Subscribe Our Channel

Please help them with the little you have.

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu.

DARULFIKR.COM TANA NEMAN TAIMAKON KUDI DAGA YAN UWA DOMIN CI GABA DA YADA ADDINI.

Darulfikr.com cibiya ce da ta shahara a shafin yanar gizo (internet) wajen yada karatukan malaman Sunnah dake nan gida najeriya da sauran sassa na duniya cikin harshen hausa.

Tun bayan kafa wannan cibiya shekaru uku da suka wuce, mun samu nasarori da dama wanda kadan daga ciki sune.

1. Muna da Malamai registered a Darulfikr.com wanda adadinsu yakai sama da dari hudu 400

2. Mun samu nasarar samun downloads na karatuka sama da milyan goma sha takwas (18 million+ )

3. Muna da audio files kama daga Muhadara, Tafsir, hudubobi da sauransu online a kan server wanda yawansu ya haura dubu arba'in da biyar (45,000) wanda nauyin su kuma ya haura 300GB

4. Darulfikr.com a kullum tana samun maziyarta daga mutum dubu biyar har zuwa dubu goma sha biyar (5000 - 15,000)

5. Muna da Admins/Agents da yawansu ya haura dari uku (300) a nan gida najeriya da ma sauran sassa na duniya

Alhamdulillah
Wannan kadan kenan daga cikin nasarori da wannan cibiya ta samu kenan.

MENE KE FARUWA DA DARULFIKR.COM?

A cikin shekaru uku da mukayi da fara wannan aiki, Alhamdulillah, babu wata matsala da ta taba taso wa darulfikr ta wuce awanni biyu batare da an Kawar da ita ba.

Kwatsam

Ranar Laraba data gabata munyi uploading wasu files wanda akai rashin nasara daya daga cikin files din yana dauke da Malware  wanda zata iya yin ta'adi mummuna akan servers din service providers dinmu kuma hakan na iya shafan sauran kwastomomin su, ba iya darulfikr ba.

Hakan ta saka service providers din mu tilas suka dakatar da account din darulfikr tare da kulle shi suka aike mana da sakon email.

Bayan mun tattauna dasu suka tilasta mana lallai upgrading tsarin(Plan) da muke kai tare da tilasta mana biyan wasu kudi Kafin bude shi.

Yanzu haka muna neman kudi Wanda ya kai kimanin Dala dubu daya da dari biyu da saba'in ($1,270), wanda a canjin naira suka kama naira dubu dari hudu da hamsin da bakwai da dari uku da sittin (N457,360) akan farashin canji N360.

Munyi  iya kokarin kawo karshen matsalar ta wasu hanyoyin daban da muke ganin yiwuwar su amma hakar mu bata cimma ruwa ba, tilas sai mun fito mun bayyana wa mabiyanmu abinda ke faruwa mun nemi taimako.

A yanzu haka muna da kudi a asusun mu da yakai dala $100, naira dubu talatin da biyar N35, 000.

Yan uwa masu albarka, ku tallafa wa wannan cibiya mai albarka domin ci gaba da yada Sunnah.

Zaka iya tallafawa da duk kankantar abin da Allah ya hore maka, ko ka taya mu isar da wannan sakon ga wanda kasan zai iya tallafawa.

Allah ya na cewa cikin Suratu Ali Imran

لَن تَنَالُوا الْبِرَّ حَتَّىٰ تُنفِقُوا مِمَّا تُحِبُّونَ وَمَا تُنفِقُوا مِن شَيْءٍ فَإِنَّ اللَّهَ بِهِ عَلِيمٌ

Ga account details na banki Kamar haka :

Banki: Access Bank
Sunan akawun: Mubarak Auwal
Lambar akawun: 0737644005

A taimaka domin ciyar da darulfikr gaba.
Darulfikr taku ce domin yada sunnah

Allah ya bada ikon taimakawa. Ameen

Domin Karin bayani za'a iya tuntubar wadannan lambobin:

Muhammad Basheer   08139545853
Mubarak Auwal             09020514667.

Mubarak Auwal.
A madadin kwamitin gudanarwa na Darulfikr.com
22-07-1439.
09-04-2018.

*ANA CI GABA DA KARBAR TAIMAKON FARFADO DA SHAFIN DARULFIKR.COM*

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu.

Kamar yadda sanarwa ta gabata jiya, na neman taimakawa wannan cibiya mai albarka, Alhamdulillah mun samu mutane da suka taimaka kowa dai dai gwargwadon abin da Allah ya hore  masa.

Daga sanarwar a safiyar jiya litinin zuwa wayewar garin yau talata @7:52am, mun samu N124,539.10 (daga mutane 54 ) idan muka tara da N35, 000 da muke dasu kudi Jimilla sun kama N169, 539.1

Muna addua ga wadanda suka taimaka, da Kudinsu, da lokacin su wajen isar da sakon, dama masu addua da fata nagari, Allah ya saka muku da Aljannah.

Har Yanzu dai muna ci gaba da neman wannan taimako daga yan uwa.

Ga account details na banki Kamar haka :

Banki: Access Bank
Sunan akawun: Mubarak Auwal
Lambar akawun: 0737644005

A taimaka domin ciyar da darulfikr gaba.
Darulfikr taku ce domin yada sunnah

Allah ya bada ikon taimakawa. Ameen

Domin Karin bayani za'a iya tuntubar wadannan lambobin:

Muhammad Basheer   08139545853
Mubarak Auwal             09020514667.

Mubarak Auwal.
A madadin kwamitin gudanarwa na Darulfikr.com
23-07-1439.
10-04-2018.@7:52 am

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter