Subscribe Our Channel

 An samu guluwwi a cikin wannar al'umma ne daga bangarori guda biyu:


1- Rafidha 'Yan Shi'a da suke bai ma Annabawa da Imamansu cikin Ahlul Baiti Matsayin Allah.


2- Jahilan Sufaye da suke bai ma Annabawa da Shehunansu Matsayin Allah.


Alhali duk wanda ya bai ma wani halitta Matsayin Allah ta fiskar bauta ko ta fiskar Rububiyya da halitta ko gudanarwa to ya yi kama da Kiristoci da suke bai ma Annabi Isa (as) matsayin Allah a komai, har suke cewa; Allah uku ne.


Alhali Allah ya yi bayanin hakkokin Annabawa cikin Alkur'ani da Sunnar Manzonsa (saw). Ayoyi da yawa sun zo sun yi bayanin wadannan hakkoki, musamman hakkokin Annabi (saw).

Daga ciki:

1- Imani da shi.

2- Sonsa fiye da kowa da komai, har fiye da kanka.

3- Girmama shi da sanin matsayinsa na Annabta da Manzanci.

4- Gaskata shi a dukkan labari da ya bayar.

5- Yi masa da'a a dukkan umurni da hani da ya yi.

6- Gabatar da hukuncinsa a kan hukuncin kowa, da yarda da hukuncin.

7- Taimakonsa da karfafa shi.

8- Bin Sunnarsa da taimakonta da yada ta, da gabatar da ita a kan ra'ayin kowa.

9- Yi masa Salati da Sallama.

10- Girmama shi wajen kiran sunansa.

11- Son iyalan gidansa; matansa, zurriyarsa da danginsa, da kuma sauran Sahabbansa.


Da sauran hakkoki da suka zo cikin Alkur'ani da Sunna.


Saboda haka guluwwi a kan Annabi (saw) ba shi da alaka da sonsa ko binsa, kamar yadda wasu suke zato.


✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

      28 October, 2018

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter