ALLAH YANA INA? YANA SAMA? KO YANA KO INA?.
.
Abune sananne da kowa ya sani cewa lallai Allah yana sama, idan da zaka tambayi yaro karami kace dashi ina Allah yake zai ce maka yana sama, hatta wadanda ba musulmai ba idan da zaka tambaye su ina Allah yake zasu ce maka yana sama, yayin da kuma idan muka koma acikin Al-kur'ani zamu ga Allah yana tambayarsu akan wanda ke sama? Fadin Allah cewa: "Shin kun Yarda akan wanda ke sama bazai iya shafe kasa ba tare daku...." [Suratu Mulk : 16].
.
Shin wanene wanda ke Saman? Wanda yake da ikon shafe kasa da abunda ke cikinta bayan Allah?. Wannan aya karara tana nuna Allah yana sama domin shine mai ikon kifar da duniya da abunda ke cikinta
.
Dalilai da dama sunzo daga Al-kur'ani da sunnah da maganganun malamai wanda suke nuni da Allah yana sama. Allah yana cewa "Zuwa gare shine Kyawawan kalmomi da ayyuka kyawawa suke daukaka" [Suratul Fadir]. - shin a ina suke daukaka, idan ba sama ba dalili da dama sun nuna ayyukan bayi sama suke daukaka, to wanene wanda gareshi ne suke daukaka.
.
A wani wuri kuma yace "Ka tsarkake sunan ubangijinka ma daukaki" [Suratul A'ala]. - madaukaki wanda ya daukaka zuwa samma sannan ya daidaita akan al-arshi.
.
Fadin Allah: "Saukakke ne (Al-kur'ani) daga wanda ya halicci kasa da sammai madaukaka" [Daha : 4] - Daga ina aka saukar da Al-kur'ani daga sama, tunda Daga sama aka sukar dashi kuma daga wurin ubangiji, to lallai Allah yana sama.
.
Aya ta gaba suraud Daha 5: "Mai rahma (Allah) ya daidaita Akan Al-arshi" - a ina al-arshin Allah yake? Idan yana sama to Allah ma yana sama.
.
fadin Allah a cikin suratul A'araf ayata 54, tana kara karfafa wancen Zancen na Allah dake sama "....Sannan ya daidaita Akan Al-arshi..."
.
Da kuma fadin Allah cewe "...Sannan ya daidaita zuwa sama..." [Bakara : 29] wannan ayar tayi bayani karara cewa Allah yana sama - imamul bukahari ya nakalto a cikin littafinsa, a kitabut tauheed daga Mujaheed da waninsa yayin da sukazo tafsirin wannan aya sai sukace "Ma'ana ya daidai akan sama shine: Madaukaki wanda ya daukaka (zuwa sama)".
.
Wadannan ayaoyin dama wasu ayoyin da dama suna nuna Lallai Allah yana sama, amma bari muje ga hadisan annabi SaW:
.
Hadisi yazo cikin Sahihi Muslum cewa Manzon Allah SAW yayiwa sahabbai kuduba a ranar arfa a hajjin bankwana sai yace dasu "Shin ko na isar(da sakon Allah). Sai sahabbai sukace Eh!, sai Manzon Allah ya nuna yatsansa zuwa sama yana mai nuni zuwa ga munate yana Cewa "Ya Allah ka shaida". [Muslum] - Idan Allah baya sama menene dalilin da Manzon Allah sai ya daga hannunsa da fuskarsa zuwa sama, hakama mai addua idan yana addua?.
.
A hadisin Mu'awuya dan Hakim kuma manzon Allah yake cewa " Ubangiji Allah wanda ke acikin sama sunanka ya tsarkaka" Sai manzon Allah yace da baiwar Mu'awuya "A ina Allah yake?" Sai tace yana acikin sama Sai manzon Allah yace "Ka yantata domin ita mumina ce" Imamu maliku ya fitar dashi acikin muwadda, da muslum da waninsu. - Sannan hadisi yayi bayani karara cewa Allah yana sama, amma bari mu kawo wani wanda manzon Allah ya ambata Allah yana sama karara shine:
.
SAW yace da husaini "Ubangijji nawa ake bauta mawa?" sai yace guda bakawai, shidda suna kasa, daya kuma yana sama. Sai SAW yace "Daga wa(Cikinsu) kake kwadayin sakamakonka?" sai yace wanda yake acikin sama. Sai SAW yace "To kabar(bautama) shiddan, ka bautama wanda yake acikin sama, Ni kuma zan koya maka addu'o'i guda biyu" sai ya muslumta......." Turmizi (3483).
.
Wannan kenan atakaice, dangane da hadisan manzon Allah, Ga kuma abunda magabata suka fada dangane da wannan mas'alar:
1- Imamush Shafi'i: "Lallai Allah madaukaki yana akan Al-arshi a cikin saman sa, yana kusantar halittunsa(da iliminsa) yadda yaso, sannan yana sauka saman duniya yadda yaso. "Shin wai daga ina yake sakkwowa zuwa saman duniya" (Hadisi ya tabbata cikin bukhari da muslum cewe Allah yana sauka saman duniya a 1/3 dare na karshe) amma daga ina yake sakkowa.
.
A cikin Sharhul akidatud dahawiyy 322, Imama abu hanifa yana cewa "Duk wanda yace, ban sani ba shin ubangijina yana sama ko yana kasa ya kafurta, domin fadin Allah "Mai rahman ya daidaita akan al-arshi" al-arshinsa kuma yana saman sama ta bakwai, Kuma lallai dole muce yana akan al-arshinsa....".
.
Da wadannan ayoyin da hadisai da maganganun magabata na kwarai zamu fahimci cewa lallai Allah yana sama, sai dai ilimisa yana kewaye da komai. Idan kace Allah yana ko ina, to kamar kanaso kace Allah bazai iya sarrafa alarsa ba, sai yana wurarensu.
.
Sannan abunda muka fahimta shine, wannan akidace ta sufaye kuma sun kirkire tane don manufarsu manufar kuma itace, idan sukace Allah yana sama, to yaya sufee zaice shi Allah ne ko waliyyi wane Allah ne bayan shi Allah yana sama, amma idan sukace yana ko ina kenan zaa samu Allah anan duniya. Sannan acikin littattafan sufaye ne sukace komai ma Allah ne dutsi, icce kasa kaya, waliyyi, duk Allah ne Allah ya kiyashe mu.
.
Mudau bazamu juya aya ko hadisi ba don bukatarmu kota wanin mu "ALLAH DAI YANA SAMA" - "kA TAMBAYI WANI YARO A ANGUWAR KU IDAN BAKA YARDA BA".
.
"Kada kayi comment a wannan post din matukar ba fadin Allah da manzon Sa zaka fada ba a bisa manhajin magabata nakwarai"
.
Abu-Ammar
15/03/2017