Subscribe Our Channel

Yana Daga Akidar Shi'a!!!
* An tambayi Kuu'iy, wani babban malamin shi'a ne, ya rasu kafin zuwan Kumaini, cewa: "Shin za'a ce da dan shi'a mumini, koda ya bar wasu wajibai kamar sallah?" sai yace "Eh".
— Duba Firakin Najah Juz'i na Biyu Shafi na Dari hudu da talatin da takwas: (2/438), Tambaya ta (1375).
Bari na dan kawo wasu yan dalilai daga sunnah:
1 — Manzon Allah SAW yace "Lallai Tsakanin Mutum da Shirka da kafurci: Barin Yin Sallah" (Muslum: 987, Abu-Dawood: 1658, An-Nasa'i: 1/231 da wasunsu). Wani hadisin na (Turmizi 2621, da An-Nasa'i: 1/132, da Ibn Maja: 1079) duka suna suna da mutum ya bar sallah to ya zama kafuri mudlaqan.
2 — Abdullahi Dan Shaqiiq (Tabi'ine) yake cewa: "Sahabban Manzon Allah mai tsira da Aminchin Allah, sun kasance basa ganin barin wani aiki (Daga cikin ayyukan Muslunchi) kafurchi ne (Barin addinin Muslunchi ne) bayan Sallah" Duba (Turmizi: 2622, Da Littafin Ibn Nasir "Ta'azeemu Qadrus Salah" (948).
.
— Allah ya Kyauta ya kiyaye mu daga irin wannan muguwar Akida Ameen.
:
Abu-Ammar
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter