Ko kasan? /1
Ko kasan Cewa shi'a Imamiyya kashi-Kashi ne: "Shi'a Imamiyya Sun kasu kashi-kashi ne saboda yawan Sabani da Malmansu suka shiga wurin tantance Imami da kuma tabbatarda Imamansu, hakan na faruwane aduk lokacin da Wani daga Imamansu ya rasu wurin tabbatar da wani imami sai a samu rabuwa ("Shi kuma Addinin Musulunci Yafi kowane addini kira da kwadaidarwa akan hadinka da nuna munin rabuwar ka!"), Kumafa Imamanci Shine Abu Mafi girma da Muhimmanci sama da komai a addininsu, kamar yadda Malamansu suka tabbatar, Kamar mai Littafin Minhajil Karama.. Ibn Mudahhiril Hilliy.. Ya fada.
.
Misali:
Shi'a Imamiyya da ake kira da kaisaniyya: Su cewa sukayi Imamima kwata-Kwata guda hudune dagasu babu wani Imami bayansu Sune.
1- Aliyu
2- Hasan
3- Husain
4- Muh'd Bn Hanafiyya
- Shiyasa Wani Mawakinsu Mai Suna Kusayyar Azzah Yace Cewa:
"Ku saurara Lallai Imamai daga kuraishawa ne, Shuwagabanni na gaskiya guda hudune Cif, Aliyu da Ukku daga Yayanshi, Sune Jikokinnan babu Wani boyuwa a garesu (Sanannu ne), Daya daga cikin Jikokin Jikane na Imani da Da'a (Hasan), Wani Jikan Kuma Karbala ta boye Shi (Husain), Dayan Jikan Kuma baya Dan-Danar Mutuwa harsai ya Jagoranci dawaki (Runduna) ga tutanan a gabanshi, Ya buya bama ganinsa tsawon zamani, Yana can Rabwa (Wani kogon dutsine dake Tsakin Makka da Madina) A wurinsa akwai Zuma da Ruwa (Muh'd, Yana Nufin Mahdi)"
.
Abin Lura Cikin Wannan Baiti:
1- A'imma (Shuwagabanni) daga Kuraishawa ne tabbas Wannan haka yake da fadin manzon Allah "Kuraishawa Sune Majibinta Wannan Al-amarin..." Duba: Musnad Ahmad (1/18) Tahkikin Ahmad Shakir.
2- Shuwagabanni na gaskia Guda hudune Cif! Tabbas "Mafi girman Shuwagabanni Masu daraja da gaskia sama da duk wasu shuwagabanni sune khulafa: 1. Abubakar, 2. Umar, 3. Usman, 4. Aliyu Yardar Allah ta kara tabbata a garesu.
3- Shuwagabannin nan Sune, Aliyu, da yayansa Ukku Hasan, Husaini, Muh'd, Wannan kuma karyane, bayyanannen tarihi ya nuna cewa cikinsu Hudun Biyu ne kawai sukai mulki Aliyu da Hasan, Hasanma daga karshe Murabus yayi ya bawa wanda yake ganin yafishi cancanta ya rike mulki.
4- An Siffanta Hasan da imani da biyayya amma sauran ko oho, Kenan Shi kadai ne Mai Imani da biyayya?
5- Zamu lura cewa: "Shin abunda yafi komai muhimmanci da daukaka, da bukatuwa a addini shine ake samun sabani akansa har ake samun rabuwar kai?", kenan Imamancin ma ra'ayine Mutum yana bin Ra'ayinsa Ne, Mun sani cewa Imani da Sallah da zakka, azumi hajji, duk sun fishi domin ba'a samu Irin wannan Batar Ba a wurin fahimtarsu da tabbatar dasu da rabuwar kai.
.
(Zan cigaba Insha Allah)
Ibrahim Yunusa Abu-Ammar
08/12/1438H - 30/08/2017
Ko kasan? /1
Subscribe Our Channel