Abokinku ya ce:
من السلفي؟
السلفي من كان على عقيدة السلف؛ أهل السنة والجماعة.
قال الإمام الذهبي:
"السلفي -بفتحتين- وهو من كان على مذهب السلف".
سير أعلام النبلاء (21/ 6)
فمن وافق السلف في مصدر التلقي ومنهج الاستدلال وفي أصول السنة، وخالف المبتدعة في ذلك فهو سلفي، سواء انتسب إلى مشايخ معينين، أو طائفة معينة التى تعرف بـ "السلفيين" أو لم ينتسب.
ومصدر التلقي هو الكتاب والسنة وإجماع السلف.
قال شيخ الإسلام:
"فمن قال بالكتاب والسنة والإجماع كان من أهل السنة والجماعة".
مجموع الفتاوى (3/ 346)
وأصول السنة هي أصول الإيمان الستة وما ألحق بها، وهي الإيمان بالله وملائكته وكتبه ورسله واليوم الآخر، والإيمان بالقدر خيره وشره.
ويلحق بها مسائل الإيمان (باب الأسماء والأحكام)، ومنزلة الصحابة، ومسألة الإمامة وطاعة ولاة الأمور، والولاء والبراء، والاعتصام بالسنة والجماعة واجتناب البدع في الدين والتفرق.
فمن وافق الكتاب والسنة وأئمة السلف في هذه الأبواب فهو سلفي على الجادة، وإن لم ينتسب إلى مشايخ معينين، أو طائفة معينة التى تعرف بـ "السلفيين".
ومعرفة تفاصيل هذه الأبواب عند علماء السنة السلفيين، خاصة المتخصصين منهم في العقيدة.
والله أعلم
حرره علي محمد ثاني
Wanene Dan Salafiyya?
Dan Salafiyya shi ne wanda ya kasance a kan Aqidar Salaf (Magabata); Ahlus Sunnati wal Jama'ah.
Imamu Zahabiy ya ce:
"Dan Salafiyya shi ne wanda ya kasance a kan Mazhabar Salaf (Tafarkinsu)".
Duba Siyar 21/ 6.
Duk wanda ya dace da Salaf (Magabata) a tushen daukar Addini, da tsarin kafa hujja, da kuma a Tushen Sunna, kuma ya saba ma 'yan bidi'a a cikinsu to shi Dan Salafiyya ne, sawa'un ya dangantu zuwa ga wasu Malamai Sanannu, ko kuma wata Kungiya Sananniya wacce ake kira da "Salafiyyun, ko 'Yan Salafiyya", ko kuma bai dangantu zuwa garesu ba.
Tushen Dauko Addini shi ne Qur'ani da Sunna da Ijma'in Magabata.
Shaikhul Islami ya ce:
"Duk wanda ya yarda da Qur'ani da Sunna da Ijma'in Salaf to ya kasance yana cikin Ahlus Sunnati wal Jama'a".
Duba Fatawa 3/ 346.
Tushen Sunna su ne Ginshikan Imani guda shida (6) da abubuwan da aka riskar da su garesu, su ne:
(1) Imani da Allah.
(2) Imani da Mala'ikunsa.
(3) Imani da Littatafansa.
(4) Imani da Manzanninsa.
(5) Imani da Ranar Karshe.
(6) Imani da Qaddara na Alheri da na Sharri.
Ana riskarwa garesu:
(1) Mas'alolin Imani (Babin Sunayen Shari'a da Hukunce - hukuncensu).
(2) Matsayin Sahabbai.
(3) Mas'alar Shugabanci da biyayya wa shugabanni.
(4) Wala'i da Bara'i (Son Muminai da Barranta daga Kafirai).
(5) Riko da Sunna da Hadin kai.
(6) Nisantar Bidi'a da Rarrabuwar kai.
Duk wanda ya dace da Qur'ani da Sunna da Malaman Salaf a wadannan babuka to shi Dan Salafiyya ne a kan Tafarki dodar, ko da kuwa bai dangantu zuwa ga wasu Malamai Sanannu, ko kuma wata Kungiya Sananniya wacce ake kira da "Salafiyyun, ko 'Yan Salafiyya" ba.
Sanin wadannan babuka a fayyace ana samunsa ne a wajen Malaman Sunna Mabiya tafarkin Salaf, musamman wadanda suka kware a bangaren Ilimin Aqida daga cikinsu.
Allahu A'alam.