Allah ya aiko Annabi (saw) ya umurce shi da isar da sako. To shi ya gama aikinsa ya isar da sako, ya rage namu mu gaskata shi, mu mika wuya, mu yi masa biyayya, kamar yadda Imamu Zuhriy ya fada:
«من الله الرسالة، وعلى رسول الله صلى الله عليه وسلم البلاغ، وعلينا التسليم»
صحيح البخاري (9/ 154)، صحيح ابن حبان - مخرجا (1/ 414)
Daga cikin Aqidar Ahlus Sunnati wal Jama'a, duk Hadisin da ya inganta daga Annabi (saw) to haka za a bar shi kamar yadda ya zo bisa ma'anarsa, bisa yadda Allah da Manzonsa suke nufi. Wannan ya sa Ahlus Sunna ba sa shisshigi wajen tawili da murde ma'anarsa da canza ta, kawai don ta saba ma son ransu. A'a, su ba sa haka, wannar hanya ce ta 'Yan Bidi'a, masu gabatar da abin da suke so a kan maganar Allah da Manzonsa (saw).
Ahlus Sunna suna mika wuya ga maganar Allah da Manzonsa ne saboda babu mai kubuta a Addininsa sai wanda ya mik'a wuya ga Allah da Manzonsa, ya mayar da abin da ya rikice masa zuwa ga masu iliminsa.
Lallai mika wuya ga Allah shi ne hakikanin Muslunci, Imamu Dahawiy ya ce:
ولا تثبت قدم الإسلام إلا على ظهر التسليم والاستسلام
متن الطحاوية بتعليق الألباني (ص: 43)
"Muslunci ba ya tabbata ga bawa sai a kan doron mik'a wuya da karban Addini daga Allah da Manzonsa".
Saboda haka gaskata Allah da Manzonsa da mik'a wuya gare su shi yake samar da girmama Allah da umurninsa da haninsa. Imani ba ya samuwa sai da girmama Allah, girmama shi kuwa ba ya samuwa sai da girmama umurni da haninsa da gaskata labarin da ya bayar a Littatafinsa ko ta harshen Manzonsa (saw).
Saboda haka, hakikanin Muslunci shi ne gaskata Allah da mik'a wuya ga maganarsa da maganar Manzonsa, ba tare da kalubalantarsu da ra'ayi ko hankali ko mazhaba ko darika ko kungiya ko siyasa ba.