HAKIKANIN YABON DA MALAMAN SUNNA SUKA YI WA SAYYID QUTUB (1)
HAKIKANIN YABON SHAIKH IBNU BAAZ GA SAYYID QUTUB
Babbar shubuha da ake yadawa don hana mutane su fahimci hatsarin Fikrorin Sayyid Qutub, wanda Fikrorinsa ne suka haifar da Tunanin Ta'addanci a wannan zamani, har aka samu bayyanar Kungiyoyin Ta'addanci irin su Boko Haram, kuma har yanzu Fikrorin nasa ba su gushe ba suna tasiri a kan tunanin matasa masu kishin Addini, akwai cewa: ai Manyan Malamai sun yabe shi.
To alal hakika duk mai hankali da ilimi ya san cewa; wannan ba shi ne abin da zai ba da kariya wa Munanan Fikrorin Sayyid Qutub ba, saboda Malaman nan suna da uzuri, saboda ba su san hakikanin abin da ke cikin Littatafansa ba.
Amma duk wanda ya san ra'ayoyin 'Yan Bidi'a, kuma ya bude littatafan Sayyid Qutub ya karanta, to lallai zai iya cewa: galibin Bidi'o'in Kungiyoyin Bidi'a akawi su a cikin littatafan nasa, hatta littatafan da aka ruwaito cewa; a karshen rayuwarsa ya zabe su a matsayin wadanda ya yarda da su.
Misali idan ka dauki: "Fi Zilalil Qur'an", da "Ma'alim Fi al-Dareeq" babu abin da za ka gani a ciki sai kafirta al'umma, da cewa: duka Musulmai sun yi ridda, sun bar Addini, sun koma Jahiliyya.
Ka ga wannar Akidar Khawarijawa ce.
Haka idan ka duba "Fi Zilal..", ka duba Ayoyin Siffofin Allah, babu abin da za ka gani sai kore siffofin Allah da Tawilinsu, irin yadda 'Yan Bidi'a suke yi.
Da sauran Bidi'o'i na Kungiyoyin Bidi'a daban – daban.
To amma sai dai Shaikh Ibnu Baaz ya sarraha cewa; bai karanta littatafansa ba sai abu dan kadan kawai a cikin Tafsirinsa.
To yanzu, shin yabon Ibnu Baaz gare shi - alhali ya ce bai karanta littatafansa ba - zai kare shi daga alhakin Ta'addancin da Fikrorinsa suka haifar, na bullar Kungiyoyin Ta'addanci, masu kafirta al'ummar Musulmi, suna kashe su?!
An tambayi Ibnu Baaz a kan wata fassara da Sayyid Qutub din ya yi ma wata Aya a cikin Tafsirin nasa sai ya ce:
((ما قرأت تفسير سيد قطب وإنما قرأت شيئا منه، والتفسير عظيم ومفيد ولكنه لا يخلو من أخطاء ومن أغلاط، ولكني لا أذكر الآن شيئًا يتعلق بما سألت عنه يحتاج إلى مراجعة)).
((Ban karanta Tafsirin Sayyid Qutub ba, kawai abu kadan na karanta a cikinsa. Tafsirin Mai girma ne, yana da fa'ida, sai dai ba zai tsira daga kurakurai da galadi masu yawa ba, amma yanzu ba zan iya tuna wani abu da yake da alaka da abin da ka tambaya a kansa ba, yana bukatar a yi muraja'a)).
Duba nan:
https://binbaz.org.sa/fatwas/3327/%D8%AA%D9%81%D8%B3%D9%8A%D8%B1-%D8%B3%D9%8A%D8%AF-%D9%82%D8%B7%D8%A8-%D9%81%D9%8A-%D8%A7%D9%84%D9%85%D9%8A%D8%B2%D8%A7%D9%86
A wani wajen ma ya fadi magana irin wannar kamar haka:
((ما قرأته، قرأت منه شيئًا يسيرًا، فيه بحوث طيبة ولكن ما قرأته كله، ويقول بعض الناس: أن فيه بعض الأخطاء من جهة الصفات من طلاب العلم الذين قرؤوه، وقل أن يسلم كتاب فكل كتاب خلا كتاب الله جل وعلا قل أن يسلم من بعض الانتقادات وبعض الأخطاء، ولكن مثل غيره يؤخذ ما فيه من الطيب والفائدة الطيبة وما أخطأ فيه يترك خطأه))
Ma'ana; ya ce: Bai karanta littafin ba sai dan kadan. Akwai abubuwa masu kyau a cikinsa. Amma wani cikin mutane yana cewa; akwai kurakurai a Babin Siffofin Allah. Sai kuma ya nuna cewa: kowane littafi ba ya rabuwa da kurakurai, amma kamar kowa, za a karbi mai kyau dinsa, kuma za a yi watsi da munanan da suke ciki.
Duba nan:
https://binbaz.org.sa/fatwas/1546/%D8%AA%D9%82%D9%88%D9%8A%D9%85-%D8%AA%D9%81%D8%B3%D9%8A%D8%B1-%D8%B3%D9%8A%D8%AF-%D9%82%D8%B7%D8%A8
To don haka ta yaya wasu za su tayar da hankulansu don ana bayyana munanan Fikirorin da suke cikin littatafan nasa, don a yi watsi da su?!
Kuma akwai wuraren da aka karanta masa daga littatafan mutumin, ya soke shi. Daga ciki an karanta masa Tawilin da ya yi ma Ayar "Istiwa'in Allah a kan al-Arshi", sai aka tambaye shi a kan haka, bayan an karanta masa maganar tasa sai Ibnu Baaz din ya ce:
((كله كلام فاسد...، معناه إنكار الاستواء المعروف وهو العلو على العرش وهذا باطل يدل على أنه مسكين ضائع في التفسير)).
((Duka magana ce batacciya…, ma'anar maganar tasa shi ne inkarin Istiwa'in da aka sani, wanda shi ne daukakar Allah a kan al-Arshi, wannan bataccen ra'ayi ne, yana nuna cewa; shi miskini ne, batacce a Tafsiri)).
Duba nan:
https://www.youtube.com/watch?v=dWV4V3pxYrk
Idan wani zai ce: ai waccar magana ta Sayyid Qutub tana cikin littafin da bai yarda da su ba ne, to ga irinta a cikin "Fi Zilalil Qur'an" kamar haka:
((«ثُمَّ اسْتَوى عَلَى الْعَرْشِ» ..
والاستواء على العرش. كناية عن مقام السيطرة العلوية الثابتة الراسخة، باللغة التي يفهمها البشر ويتمثلون بها المعاني، على طريقة القرآن في التصوير (كما فصلنا هذا في فصل التخييل الحسي والتجسيم من كتاب التصوير الفني في القرآن) .
و «ثم» هنا ليست للتراخي الزماني، إنما هي للبعد المعنوي. فالزمان في هذا المقام لا ظل له. وليست هناك حالة ولا هيئة لم تكن لله- سبحانه- ثم كانت. فهو- سبحانه- منزه عن الحدوث وما يتعلق به من الزمان
والمكان. لذلك نجزم بأن «ثم» هنا للبعد المعنوي، ونحن آمنون من أننا لم نتجاوز المنطقة المأمونة التي يحق فيها للعقل البشري أن يحكم ويجزم. لأننا نستند إلى قاعدة كلية في تنزيه الله سبحانه عن تعاقب الهيئات والحالات، وعن مقتضيات الزمان والمكان)).
في ظلال القرآن (3/ 1762 - 1763).
Ka ga wannar magana, duk wanda ya karanta ta, kuma ya san Akidar 'Yan Bidi'a, cikin Jahamiyya da Mu'utazila zai san cewa; wannar Akidarsu ce Sayyid Qutub ya tabbar a nan.
Yanzu duba maganar Zamakhshariy Bamu'utazile a nan:
((لما كان الاستواء على العرش وهو سرير الملك مما يردف الملك، جعلوه كناية عن الملك فقالوا: استوى فلان على العرش يريدون ملك وإن لم يقعد على السرير البتة)).
تفسير الزمخشري = الكشاف عن حقائق غوامض التنزيل (3/ 52)
Ka ga kamar yadda Bamu'utazile Zamakhshariy ya ce: "Istiwa'i" (كناية) ne, haka shi ma Sayyid Qutub ya fada.
To amma matsalar ita ce; su masu kare shin, ba su san Akidar 'Yan Bidi'an ba, balle har su san cewa: Akidar Bidi'a Sayyid Qutub ya tabbatar a nan. Kai, wadanda suka fi kowa rashin mutunci da zagin mutane a kan Sayyid Qutub, idan ka ba shi wannar maganar, ka sa shi a gaba, ka ce: ya karanta maka ita, ya yi maka bayanin abin da take nufi, ba zai iya ba. Amma ya fi kowa rashin kunya da zage - zage.
To yanzu Sayyid Qutub mai irin wadannan Akidu ne har za a samu masu danganta kawunansu ga Ahlus Sunna suna ta tayar da jijiyar wuya a kansa, suna ta kare shi ido rufe?!
A takaice: maganganun yabo da Shaikh Ibnu Baaz ya yi ma Sayyid Qutub ba su da alaka da Miyagun Akidunsa da Munanan Fikrorinsa masu haifar da tunanin ta'addanci. Kuma Shaikh Ibnu Baaz din - bayan ya tabbatar da cewa; bai karanta littatafan nasa ba -ya yi nuni da a yi taka-tsam-tsam da littatafan nasa, idan an ga dadai a ciki a dauka, barna da suke cikin littatafan kuma a yi watsi da su.
Kuma abin mamaki, wadanda ba sa so a bayyana barnar da Sayyid Qutub ya shuka, har ya haifar da Kungiyoyi irin su Boko Haram, suka zo suna kare shi ta hanyar kafa hujja da maganar Shaikh Ibnu Baaz, da Dan Kungiyar Salafiyyun zai kawo musu maganar Ibnu Baaz inda yake yabon Shaikh Rabee'i al-Madkhaliy ba za su karba ba.
A takaice; salon da Mabiya Sayyid Qutub suke bi don boye barnarsa kawai salo ne na zabi sonka wa maganagnun Malamai, shi ya sa ba sa kawo inda Shaikh Ibnu Baaz da sauran Malaman suka soki Sayyid Qutub a kan barnar tasa. Kuma idan 'Yan Kungiyar Salafiyyun sun kawo musu maganar Ibnu Baaz ta yabo ga Shaikh Rabee'i ba za su karba ba. Ka ga wannan kawai ta'assubanci ne, da daure ma karya gindi.
Saboda haka a bisa hakika maganganun Ibnu Baaz da wadancan suke yadawa, hasali suna nuni ne a kan cewa; Littatafan Sayyid Qutub suna bukatar rariya, don tantance barnar da ya rubuta a cikinsu. Kuma maganganun na Ibnu Baaz ba sa kore Tabbatar ma Sayyid Qutub munanan Fikrorinsa da suke barna a bayan kasa a wannan zamani, ta hanyar haifar da Kungiyoyin Ta'addanci irin su Boko Haram.
✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
27 October, 2021