Subscribe Our Channel

 Menene "Wajibul Waqti" a yanzu?


Dr. Yusuf Qardhawiy babban masanin "Fiqhul waqi'i" ya ba mu amsar wannar tambaya, a inda yake bayani a kan Fikrorin Sayyid Qutub, ya ce:

((وهي أفكار انفرد بها في ساحة الدعوة، ويخالفه فيها جمهرة العلماء والدعاة الإسلاميين في مصر، وفي غيرها من العالم العربي والعالم الإسلامي.


ومن أبرز هذه الأفكار وأشدها خطرا وأبعدها أثرا: فكرة "تكفير المسلمين الموجودين في العالم اليوم"، إلا فئة قليلة جدا منهم. أما مئات الملايين في العالم الإسلامي – الذين يظنون أنفسهم "مسلمين" أو يحبون أن يكونوا "مسلمين" – فهم ليسوا من الإسلام في شيء، وإن كانوا يشهدون أن "لا إله إلا الله"؛ لأنهم يفهمونها على غير مدلولها الحقيقي الذي لا معنى لها – في نظره – غيره، وهو الذي يتضمن معنى "الحاكمية"، بل لا يغني عنهم أن يكونوا من المصلين والصائمين والمزكين وحجاج بيت الله الحرام!


ومن هنا لا يتحدث عن الحكام وحواشيهم، كما يزعم بعض الناس، بل يتحدث عن "مئات الملايين" من المسلمين، أو ممن يظنون أنفسهم مسلمين. والحكام ومن حولهم إنما هم ألوف من الناس لا ملايين ولا عشرات الملايين.


هذه الفكرة الخطيرة التي فتحت أبواب التكفير والعنف واستباحة الدماء والأموال من المسلمين، وقامت عليها – في أوطاننا الإسلامية – جماعات تقاتل قومها، وتحارب أهل وطنها، هي الجديرة بأن يقف العلماء والدعاة في وجهها، ويتصدون لبيان ما فيها من انحراف عن الأحكام الشرعية المقررة. ويبينوا بطلانها بالأدلة من كتاب الله وسنة رسوله صلى الله عليه وسلم، مسترشدين بأقوال الأئمة الراسخين من علماء السلف والخلف)).

ابن القرية والكتاب (3/ 487 - 488)


((Fikrori ne wadanda Sayyid Qutub ne ya kadaita da su a fagen da'awa, shi kadai ya fara bayyana su, Jamhurin Malamai da masu da'awa a Misra da wajenta a kasashen Larabawa da Duniyar Muslunci gaba daya sun saba masa a kansu.


Daga cikin manya wadannan Fikrori nasa, kuma mafi bayyana, kuma mafi girman hatsari, kuma tasirinta yake da nisan zango ita ce: Fikrarsa ta "KAFIRTA MUSULMAN DA SUKE RAYUWA A YAU A FADIN DUNIYA", sai 'yan kadan ya ware ya ce su ne kadai Musulmai. Amma daruruwan Miliyoyin Musulmai da suke kasashen Musulman Duniya - wadanda suke zaton kawunansu a matsayin Musulmai, ko suke so su kasance Musulmai - a wajensa ba su da alaka da Muslunci a komai, ko da kuwa suna shaidawa da Kalmar Shahada: "Babu abin bauta da gaskiya sai Allah", saboda a ganinsa sun fahimci Kalmar ce ba bisa ma'anarta na hakika ba, ma'anar da babu wata ma'ana sai ita kadai. Ita ce ma'anar da ta kunshi ma'anar "HAKIMIYYA". Kai, a ganinsa kasancewarsu masu Sallah, masu ba da Zakka, masu yin Aikin Hajji duka ba zai wadatar da su komai ba, duka aikin banza suke yi.


A nan fa ba a kan Masu mulki da fadawansu yake magana ba, kamar yadda wasu mutane suke raya hakan ('Yan tawili), a'a, yana magana ne a kan "Daruruwan Miliyoyi" na Musulmai, ko wadanda suke zaton su Musulmai ne. Ai su Masu mulki da wadanda suke kewaye da su, ai su sai dai a kirga su da Dubunnai kawai, ba Miliyoyi ko Daruruwan Miliyoyi ba. 


Wannar Fikra mai hatsari, wacce ta bude kofofin kafirta Musulmai da ta'addanci da halasta jinane da dukiyoyin Musulmai, kuma AKA SAMU KUNGIYOYI A KANTA – A KASASHEN MUSULMAI – SUNA KASHE MUTANE, SUNA YAKAR 'YAN KASASHENSU, ita ta fi cancanta Malamai da masu da'awa su tashi tsaye su tare ta, su tinkare ta don bayanin abin da ke cikinta na karkacewa daga hukunce - hukuncen Shari'a tabbatattu, su bayyana bacinta da dalilai daga Littafin Allah da Sunnar Manzonsa (saw), suna masu nusarwa ta hanyar amfani da maganganun Malamai tabbatattu a ilimi, cikin Malamai Magabata da na baya)).


Wannan shi ne bayanin da Dr. Qardhawiy ya yi a kan Fikrorin Sayyid Qutub na kafirta al'umma da bayanin hatsarin hakan.


Saboda haka duk mai neman "Wajibul waqti", wato abin da ya wajaba a kan Malamai da masu da'awa su tashi tsaye su tinkare shi, su yake shi a wannan lokaci to ga nan babban Masanin Fiqhul Waqi'i ya ba shi amsar cewa; "Wajibul waqti" shi ne tona asirin Fikrorin Sayyid Qutub da bayanin bacinsu, na kafirta kowa da kowa, wadanda suka haifar da Kungiyoyin Ta'addanci masu halasta jinanen Musulman Duniya, suna kashe su a ko'ina a fadin Duniya.




 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter