Subscribe Our Channel

Ramadhaniyyat@1439H [8]
Dr.  Dani Umar rijiyar lemu
Su Ma Al'ummu Ne Irinku

Allah Ta’ala yana cewa:

1. (Kuma babu wata dabba da take tafiya a bayan kasa, kuma babu wani tsuntsu da yake tashi da fukafukansa, face (su ma) al’ummomi ne irinku. Ba mu yi sakacin barin wani abu ba a cikin littafi, sannan kuma zuwa ga Ubangijinsu ne za a tara su). [Al-An'am, aya ta 38].
2. Ya wajaba mutane su sani ba su kadai Allah ya halitta a wannan duniya ba, balle su yi zaton zai bar su sakaka babu wani tsari. Duk halittar da Allah ya yi ya tanadar mata wani tsari da take tafiya a kansa, hatta dabbobi da tsuntsaye da ya halitta yana gudanar da rayuwarsu ne cikin wani tsari da ya dora su a kai.
3. To haka ya zama wajibi rayuwar mutane ta kasance tana gudana ne a kan irin tsarin da Allah ya tanadar musu su gudanar da rayuwa a kansa, wanda shi ne abin da ya aiko annabawansa da shi.
4. Manufar a nan ita ce bayanin fadin Kudurar Allah da zurfin iliminsa da kuma yalwar ikonsa.
5. Duk wanda ya kauce wa tsarin da Allah ya dora dan'adam a kansa ya zabi ya yi rayuwa yadda zuciyarsa take gwada masa, to babu shakka wannan dabbobi sun fifi ta a kansa, domin kuwa su al'ummu ne da suke rayuwa a bisa wani tsari da Allah ya so musu su rayu a kansa ba tare da kauce masa ba.

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter