[INUWAR SUNNAH (2)] HASKEN ILIMI A RAYUWA KASHI NA BIYU
*****************
.
°°°°HASKEN ILIMI A RAYUWA°°°°°
.
• FALALAR NEMAN ILIMI; Neman ilimi yanada fawa'id da dama, wadanda suka fito gada taskar Al-kur'ani da Sunnah da maganganun magabata na kwara.
..
• Ubangiji Ta'ala yana cewa; "Allah yana daukaka wadanda sukayi imani daga cikinku, da wadanda ya baiwa ilimi, da wata daraja. Kuma Allah mai bada labari ne akan Abunda kuke aikatawa" [Mujadatal-11]
.
• A wata ayar kuma yake cewa; "Kace Ya ubangiji Karamun Ilimi" [Daha-114] Saboda darajar da ilimi ke da ita ubangiji bai umurci annabinsa da ya roki dukiya ko waninta ba, sai ilimi.
,
• A karkashin Wannan ayarce Muhyiddeen Imamun Nawawiyy yake cewa; "Wannan ke nuna Darajar ilimi da kuma girman falalrsa, Ta yadda babu wani umurni da (Allah) ya yiwa Annabi SAW akan ya roka a kara masa Shi, face ilimi" [Sharhur-Rayadus-Saleehina-babu fadlil Ilim]. - Sannan Turmizi ya fitar da hadis daga Abu-huraira, wanda hadisin yake hakaito addu'ar da manzon Allah SAW yayi akan karin ilimi, hadisin zaizo nan gaba, insha Allah.
,
• A wani Wurin Mahaliccin Sammai da kasa yake cewa; "Kace 'Shin da wadanda suna sani (sunada ilimi) da wadanda babu sani ba (jahilai) yasu zama daya?...." [Zumar-09], Tambayace wacce ansar ta itace bazasu taba zama daya ba har sai ranar da rakumi ya shiga ta kofar Allura. Abun nufi anan shine; Allah zai daukaka masu ilimi akan muminai, matukar sun hada da ilimi da kuma aiki dashi da tsoron Allah.
,
• A wata Ayar Mahaliccin Abu-Ammar da sauran halittin gaba daya yake cewa "Lallai wadanda suka kasance suna Tsoron Allah a cikin bayinshi(Allah) Sune Masu Ilimi, Lallai Allah Madaukaki ne kuma mai gafara" [Fadir-28]
,
• A karkashin Wannan ayace Abdullahi dan Mas'ud Allah ya kara yarda dashi yake cewa; "Malami ba ana nufin mai tarin hadisai ba(tarin ilimi), a'a abun nufi shi malami shine mai yawan tsoron Allah (A cikin Iliminsa)."
,
• Shi kuwa Hasanul Basari cewa yayi; "Malami Shine wanda yake jin Tsoron Allah a boye(ba tare da nunawa jama'a ba), ya kuma kyamaci abunda Allah ya kyamata, sannan ya nisanci abunda Allah yake fushi dashi, sannan sai ya karanta waccen ayar dake sama.
,
• Idan mukayi duba acikin wadannan ayoyin dana kawo zamu lura da wasu falaloli masu yawa da ubangiji ta'ala, yayiwa ilimi da mai dauke da ilimi ta yadda mai ilimi fifikonsa yafi mumini wanda bashida Ilimi.
,
• Haka zalika falalarsa ce tasa ubangiji jalla wa'ala ya umurci bawansa badadayins annabinsa muhammad SAW ya tambayi kari akan ilimi, wanda ko a kissar annabi musa da kidru, idan muka duba zamuga yadda ilimin ke jagorantar tafiya, shiyasa suka shallake duk wata matsala ta kan hanya, da ayyukan lada.
,
• Dan uwa, menene ya kangeka daga tashi ka nemi, ilimi rayuwar iyali shin kakai annabi SAW, koko harkokin rayuwa baka kai annabin rahama ba, idan kasuwanci ne kuma baka kai usman dan affan ba khalifa na ukku, kaji tsoron Allah, kiji tsoron Allah, kuji, suji, muji, kowa ma yaji tsoron Allah, mu tashi muneni wannan falala mai tarin albarka. Muna fatan Allah ya bamu ilimi mai amfani.
,
Anan zamu dakata sai kuma wani darasin idan Allah ya kaimu zamu dasa akan wannan falalar ta ilimi daga hadisan annabin rahama in gatattu. insha Allahu ta'ala.
.
○
○
,
↓↓↓↓↓
♫ Rubutawa;
Ibrahim Yunusa Abu-Ammar
••••••••••••••••••••••••