Jagoran daya daga cikin coci-coci mafi girma a Najeriya ya haifar da rudani a cikin wani wa'azinsa ga mabiya addinin Kirista.
Pastor Enoch Adeboye, wanda shi ne shugaban cocin Redeem na daya daga cikin fastoci ma su arziki a Najeriya.
A cikin wani hoton bidiyonsa da ya mamaye shafukan sada zumunta na intanet, Faston ya ce duk wanda ya ki bayar da kudin sadaka da ake kira baiko ba zai shiga aljanna ba.
Sannan ya bukaci sauran shugabannin rassan cocin su gabatar da sakon ga mabiyansu a lokacin da yake wa'azin.
Kalaman na Mista Adeboye sun haifar da cece-kuce tsakanin mabiya addinin kirista a Najeriya.
Wasu daga cikin mabiyan sun bayyana rashin jin dadi kan yadda ake kokarin mayar da addinin kirista na kudi.
Wasu kuma da ke goyon bayan kalaman na faston sun ce hakan yana cikin karantarwar littafi mai tsarki.