Subscribe Our Channel

 ME YA SA AKE MAGANA KAN RA'AYIN FARFESA FANTAMI ?


Ba abu ne mara amfani ba bayyana saɓanin ra'ayin Farfesa Fantami kan carbi, domin da mara amfani ne shima Farfesan ba zai ce a zo a zauna kan abu mara amfani ba. Shi Farfesan shi ya tada maganar kuma ya soki masu akasin fahimtarsa.

Daga cikin fa'idar abin da zai sa a yi wannan maganar, shine shi Farfesa yayi wasu maganganun masu illa ga ɗaliban ilimi na Ahlussunna da kuma da'awar sunna wurin bayyana ra'ayinsa kan mas'alar, shi yasa ya dace a nazarci maganar ta sa. Maganganunshi na nuna :

1- Masu ganin bidi'a ne riƙe carbin, zafin kai ne ke kai su ga ɗaukar wannan matsayar cikin mas'alar. Wanda shi kansa Ferfesan ya faɗa wannan ra'ayin da yake suka da zafin kai itace fahimtar Albani da Bakar Abu Zaid, idan malam ya dogara da fatawar Usaimin da Bin Baz, da Fauzan meye laifin wanda ya dogara da fatawar Bakar da Albani kuma me yayi na zafin kai ?


2- Maganganun malam a kaikaice suka yake ga littafin Bakar Abu Zaid, shima madadin gugar zanar da yake yi ga littafin Bakar, ai kawai da sai ya wallafa nasa littafin babba ya yi wa wancan Kutayyib ɗin raddi.


3- Sukar masu saɓa masa da ƙananan shekaru, wanda hakan zai buɗe ƙofofin da 'yan ɗariƙu suka daɗe suna zagin Ahlussunna da su.


4- Suka da ƙarancin bincike da na ilimi, wanda illar hakan ba zai tsaya iya wannan mas'alar ba, zai dawo da sharri ga Ahlussunna har kan kusan dukkan mas'alolin da suka saɓa da 'yan ɗariƙu.


5- Malam mutum ne mai mabiya da yawa yanzu kuma sun fi yawa cikin awam, fatawarsa za ta sa jahilai shakka kan mas'alolin da ake ƙalubalantar 'yan bidi'a kansu, a riƙa ganin koyaushe ko jahilci ne, ko yarinta, ko ƙarancin ilimi da na bincike ke sa Ahlussunna saɓawa da 'yan ɗariƙa, musamman dama 'yan ɗariƙu sun daɗe suna jifan Ahlussunna da waɗannan maganganun. Haka kuma yanzu an samu wasu 'yan boko aƙida na sukar mutane da talauci, da nuna yanzu shi Farfesa yayi kuɗi ya daina zafin kan riƙo da aƙidu da fahimtocin Ahlussunna.


A taƙaice dai illoli, da damar wulaƙanta da raina ɗaliban sunna da maganar Farfesa za ta jawo ita tasa ake magana kan Fatawarsa ba wai don matsayar da ya ɗauka ba. Muƙabalar kuma da Farfesan ya gayyata ita ta fi komai zama abu mara amfani a maganar.


Dr. Abdulmalik Sani

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter