Subscribe Our Channel

BAMBANCIN MU DA MAGABATA A KAN RANAR JUMA'A

1)Magabata suna dau kan Juma'a kaman Ranar Idi don haka suke kwalliya da ziyara,sadaqa da yawai ta aikin Alkhairi don samun kusanci gurin Ubangijin mu
Mu muna daukan juma'a yan da suka dauke ta sai dai bama bata haqqin ta na ruban ya aikin Alkhairi kaman yadda suke yi!!
2)Magabata sun tsaya chak a in da Manzo S.A.W ya tsaya da ranar Juma'a basu qir qiro sabbin abuba
MU mun qir qiro abubuwan da basu cikin addini Kamar fadin JUMA'A KAREEM dss da turo saqonni ta waya da Hadithai yawanci marasa inganci kan falalar ranar!!
3)Magabata suna cika Masallacin Juma'a tun bayan Alfijir kaman yadda aka ruwaito daga gare su
Mu yawancin mu sai Sallar kawai muke samu!!
4)Magabata suna girmama darajar ranar(kasance war a ita za a tashi qiyamah)don haka suke tsoron yin sabo acikin ta
Mu muna darajata kuma mun san a ita za'a tashi qiyama amma bamu bar gulma,munafunci,zalunci da qaryaba!!
5)Magabata cike suke da kwadayin wannan Saa'ah da a kace ba a mayar da addua a lokacin don haka tashin hankalin su shine Juma ah ta wuce ba tare da sun dage da ibadu ba
Mu muna kwadayin samun lokacin sai dai hakan bai sa mun dage da yin Abubuwan da zai amfane mu ba har a lokacin da ake zaton Saa'ar(bayan la'asar)!!
6)Magabata suna cike da tsoro har sai sun ga jumaah ta wuce ba'a tashi qiyamah ba(Saboda a irin ranar zata tashi)
Mu neman duniyar mu da dogon buri da shagala bai sa mun iya jin wannan tsoro ba!!
Allah kasa muna daga cikin waďan da zasu sallaci wannan sallah gobe kasa mu dace da lokacin da baka mayar da Addu'a Ameeen
Wannan tunani na ne ba lallai yazo 1 da naka ba! idan nayi dai dai daga Allah ne idan nayi  kus kure daga gare nine kasancewa ta ba  Ma'asoomi ba
Mal. Ibrahim Nuhu Imam Rimi
 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter