Subscribe Our Channel

 Idan Allah ya albarkaceka da gina karatunka akan ta'sili ingantacce na ilimi to ka godewa Allah. 


Wasu yan uwanmu daliban ilimi lamarinsu ze ba ka tausayi gami da ba ka takaici ; wani ze lazimta ma ka dacewa da shi acikin komai a harkar mas'aloli na ilimi , duk da cewa kun sha banban ta fuskar mashayar ilimi , shi abun da ya dauka ilimi shine kiyaye matsayar wani sashe na malamai na zamani acikin mas'aloli na addini , don haka shi harkar iliminsa kullum tana nan acikin fatawowin Malamai na zamani , ba ya da hunkoro akan isa zuwa ga dalilai na mas'lolin addini , kuma ba shi da basira wurin tantance zare da abawa yayin sabanin Malamai acikin mas'aloli na addini . 

Kai kuma ka san matsayar malamai na da da na yanzu akan wasu mas'alolin , kuma dede gwargwado ka san dalilai na shari'a akan mas'alolin , kuma kana iya yin nazari na ilimi akan dalilan har ka iya tantance zare da abawa acikin zantukan malamai mabanbanta . To a haka se ka ga wancan 'dalibin na matakin farko se ya yi qoqarin lazimta maka dacewa da shi acikin duk matsayoyansa a harkar ilimi , bisa hujjar cewa wai ai shi madogararsa akan matsayarsa itace wasu malamai na zamani , ze iya wuce iyaka akanka idan ka saba ma sa , idan tsautsayi ya ratsa ze iya jifanka da rena malamai da sauka daga tafarkin magabata ! 


Wata rana wasu mutum biyu su na magana akan mas'alar ha'de Sallah saboda ruwan sama , ni kuma ina gefe ina sauraronsu , dukkansu madogararsu akan matsayarsu acikin mas'alar shine Shaikh wane ya ce , dukkansu sun dogarane da fatawar wani babban Malami na zamani akan mas'alar , kuma so su ke yi ni ma in dace da su akan matsayarsu da madogararsu , alhali ni alokacin na kiyaye Hadisan da su ka zo akan mas'alar, kuma na kiyaye ingantattunsu da masu rauninsu , kuma na san illolin masu raunin , sannan na san i'itiradat da a ka yi akan manuniyar Hadisan akan mas'alar , sannan kuma na san mazhabobin Malaman Fiqhu akan mas'alar . Amma fa a haka su wadancan mutanen so su ke idan zan yi magana akan mas'alar to in yi magana acikin mas'alar irin yanda su ma su ka yi ; in dace da su ta fuskar matsaya da madogara ! Duk da cewa madogararsu ba madogara bace ta ilimi da shari'a , amma ahaka suke so su lazimtawa waninsu tsayuwa akanta .


Hakanan wata rana wani shima yana magana akan Hadisin Ibnu Abbas , hadisin da yake magana akan ramakon azumi ga wanda ya mutu , bayan ya kawo hadisin se ya ce : Amma Lajnatud da'ima ta ce azumin alwashi kawai za a rama " !


Ya kawo hadisi gamamme , amma se ya kebanceshi da Lajnatud da'ima ! 


Yau da cewa ya yi : Mazhabar Hambaliyya , ko Imamu Ahmad , ko wasu magabata su na ganin cewa azumin alwashi ne za a rama amma banda na Ramadana " to da hakan ya dan fi sauqi_sauqi . 

Shima wannan se de ka kame baki ka qyaleshi kawai , idan ka ce za ka warware mas'alar to ba lalle bane a tashi lafiya ; yana iya jifanka da rena manyan Malamai , ko ya jefeka da sauka daga hanyar magabata , ko ya ce kana ji da kanka , ko girman kai , lefinka shine : ba ka tunani irin na shi , ba ka tasarrufi irin na shi , kai kuma uzurinka shine : banbancin da ke tsakaninku na ginin hanyar ilimi . 


Matsalolin suna da yawa , se de a yi ta haquri da juna

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter