Subscribe Our Channel

Ramadhaniyyat@1439H [4]

Malami

1. Ka nemi ilimi wanda ya samo asali daga Littafin Allah da Sunnar Manzon Allah (SAW) da fahimtar sahabbai da tabi'ai da sauran malamai magabata.
2. Ka sani ilimi mai amfani shi ne wanda zai koya maka abubuwa guda biyu:
Na daya, sanin Allah da siffofinsa da sunayensa da ayyukansa. Wannan shi ne zai gadar maka da kaunarsa da ganin girmansa da tsoronsa da yarda da kaddararsa.
Na biyu, sanin abin da Allah yake so yake kuma yarda da shi da kuma abin da yake ki yake kuma fushi da shi, cikin abin da ya danganci akida da ibada da mu'amala da sauran ayyuka na bayyane da na boye.
3. Kuma ka sani banbanci tsakanin malamai na-Allah da malamai yan duniya shi ne, su malamai 'yan duniya su ne wadanda suke neman duniya da iliminsu, masu son shugabanci da daukaka da shuhura da yabon mutane ta kowane hali ko da kuwa za su kauce wa hanyar Allah ne. Malamai na-Allah kuwa ba haka suke ba, kuma wadannan abubuwa duka ba sa gabansu.
4. Kai mai kira zuwa ga Allah ka tuna cewa babban guzurinka shi ne neman ilimi koyaushe, ka nemi sannin kowanne fanni daga cikin fannonin ilimin addini, kamar Tafsiri da Hadisi da Fikihu da Tarihi da harshen Larabci da adabinsa, domin fahimtar ilimin addini tana bukatar duk wadannan fannoni, don haka wajibi ne ka sami rabonka daga kowannensu.
5. Yana da kyau matuka ka dimanci karanta tarihin magabata na kwarai domin yana tausasa zuciya ya fitar mata da jiji-da-kai ya kuma gadar mata da tsoron Allah. Don haka ka lizimci karatun littafin Siyaru A'lamin Nubala' Na Az-Zahabi (R.H).
Dr. Sani Umar

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter