munanan Aqidu na kafirci da ilhadi daga Addinai daban-daban, kamar Kirastanci, Addinin Hindu, Buda da kuma Falsafar Girkawa.

Aqidar Hululi (Allah ya shiga cikin halitta) tana daga cikin mafi munin Aqidun Sufaye, wacce ta shahara daga Hallaju. Asali wannar Aqida ce ta Kiristoci.

Aqidar Ittihadi (hadewar Allah a halitta) ita ma Aqida ce ta Kiristoci, wacce ta shahara a hanun su Ibnu Arabiy, Ibnu Saba'en da Ibnul Faridh da sauransu cikin Sufaye 'Yan Falsafa, su suka dauki alhakin shigar da wannar Aqida cikin Sufanci da kuma yada ta.

Banbancin da ke tsakanin Sufaye da Kiristoci a cikin wadannan Aqidu guda biyu, su Kiristoci sun takaita "Hululi" da "Ittihadi" ne ga Annabi Isa (as) kawai, a lokacin da su kuma Sufaye suka game "Hululi" da "Ittihadin" ga halitta gaba daya. Ma'ana; Allah yana shiga cikin komai, kuma yana hadewa da dukkan halitta, komai ya zama Allah, abin da ya kai su ga Aqidar "Wahdatul Wujudi" (komai Allah ne).

Abdulkareem Al-jiliy, jikan Abdulkadir Jilaniy yana yabon Kiristoci a kan Aqdarsu ta "Hululi" da "Ittihadi" sai ya ce:
"وأما النصارى فإنهم أقرب من جميع الأمم الماضية إلى الحق تعالى، فهم دون المحمديين، سببه أنهم طلبوا الله تعالى فعبدوه في عيسى ومريم وروح القدس، ثم قالوا بعدم التجزئة، ثم قالوا بمقدمه على وجوده في محدث عيسى وكل هذا تنزيه في تشبيه لائق بالجناب الإلهي".
الإنسان الكامل لعبد الكريم الجيلي (ص: 127)

Yana nufin wannar Aqida ta Kiristoci ta kamanta Allah da halitta, da bauta ma Alloli uku (Trinity) hakan dadai ne, amma duk da haka sun gaza saboda sun takaita abin cikin Alloli uku kawai, alhali ba zai yiwu a takaice Allah cikin uku kawai ba, a'a, komai ma Allah ne.

Haka kuma wannar Tarbiyya da Sufaye suke yi, a kulle mutum a daki yana wasu wuridai, a hana shi ci da sha sai dan abin da zai sa ya rayu, har sai ya yi "Wusuli" ya yi "Fana'i", wato sai shi kansa ya kare a cikin zatin Allah, ya samu "Wahdatush Shuhudi", ya zama yana ganin komai a cikin zatin Allah, komai ya zama abu daya ya zama Allah.
Ita ma wannar Tarbiyya asalinta daga Kiristanci ne, Limaman Coci ne suke yin haka wa mabiyansu.

A da ne ake kasa Sufanci kashi-kashi; 'Yan Zuhudu, 'Yan Ibada, Faqirai da 'Yan Hakika, amma daga karshe gaba daya sun zama abu daya, tun da su Ibnu Arabiy suka jagula Sufancin har ya zama iri daya. Wato Sufancin da ya kunshi "Wahdatul Wujudi" da Aqidar "Hakika".

Da ma haka lamarin yake, farko Bidi'a daga karamar da'ira take farawa, sai ta yi ta fadi tana girma har ta kunshi Aqidu na kafirci da ilhadi. Wannan yake nuna hatsarin Bidi'a komai kankantarta.

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter