*ADADIN SHAHIDAI DA INGANCIN SHAHADAR WACCE TA MUTU A NAKUDAR CIKIN SHEGE ?*
*Tambaya*
Assalamu alaikum Allah ya gafarta Mallam don Allah ina Matsayar Malamai akan wadannan Mas'aloli, tare da ambaton dalilai daga Qur,ani/Hadithi : Mutane nawa ne Ya tabbata a Alqur,ani/Hadithi Sunyi Mutuwar Shahada? Domin wani Dalibi abokina ya ce: Albani ya ya Ambaci : 9 a cikin AHKAMIL JANA'IZ na duba ban gani ba, sannan idan Mace ta Mutu ayayin haihuwar Cikin Shege, shin itama ta yi Shahada?
*Amsa*
Wa'alaikumus salam
To dan'uwa shahidai suna da yawa: sun haura guda tara : Ibnu- hajar yana cewa : "Mun tattara hadisan da suka yi bayani akan shahidai sai muka samu sama da nau'i ashirin, na shahidai, Fathul-bary 6\43 hakanan Suyudi a littafinsa mai suna : Abwabissa'adah fi asbabi assa'adah, ya kawo sama da guda talatin
Ka ga daga ciki, akwai wanda ya mutu a fagen daga, da wanda ya mutu da ciwon ciki, sai wanda ya mutu a lokacinn kwalara sai kuma wanda ya mutu ta hanyar rusowar gini, sai wanda ya nutse a ruwa, Hakanan wanda ya mutum wajan kare dukiyarsa, da wanda kunama ko mijiji ya harba, sai ya yi ajlinsa, haka matar da ta mutu wajan haihuwa, dama wanda namun daji suka cinye shi Haka wanda aka kashe shi saboda kare iyalansa, duk wadannan sun tabbata a cikin hadisai .
Sai dai wasu malaman suna ganin akwai sharuda kafin mutum ya samu shahada :
Daga ciki kada ya zama : Ba ta hanyar gangaci ya mutu ba, kamar mutumin da bai iya ruwa ba, ya shiga kogi, sai ya mutu, sannan kar ya zama ta hanyar sabo ya isa zuwa shahadar, kamar matar da ta mutu wajan nakudar cikin shege, ko bawan da ya gujewa mai gidansa, sai ya mutu a hanya, wasu kuma suna ganinin hakan ba sharadi ba ne, tun da hadisan ba su kayyade ba.
Don neman Karin bayani duba : Fataawal-kubra na Ibnu-taimiyya 3\22 da Mugni A l-muhtaj 3/166
Allah ne mafi sani
*Dr Jamilu zarewa*
9/12/2014
Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*