NASIHA.
(Mal. Bahause Kamar yadda muka sani, an sanshi da kunya)
.
* Yana daga cikin manyan kura-kurai masu halakarwa, da mutane ke aikatawa musamman a wannan zamani, lokacin biyan bukata (Fitsari ko Ga'idi) shine bayyana tsiraici ta yadda za'aga Al-aurarki/ka, koma yinsa kusa da Mazaunan Mutane.
.
— Shiriyar Annabi Mai tsira da Amincin Allah Yayin Biyan bukata ita ce: Ya kasance yana Buya daga Jama'a, ba'a jin sauti ko Wari, yayin da yake biyan bukata.
.
— Kamar yadda ya tabbata acikin hadisin Jabir wanda Abu-Dawood (2), da ibn Majah (335) suka fitar, Shi Jabir R.A din yake cewa mun fita da Manzon Allah SAW a cikin wata tafia, sai ya kasance baya shiga duhuwa (Cikin itatuwa haka) (Yana nufin baya fita biyan bukata) har sai ya faku, ba'a ganinsa" Duba Ibn Majah da Abu-Dawood.
.
— Hakama A hadisin Abdullahi Dan Ja'afar, yace Manzon Allah SAW ya kasance Yafi soyuwa a gareshi yayi Sutura da Tudun Kasa(bogo ko waninsa), ko itacen dabino" Duba: Muslum (342), da Abu-dawood (2549), da Ibn Maajah (340), da Ahmad (1/304) A Musnad.
.
* Imamun nawawiy yace karkashin wannan hadisin: "A cikin wannan hadisin, yana daga fiqhunsa (da zamu fahimta) Mustahabbancin Suturcewa yayin biyan bukata...." Duba Sharhin Muslum (3-4/275).
.
* Abun Tsoron Shine Hadisin Bukari da Muslum, daga Abdullahi Dan Abbas R.A, yace: Manzon Allah Mai tsira da Amincin Allah ya Gitta wasu kaburbura guda biyu, sai yace: "Lallai su biyun nan (yanzu haka) yana azabtar dasu, kuma ba'ana azabtar dasu da wani abu mai girma bane (bisa al-adar mutane muna daukarsu kananan ayyuka na sabo), amma na dayan su ana azabtar dashi ne saboda ya kasance baya sitirtuwa yayin fitsari, amma na karshen su ya kasance yana tafiya da Annamimanci (Tsakanin Jama'a), sai ya dauki tarkajiyar dabino danya ya tsagata biyu, sai ya dasata a cikin kowanne kabari daya daya. Sai mukace (sahabbai): Ya manzon Allah mai yasa ka aikata haka? yace: "Meyuwa a saukaka musu matukar dai bata bushe ba" Duba: bukhari (1/379, 385), da Muslum (1/3/200 Sharhin nawawiy), da Abu-dawood: (1/5/20) da wasunsu.
.
— Wannan Hadisin yana nuna mana cewa Lallai Rashin suturcewa daga fitsari yana jawo azabar kabar, sannan muna daukarShi karamin aikin sabo Amma a wurin Allah babban Laifi ne, kamar yadda malamai sukayi bayani tiryan-tiryan.
.
— Ya Allah ka tsaremu daga Azabar kabari, ka kara shiryar damu hanyarka Mikakkiya.
.
Ibrahim Yunusa Abu-Ammar
09/10/1438H - 03/07/2017M