Subscribe Our Channel

 *Kyautata wa mutane kala biyu ne:*


Akwai kyautata wa mutane saboda mutuntaka da jin kai da tausayin mutane, wanda ake kira kyautata wa mutane saboda "Insaniyya" (Humanity). Irin wannan ne Mulhidai, Kafirai da Munafukai cikin 'Yan Film, 'Yan Kwallo da masu kudi na Duniya suke yi, karkashin foundation da suke kafawa don tallafi (Gidauniyar Tallafa wa Gajiyayyu). Wato ba suna yi ne don Addini da neman lada a wajen Allah ba.

Irinsa ne Allah ya ce:

{وَقَدِمْنَا إِلَى مَا عَمِلُوا مِنْ عَمَلٍ فَجَعَلْنَاهُ هَبَاءً مَنْثُورًا } [الفرقان: 23]


Ma'ana; duk aikin kirki da kafirai za su yi aikin banza ne kawai, ba zai amfane su a Lahira ba.


Kuma irinsa ne wanda 'Yan Boko Aqida suke yabawa da zuzutawa, saboda don humanity aka yi ba don Addini ba. Saboda a wajensu humanity ne abin birgewa ba Addini ba.


Akwai kuma kyautata wa mutane saboda jin kai da tausayin mutane, bisa bin umurnin Allah da neman yardarsa da neman lada a wajensa.

To irin wannan shi ne wanda Muminai suke yi, kuma shi ne aikin alheri, domin zai gadar da rabo wa Mumini a Duniya da Lahira.


Saboda haka muke kira ga dukkan 'yan uwanmu Musulmai, a kullum in za su kyautata wa mutane su yi aikin kirki, to su yi kokari ya zama aikin alheri, wato aikin neman lada da neman yardar Allah, kuma don bin umurnin Allah da Shari'arsa, tun da shi ya yi umurni da kyautata wa mutane, kuma ya shar'anta hakan, kuma ya tanadi lada da sakamako mai girma a kan hakan.


Don haka muna fatan Allah ya shiryi Musulmai suna yin aiyukan kirki don Allah don neman yardarsa, ba saboda "insaniyya" (Humanity) kadai ba, ba kuma don neman yardar mutane ko riya da neman suna ba.


Lallai duk wanda ya yi aiki na kwarai, alhali shi Mumini ne to zai yi rayuwa ta jin dadi, kuma Allah zai yi masa sakamako mai girma a Ranar Lahira.


Saboda haka wannan shi ne ma'aunin aikin kowane Musulmi, in ya yi don Allah, kuma ya kyautata wa mutane daga dukiya ta halas to Allah zai karba. In kuma ya zama sabanin haka to lallai ba shi da komai a wajen Allah.


Allah ya shiryar da mu gaba daya, ya ba mu ikon kyautata wa mutane bisa ikhlasi da neman yardar Allah.


✍️ *Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)*

       *24 October, 2019*

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter