Subscribe Our Channel

Ramalana //2
(1) Yana daga Cikin Fa'idojin azumi, shine samun Tsarkin Zuci, dana Jiki, Al-Imamu Ibn Kathiirin a Cikin Tafsirinsa, a karkashin Tafsirin fadin Allah Ta'ala: "Yaku wadanda kukayi Imani an wajabta azumi akanku....." (Suratul-Bakara)
.
Sai Yace:
Allah ya wajabta azumi akan bayinsa domin su samu TSARKIN ZUCIYA, daga dattin Zunnubai da
tsarkake Jiki, daga kasala, da Takura hanyar shaidan, sai ya ambaci hadisin Ibn Mas'ud wanda Al-Imamul bukhari da Muslum suka rawaito, wanda Annabi mai tsira da Amincin Allah yake, kira ga matasa dasuyi aure, idan basu samu dama ba tosuyi azumin domin ya kangesu daga sabon Allah.
(2) Azumi yana koya mana hakuri da Juriya da kuma jajurcewa, ta hanyar kamewa daga abubuwanda ka kwashe wata da watanni kana aikatawa na daga ci-da-Sha da sauransu, Kamar Yadda Alu bassam ya ambata a cikin "Tayassirul Allama sharhin Umdatul-Ahkam".
(3) Azumi yana koya mana yan uwantaka, a dauka tare a aje tare, sahur da buda baki da sauran ibadoji duk tare akeyi, yana daka cikin manyar manufar shari'a shine samun hadin kai, shiyasa annabi yayi ta horonMu akan hadin kai da nisantar sabani mai janyo rabuwar kai, Allah ka kara hada kawunan mu akan Al-Kur'ani da Sunnah
#Haskensunnah,blogspot,com
#IbrahimAbuammar
02/09/1439H - 2018M
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter