Subscribe Our Channel

Ingantaccen ilimin kimiyya da fasaha (Science & Technology) ba ya cin karo da ingantaccen Addini
Alaka tsakanin Addini da kimiyya da fasaha (Science & Technology) kamar alaka ce tsakanin Addini da hankali. Kamar yadda ba za a taba samun karo tsakanin lafiyayyen hankali da ingantaccen Addini ba, haka ba za a taba samun cin karo tsakanin ingantaccen Addini da ingantacciyar nazariyya ta ilimin kimiyya da fasaha (Science & Technology) ba. Saboda dukkan abin da suka gina ingantaccen Addini na gaskiya abubuwa ne na yakini tabbatattu da suke dacewa da abin da suke hukuntawa, don haka ba za su ci karo da abin da ingantaccen ilimin kimiyya ya tabbatar ba.
Shaikh Ibnu Uthaimeen ya ce:
لا يمكن أن يتعارض صريح القرآن الكريم مع الواقع أبدا، وأنه إذا ظهر في الواقع ما ظاهره المعارضة، فإما أن يكون الواقع مجرد دعوى لا حقيقة له، وإما أن يكون القرآن الكريم غير صريح في معارضته؛ لأن صريح القرآن الكريم وحقيقة الواقع كلاهما قطعي، ولا يمكن تعارض القطعيين أبدا.
مجموع فتاوى ورسائل العثيمين (1/ 68)
"Har abada, ba zai taba yiwuwa a samo karo tsakanin sarihin Alkur'ani Mai girma da waki'i ba, idan wani abu ya bayyana a waki'i alhali zahirinsa ya saba ma sarihin Alkur'ani to imma ya zama waki'in ba hakika ba ne, kawai zato ne, ko kuma ya kasance bai bayyana a fili Alkur'ani ya saba masa ba (kawai wani ne ya yi zaton akwai sabani tsakaninsu). Saboda sarihin Alkur'ani da yake a fili, da kuma waki'i (abu da ya faru a zahiri) dukkansu tabbatattu ne na yankan shakku, kuma har abada abubuwa tabbatattu na yankan shakku ba za su taba cin karo da juna ba".
Wannan ne ya sa yana daga cikin abubuwa da ake amfani da su wajen tantance Addinin gaskiya, da tabbatar da ingancinsa akwai tabbatar da cewa; shin abubuwan da Addinin ya kunsa ya dace da waki'in abin da yake zahiri ko ya saba masa?
Idan an samu sabani to Addinin ya zama batacce, imma saboda an gurbata shi, kamar yadda aka gurbata Addinin Yahudu da Nasara, ko saboda Addini ne kirkirarre. Saboda Allah ba zai saukar da abin da ya saba ma waki'in hakikanin abubuwa da suke faruwa a zahirin halitta ba.
Shi ya sa Shaikhul Islami ya ce:
يجب أن يعلم أن الحق لا ينقض بعضه بعضا، بل يصدق بعضه بعضا، بخلاف الباطل...
ما علم بالسمع الصحيح، لا يعارضه عقل ولا حس. وكذلك ما علم بالحس الصحيح، لا يناقضه خبر ولا معقول.
الجواب الصحيح لمن بدل دين المسيح (4/ 395)
"Wajibi ne a san cewa; gaskiya da gaskiya ba sa warware juna, a'a, sashe yana gaskata sashe ne, sabanin karya...
Duk abin da aka sani ta hanyar ingantaccen Nassi to hankali ko abin da yake a zahiri ba za su taba saba masa ba. Haka duk da abin da aka sani ta hanyar ingantaccen abu zahiri (ko binciken kimiyya da fasaha) to wani Nassi ko hankali ba za su taba karo da shi ba".
Saboda haka, abin da wadannan masu yakar Addinin suke kawowa, da nuna cewa; an samu abubuwa a bincike kimiyya da fasahar zamani da suka saba Alkur'ani ko Hadisi rudu ne kawai da jahilci, imma saboda rashin sanin hakikanin ma'anar Ayar ko Hadisin, ko rashin gaskiyar nazariyyar tasu ta kimiyyar.
Saboda haka, in dai wani binciken kimiyya ya ci karo da sarihiyar Ayar Kur'ani ko sarihin ingantacce Hadisi to kawai binciken rudu ne.
RubutawaDr. Aliyu Muh'd Sani
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter