Subscribe Our Channel


Shin Sayyid Qutub Shaidan ne?!


Wato lamarin Sayyid Qutub a wajen masoyansa, kuma masu kare shi ido rufe zai ba ka mamaki matuka. Saboda yadda suka girmama lamarinsa, idan an soke shi kai ka ce: an taba wa masu bautan gumaka gunkinsu ne, ko masu bautar shaidan idan an taba masu shaidaninsu!


Dazu dan'uwa Malam Abu Abdillah Ahmad Sidi yake ba ni labarin irin cin mutuncin da ya gani daga wasu Mabiya Sayyid Qutub, kuma 'yan-a-mutun kare shi. Babu irin zagi da ja'iran hukunce - hukunce da bai sha a wajensu ba.


Sai wannan ya tuna mini cewa: Ai hatta 'Yan Kungiyar Ikhwan, har manyan jagororinsu ba su tsira ba a lokacin da suka soki Fikrorin Sayyid Qutub, a lokacin da suka tabbatar da cewa: Shi ne Madugun Masu Kafirta Musulmai kuma babban "Munazzir" na ra'ayoyin kungiyoyin Ta'addanci a wannan zamani.


Babban misali shi ne Dr. Qardhawiy, a lokacin da ya yi magana a kan haka, ya fiskanci suka da rashin mutunci daga Qutbawa, kamar yadda ya yi ishara ga hakan a rubutun nasa a kan Sayyid Qutub. Kawai don ya tabbatar da cewa: Sayyid Qutub shi ne Tushen Fikirar Kafirta Musulmai a wannan zamani, kuma Fikrorinsa ne tubalin gina Kungiyoyin Ta'addanci.


Shi ya sa Dr. Jasim Sultan, daya daga cikin 'Yan Harka, dan Kasar Qatar, ya bayyana wannar hakika, inda ya ce:

((الكلام عن الأستاذ سيد قطب محفوف بالمخاطر، فالرجل تأثر به كثير من البشر وأصبح مجرد التحدث عن أي قصور في فكرته - عند محبيه - تعرض لشهيد الإسلام، ولكن لا يمكن فهم الظاهرة الإسلامية من دون التحدث عن أهم شخصية أثرت وما زالت تؤثر في فكر الشباب الإسلامي)).

أزمة التنظيمات الإسلامية - الإخوان نموذجا (ص: 292)


((Magana a kan Ustaz Sayyid Qutub yana tattare da hatsarurruka masu yawa, mutumin mutane masu yawa sun tasirantu da shi, har aka wayi gari a wajen masoyansa, mujarradin yin magana a kan kuskure guda daya cikin Fikirorinsa to hakan suka ne ga Shahidin Muslunci. Amma sai dai ba zai yiwu a fahimci wani sabon abu da ya bayyana a cikin al'ummar Musulmi ba, ba tare da an yi magana a kan mutum mafi muhimmanci wanda ya yi tasiri, KUMA YAKE KAN YIN TASIRIN a kan tunanin Matasan Musulmai ba)).


A kasa zan saka hoton shafin littafin nasa, inda Dr. Jasim Sultan din ya yi wannar magana.


Saboda haka Malam Ahmad Sidi ka kara hakuri, ka san idan mutum ba shi da hujjan kwatan shugabansa, to kamar mahaukacin kare yake zama.


Don haka Ni Nasiha nake so na yi ma irin wadannan mutane, su tausaya ma kawunansu, su kwantar da hankulansu, domin magana a kan Sayyid Qutub, kan ne ya fito, gangar jikin yana baya.


Saboda haka za mu cigaba da bayani da iznin Allah. Muna addu'an Allah ya sa mu dace.
 


 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter