SOYAYYA GA MATASHIN SAURAYI ILLANE KAMAR YADDA NA FADA.
.
Na farko ku fahimci wata ka'ida ta malaman Usulul-Fiqhi: "Dukkanin umumi yana da kebantacce" - watau duk abunda akace umum dinsa ga hukuncinsa to sai ansamu inda ya ware da wani hukuncin.
.
Na biyu kuma ku fahimci ba ina nufin dukkanin soyayya ba duk yadda aka ginata da munufofinta illace ba, sai dai da mafi yawa nake nufi.
.
A iya nazari na, bincike na da la'akari danayi mafi yawan matasa kan gina soyayane amakance, batare da sanin wai ina suka dosa ba, bayanan sukanyi soyaya acikin lokacin wasu batare da yin tunani ko auna shin wane alfanu soyayar da suke akai zatayi musuba, ta hanyar la'akari da wasu daga cikin matsalolin da nake gani kamar haka:
.
— Mace Allah yayi mata saurin girma, shikuwa namijin ba haka abun yake ba don haka zaka samu namiji anyiwa kannansa bata sama da biyar aure amma shi ko niyya bai fara ba, don haka bisa wannan Zaka kasance kana soyayya da mace karshe wani zakayiwa hidima da reno..shin me zai hana ka jira naka lokacin.
.
— Soyayya ba tare da sanin iyaye ba: kwatsam kuna cikin soyayya da budurwarka kun soyu harkun soye dukkaninku kuna yunkurin aure kuma level din kowannenku yakai, amma iyayenku su kekashe kasa suce ba haka ba, saboda kawai ka sabawa Allah da Manzonsa na rashin neman izinin fara zance.
.
— Soyayyar Nishadi: Wasu kanyi soyayya don nishadi a takaice dai yayiwa budurwar "Takiyya" "Munafurci" ya nuna mata yana sonta da kaunarta ya dasa mata cutar so amma karshe ya juya mata baya daidai lokacin da take bukatarshi saboda dama ba sonta yake ba hakan kuma yakan jawo mata matsala.
.
— Wasu matasan kan shiga soyayya bil-haqqi su soye harsu kone yayin da iyayenta suka tado maganar aure sai ya rikice saboda bai son ya rabu da ita kuma gashi bai da karfin yin aure me zai faru dayan biyu:
1 — Ko dai ya rasata hakan kuma zai kuntata a gareshi idan yayi hakuri kenan idan kuma abun ya ta'azzara ya zama kamar laila majnun.
2 — Ko kuma auren ya yiwu amma daga baya yayi dana sanin yin auren saboda baida karfin yin auren da rike mata, karshe matsaloli su biyo baya.
.
— Dayawa daga cikin masoya sun shiga soyayya ne dashaukin sun gani ko sunji labarin yadda wasu ke zabga soyayyarsu gwanin dadi sai yayi sha'awar hakan ba tare da la'akarin cewa shin ko wane level yake yanzu? Shin kuma ya kamata yayi soyayya?.
.
— Haza zalika muna shiga soyayya ba tare da lura da yadda fidrar mace take ba na:
1 — Saurin girma.
2 — Aure da wuri.
3 — Zamanta gida ba aure illa ne
4 — Tsawaita karatu gidan iyayensu banasu bane.
5 — Da sauransu.
.
— Mu sani cewa kai najimi kana da bukatar karatu mai zurfi ta fanin karatun sana'a da addini, wanda kafi mace bukata, haka zalika kana bukatar mallakar wasu abubuwan da zaka tafiyar da rayuwarka dana iyalinka idan kayi aure.
.
— Ita kuwa mace zurfin karatunta ko a gidan miji zata iyayi domin bata nemo abinci, kayan sawa ko waninsu, tana gida a mafi yawan lokutanta.
.
— Babu wani babban dalili da ake jira ga mace takai wadannan matakan kafin ayi mata aure kamar girma da hankali.
.
— kai kuwa ko ka kai rihi tsawo kuma kaine sarkin hikima da hankali da ilimi a garinku, matukar bakada wadancen marikan rike iyalin tofa ba maganar aure sai tayaka addu'a.
.
— Akwai Dalili da dama da nake ganin cewa dayawa daga cikin matasa suna cikin matsala da rikici, wannan shawarace ina fatan mu kiyaye.
.
Amma mu sani cewa galibi abunda mutane ke cewa shine "aure nufin Allah ne" "Aure lokacine" hmm Amma idan anbi dokokin Allah da manzon Sa.
.
Abu-Ammar.
28/02/2017M.
Home
»
»Unlabelled
» SOYAYYA GA MATASHIN SAURAYI ILLANE KAMAR YADDA NA FADA.