Subscribe Our Channel

 ALWALA’U WAL BARA’U (BARRANTA DA JIBINTA), Da hukunce-hukuncen mu’amala da kafirai da ‘yan bidi’a da fasikai


- (Wala’i) Jibinta a larabci shi ne so da taimako da kusanci, majibinci shi ne masoyi, aboki, mai taimako, wato kishiyar makiyi.

- (Wala’i) Jibinta a wajen malaman addini shi ne son muminai saboda imaninsu da taimakonsu da yi musu nasiha da tausayinsu da sauransu.

- (Bara’i) barranta a larabci shi ne nisantar abu da rabuwa da shi da fita daga sha’aninsa. 

- (Bara’i) barranta a wajen malaman adini shi ne kiyayyar makiya Allah cikin munafukai da kafirai da adawa da su da nisantar su, da yaƙan Kafiran yaƙi (Harbiyyun) a cikinsu gwargwadon iko.

- Jiɓinta da Barranta wajibai ne a addini kuma asulai ne manya cikin asulan Imani.

- Ana jiɓintar mumini ne wanda ba shi da dawwama a kan manyan zunubai.

- Idan mutum ya kasance yana dawwama a kan manyan zunubai Kaman cin riba, zina, gulma, take tufafi, da sauransu, to ana son shi gwargwadon biyayyarsa ga Allah kuma ana ƙin sa gwargwadon saɓon Allah da yake.


ƘAURACEWA MAI SAƁO


- Ana ƙauracewa musulmi MAI aikata saɓo idan ƙauracewan zai sa ya bar saɓon, kuma ba tare da shi ko waninsa ya koma aikata wani saɓon makamancin wannan ko sama da shi ba. 

- Idan ƙauracewan ba zai kara masa komai ba sai ci gaba da saɓon da kusantar mutanen banza ko wata ɓarnar makamanciyar wannan, to ba a ƙaurace masa.


MUNAFIKI


- Wanda ake tuhumar sa da munafunci, ana jiɓintarsa gwargwadon abun da yake bayyanawa na alheri kuma ana adawa da shi gwargwadon abun da yake bayyanawa na ɓarna . 

- Idan munafuncin mutum ya bayyana aka tabbatar masa da hukunci, to hukuncinsa a wannan babin irin hukuncin sauran kafirai ne, bayani a kai zai zo a gaba.


ƳAN BIDI’A


- ƴan bidi’a kamar Jahmiyya, ƙadariyya, Rafida, Asha’ira, da sauransu, sun rabu gida uku: 


1. Nau’i na farko shi ne wanda bidi’arsa ba mai kafirtarwa ba ce, amma yana kira izuwa gare ta, ko yana bayyana ta.


- Wannan wajibi ne a ƙi shi gwargwadon bidi’arsa. 

- Wajibi ne a ƙaurace masa. 

- Wajibi ne a yi adawa da shi a bisa ijma’in ma’abota ilimi. 

- Ba ya halatta a zauna da shi. 

- Ba ya halatta a tattauna da shi sai dai ga malami idan zai masa nasiha. 

- Ya halatta a mai sallama ko a amsa sallamarsa. 

- Ana so a bar yi masa sallama ko amsa masa, idan akwai maslaha a ciki, kamar in hakan zai sa ya bar aikata bidi’ar ko don a nuna wa wasu munin aikinsa. 


2. Nau’i na biyu shi ne mai aikata bidi’a mai kafirtarwa, kamar sufaye masu roƙon shehunnai da matattu, kamar rafidawa masu cewa an canja Alkur’ani ko akwai bangarensa da babu, ko masu neman agaji da matattu. 

- Irin wadannan idan aka tsayar musu da hujja aka tabbatar da kafircinsu su ma hukuncinsu irin na sauran kafirai ne, bayaninsa yana tafe. 


3. Nau’i na uku shi ne wanda ya kasance yana ɓoye bidi’arsa, ba ya kira izuwa gare ta, ba ya da’awar cewa aiki mai kyau ce, haka ba ya yabon ƴan bidi’a ko ƴaɗa shubuhohi tsakanin mutane don ƙarfafar bidi’ar.


- Wannan kamar mai sabo ne a ɓoye, ana zama da shi ana masa sallama (da sauran mu’amala), ba a ƙaurace masa.   


MUHIMMAN MAHALLAN JIBINTA HALATTACCIYA


1. Wajibi ne ga kowane musulmi ya so muminai karkaf ɗinsu na kowane wuri da zamani. Lallai musulmi ya guji ƙiyayya da wani mumini saboda duniya ko ɓangarancin ƙabila ko mazhaba ko saboda wani saɓani da ya gudana tsakaninsu.


2. Wajibi ne taimakon musulmi na kowane jinsi a duk inda yake idan aka zalunce shi, ta hanyar karfi da dukiya da alƙalami da harshe, a duk halin da yake buƙatar taimakon.


3. Wajibi ne taimakon musulmai da rai da dukiya sanda suka buƙatu izuwa ga hakan.


4. Wajibi ne jin ciwon duk abun da ya sami wasu musulmai na masifa da cuta, haka wajibi ne farin ciki da nasararsu da duk abun da yake alheri a gare su.


5. Akwai sauran abubuwa masu yawa da suke shiga cikin jiɓintar musulmai, cikinsu akwai farillan ainihi kamar amsa wa mai atishawa, kamewa daga cutar da su, da sauransu, akwai kuma farillan al’uma, kamar amsa sallama, hidimar gawa da yi masa salla, da’awa da karantarwa, da sauransu. 


MISALAN HARAMTACCIYAR JIBINTA


- Jibintar makiya Allah cikin Yahudu da Nasara da Majusawa da munafukai, da sauransu, ta rabu gida biyu. 

- Nau’in farko su ne masu fitarwa daga musulunci su mayar da mutum kafiri. 


MUHIMMAN MAHALLAN IRIN WANNAN JIƁINTAR


1. Zabar zama a garin kafirai da yarda da addininsu ko yabon sa, da taya su aibata musulmai, wannan ridda ne daga musulunci.


2. Mutum ya zama ɗan ƙasa (Jinsiyya/Naturalization) a kasar kafirai masu yaƙar musulmai, yana yarda da lazumtar dukka dokokinta da tsarukanta na tilasta mutane a aikin soja tana amfani da su wajen yakar musulmai.


3. Kamanceceniya da su gabagaɗi, shi ne mutum ya zama komai yana yi irin nasu, yana zama tare da su da zuwa wuraren bautarsu da bukukuwansu.


4. Kamanceceniya da su cikin abun da yake wajabta fita daga musulunci kamar sanya cross da aƙidar neman tabarruki da shi da yarda cewa an kashe Annabi Isa (A.S) an rataye shi.


5. Zuwa coci tare da ƙudurce cewa zuwan ibada ne.


6. Kira izuwa ga hadewar Addinai (Unification of Religion) ko kusantowar Addinai (Convergence of Religions).


7. Taimakon kafirai a kan musulmai ta hanyar yaƙar musulmai tare da su ko taimakon su da dukiya ko makami ko leƙeo musu asirin musulmai, sai dai idan ya yi hakan ne don wata maslahar kansa ko tsoron kafiran, ko wata adawa ta duniya tsakaninsa da musulmin da suke yaka, to wannan kaba’ira ne amma ba ya mayar da shi kafiri.  


- Nau’i na biyu na biyu na haramtacciyar jibinta shi ne wanda yake a matsayin babban zunubi amma ba ya kai wa ga kafirci.


MISALAI


1. Son kafirai da yin abota da su.

2. Zama na dindindin a kasar kafirai. 

3. Zuwa ƙasar kafirai ba tare da buƙata ko larurar zuwan ba, idan akwai buƙatar zuwan gare shi ko sauran musulmai, kamar kasuwanci, da’awa, neman magani, ya halatta ya je da sharaɗi uku.


- Ya zama yana da ilimin Addininsa

- Ya zama yana nesa da abubuwan da za su fitini Addininsa da dabi’unsa a ƙasar da zai je.

- Ya zama yana da damar bayyana Addininsa.


4. Taya su yin bukukuwansu na Addini Kaman Kirsimeti, New year, Easter ta kowace fuska haramun ne. 

5. Kamanceceniya da su cikin wasu abubuwa da suka keɓanta da su ko da kuwa asali ba haramtacce ba ne a Musulunci, kamar Al’adu, wani abu da suka riƙa a matsayin ibada, hanyar ci da sha da gini da zama da tafiya da gyaran jiki da sauransu. 

6. Barinsu suna bayyana Addininsu a ƙasashen musulmai

7. Riƙar su abokan shawara ko abokan sirri. 

8. Zama da su waje ɗaya saboda abota ko wata maslaha ta duniya. 


- Zama a kasar kafirai don karatu shi ma yana halatta ne idan ya cika sharuɗa hudu;


1. Mutum ya kasance yana da nunar hankali da hangen nesa.

2. Mutum ya kasance yana da ilimin da zai iya bambance gaskiya da karya da shi duk sanda aka cakuɗa su.

3. Mutum ya kasance yana da ƙarfin addinin da zai zame masa garkuwa daga fadawa kafirci da fasiƙanci.

4. Ya zama cewa akwai bukatar ilimin da ya je nema, misali al’umar musulmai tana bukatar wannan ilimin kuma ba ta da shi.


- Zuwa ƙasar kafirai yawon buɗe ido haramun ne kamar yadda ya tabbata a Hadisi. 


ABUN DA YA WAJABA GA MUSULMAI CIKIN MU’AMALA DA KAFIRAI


- Kafirai sun rabu gida hudu:


1. KAFIRAN ALƘAWARI (MU'AHADUN): su ne waɗanda suke zaune a ƙasar musulmai bisa alƙawari da sulhu, kamar kafiran ƙuraishawa a lokacin sulhun hudaibiyya, haka kafiran ƙasashen da suke da alƙawuran shige da fice da sauransu da wasu ƙasashen musulmai. 


2. MASU RAYUWA A ƘARKASHIN ƘASAR MUSULMAI (ZIMMIYYUN): su ne kafiran da suke zaune a ƙasar musulmai bisa yarjejeniyar za su dinga ba da haraji (jiziya). 


3. KAFIRAN AMANA (MUSTA'AMANUN): su ne waɗanda suke shiga ƙasar musulmai bisa amincewar shugaban musulmai ko wani cikin musulmai.


4. KAFIRAN YAƘI (HARBIYYUN): su ne waɗanda ba sa cikin nau’i ukun da ambaton su ya gabata, su ne kuma waɗanda aka shar’anta wa musulmai yaƙi da su gwargwadon iko.


- Abubuwan da suke wajaba ga kafiran da ba na yaƙi ba a kan musulmai su ne kamar haka:


1. Kafiran alƙawari da na amana a ba su kariya sanda suke zaune a ƙasar musulmai, sannan kafirin amana a ba shi kariya sanda zai fita daga ƙasar musulmai har sai ya je inda zai samu aminci.

2. Yi musu adalci yayin hukunci a kansu ko yi musu hukunci a tsakaninsu ko tsakaninsu da musulmai.

3. Kiransu zuwa ga musulunci, wannan farilla ne na al’uma da wasu suke ɗauke wa wasu.

4. Haramun ne a tilasta su su canja addininsu. 

5. Haramun ne musulmi ya yi ta’adi ga wani cikin kafirai banda kafiran yaki (Harbiyyun). 

6. Haramun ne Musulmi ya cuci wani cikin Kafirai banda Kafiran yaƙi , cikin saye da sayarwa, ko ya ɗauki wani abu cikin dukiyarsu ba tare da haƙƙi ba, kuma wajibi ne ya cika musu amana. 

7. Haramun ne Musulmi ya munana mu’amala ga wani cikin Kafirai banda kafiran yaƙi, ko ya masa ƙarya . 

8. Wajibi ne ga wanda ya haɗa maƙotaka da su ya kyautata musu irin kyautatawar maƙotaka .

9. Wajibi ne idan sun yi wa musulmi sallama ya mayar musu.


ABUN DA YAKE HALATTA GA MUSULMAI CIKIN MU’AMALA DA KAFIRAI


1. Ya halatta a tausasa musu zance da mu'amala, kamar kiran kafiri da alkunyarsa, a binciki halin da yake ciki da iyalansa, taya shi murnar haihuwa, fara gaishe da shi (ba da sallama ba), saboda wata maslaha ta shari’a kamar kwaɗaitar masa da musulunci ko tunkuɗe sharrinsa ko janyo wani amfani halattacce.


2. Ya halatta a ɗauke su aiki ko leburanci wanda babu jiɓinta a garesu a cikinsa ko ɗaukaka su a kan musulmai.


3. Ya halatta a ci abinci da su idan ta kama (kamar idan gayyata ta haɗa ko baƙunta), ba tare da an riƙe su abokan mu’amala ko abokan cin abinci ba na yau da gobe.


4. Ya halatta a yi mu’amala da su cikin al’amuran duniya da suke halattattu a shari’a.


5. Ya halatta musulmi ya auri Bayahudiya ko Banasariya kamammiya idan ya aminta daga sharrinta a kan addininsa da dukiyarsa da ‘ƴaƴansa.


6. Ya halatta musulmai su nemi taimakon kafirai wajen tunkuɗe wata adawa ga musulmai da sharaɗi biyu:


- Idan ya zama ba wata mafita sai wannan.

- Idan an amintu daga makircinsu.


7. Ya halatta musulmi ya je neman magani wajen amintaccen likita kafiri.


8. Ya halatta a ba da zakka ga waɗanda zuciyoyinsu suka ɗamfaru da musulunci daga cikin kafirai.


9. Ya halatta musulmi ya yi kasuwanci da su da sharaɗin ya zama yana da cikakken iko a kan tasarrufinsa a cikin kasuwancin saboda gudun faɗawa cikin mu’amalar haram idan ya kasance kafirin ne yake juya komai.


10. Ya halatta a karɓi kyautar kafiri idan babu kasƙantar da musulmi a cikinta.


11. Ya halatta musulmi ya yi aiki a ƙarƙashin kafiri ko aikin da kafiri yake jagoranta, amma ba ya halatta ya zama mai yi wa kafirin hidima a karan kansa (kamar mai gadi, yaron gida, da makamantansu), saboda a cikinsu akwai ƙasƙantarwa ga musulmin.


ABUNDA AKA KWAƊAITAR (MUSTAHABBI) GA MUSULMI CIKIN MU’AMALA DA KAFIRAI


1. An kwaɗaitar a dinga kyautata musu ta hanyar sadaka da kyauta da yi musu nasiha.

2. An kwaɗaitar da sa da zumunci ga makusanci kafiri, kamar iyaye da ‘ƴan'uwa ta hanyar kyauta da ziyara da makamantansu.

3. An kwaɗaitar da karrama su idan suka baƙunci musulmi.


Daga littafin Alwala'u wal Bara'u na Shaikh Abdullahi bin Abdulaziz Aljibrin 

Fassara da Taƙaicewa: Mallam Bahaushe 16/10/2023

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter