Subscribe Our Channel

 Daga shafin Abu Ahmad Ateeq Sulaiman Allah Ya saka mishi da alheri. 

hmmm lallai iilimi ba wasan yara ba ne!!!!! 


WANI WAJIBI DA BA KASAFAI AKE DAMUWA DA TABBATAR DA SHI BA ( TUNATARWA GARENI 'DALIBIN ILIMI ) 


Al'umma tanada tsananin bu'katar Malamai 'kwararru a fannonin ilimi , saboda wa'dannan Malaman sune fitilu na wannan Al'ummar ; sune suke haskawa mutane amintacciyar hanya ta Addini da rayuwa , da samuwarsu Al'umma take nagartuwa , da kuma rashinsu Al'umma take halaka ta shiga cikin yamutsi da tashin_tashina acikin Addini da rayuwa . 


Ga 'Dalibin da yake fatan ya zama Malami nan gaba , wanda al'umma zata ringa maida al'amuranta zuwa gareshi , to dolene 'Dalibin ya 'daura 'dammara domin bibiyan hanyoyi na gaskiya da zasu sadar da shi zuwaga wannan katafaren matsayi .


'Dalibin ilimi wajibine ya san dukkan littattai ababen dogaro wurin fahimtar dukkan fannona na ilimi , ya tabbatar ya karance wa'dannan littattafan karatu na fahimta domin kaiwa zuwa ga abunda yake fatan isa zuwa gareshi .


Zan 'dan yi ishara zuwa ga wasu fannona wa'danda mu anan Nigeria galibi ba'a koyon fannonan daga littattafai ababen dogaro a wa'dannan fannona :


Fannin lugah da Adab : a wannan fannin ya kamata 'dalibi ka karanta wa'dannan littattafai kamar haka : 


_ إصلاح المنطق لابن السكيت 

_ إصلاح غلط العوام لابن الأعرابي 

_ الفصيح لثعلب 

_ المثلث لقطرب 

_ الصاحبي في فقه اللغة 

_ القاموس المحيط 

_ قصيدة بانت سعاد 

_ المقصورة لابن دريد 

_ لامية العرب 

_ المعلقات العشر 

_ مقامات الحريري 

_ جوهرة الأدباء لابن دريد 


Wa'dannan littattafai da na ambata , dukkansu littattafaine sanannu awurin Malamai tuntuni , Su ake karantawa da makamantansu domin fahimtar wa'dannan fannoni .

Idan zai yi ga 'Dalibi , ya haddacesu gaba 'dayansu , ko kuma ya haddace wasu daga ciki , kamar :


* إصلاح المنطق 

* موطأة الفصيح ( نظم الفصيح لثعلب ) * المعلقات العشر 

* المقصورة لابن دريد .


Ammafa wa'dancan sauran littattafan wajibine ya yi it'kaninsu , ya lazimcesu 'kwarai da gaske .

Sannan kuma ya bibiyi sharhohinsu bayan ya gama kyautata fahimtar mattaninsu , kamar Sharhin Mu'allaqat na Ibnul A'araby , da Sharhin Alfasih na Zamakhshary , da dai sharhohi da Malamai Su ka yi ga littattafan .

Kada 'dalibi ya 'bata lokacinsa wurin karanta wasu littattafai wa'danda ba ababen dogaro bane awadannan fannona , kamar wa'dannan littattafan :


# همزية 

# بدماصي 

# عشرينية 

# طنطراني 

Su wa'dannan littattafai da makamantansu , ba sune ababen dogaro wurin fahimtar lugah na larabci , don haka Kada ka shagaltu da su ka bar abunda yake shine asali awurin Malamai ma'abota ilimi . 


Fannin balagah : ka karanta littattafai kamar :


_ التبيان في علم البيان للزملكاني 

_ التبيان في علم البلاغة للطيبي 

_موجز البلاغة لابن عاشور 

_ تلخيص المفتاح للقزويني 

_ مأة المعاني والبيان لابن شحنة الحلبي 

_ الجوهر المكنون للأخضري 

_ عقود الجمان للسيوطي 


Wa'dannan littattafan wajibine ka yi it'kaninsu , sanann kuma ka haddace na haddacewa , kamar Alfiyyar Suyudy U'kudul Juman . 

Sanann kuma ka bibiyi sharhohin Talkhisul Miftah bayan ka yi it'kanin wa'dannan mattanoni .


Kada ka kuskura ka ringa jin cewa _wai_ ka san balagah saboda ka karanta littafin "Albalagatul Wadiha " , maganar gaskiya itace : indai Shi ka karanta ka'dai , to ba zaka san gardi da lagwadan Al'qur'ani da Sunnah ba ta fuskan tadabburin abunda Su ka 'kunsa na ma'anoni . 


Daga cikin abunda zai 'kara maka tamakkuni acikin Balagah , karanta littattafan Malaman da su ke bada kulawa wurin fitar da fa'idoji na balagah daga cikin Alqur'ani ko Hadisi , kamar littattafan Al'allamah A'd'diby acikin Sharhinsa ga Almasabih na Bagawy , da Al'Imam Ashshaukany Acikin Rasa'il dinsa cikin majmu'ul fatawa dinsa( Alfathur rabbany ) , da Ibnu Ashur acikin littattafansa , kamar littafin Tafsirinsa da littafinsa " Annazrul Fasih " , da Ibnu Hajar cikin Fathul Bary , Da Al'Imam Alkhaddaby acikin Sharhinsa ga Sunan Abi Dawud , da Suyudy acikin wasu ke'bantattu wasiqunsa , kamar risalarsa akan Ayar Suratul Baqara " الله ولي الذين آمنوا " , da Sharhinsa ga Hadisin Niyyah , da Alkhadib Attiftazany acikin Sharhinsa ga Al'arba'unan Nawawiyyah , da Addufy acikin littafinsa Al'iksir da Sharhin Al'arba'un . 


Bibiyan littattafan Malaman da suke bada kulawa ga wannan janibin zai taimakawa 'dalibi wurin amfana da qa'idojin da ya koya daga wa'dancan mattanoni ta yanda zai san yanda ake aiwatar da su akan nassoshi da fitar da fa'idoji daga cikinsu .  


Fannin Sarfu : ka karanta littattafai kamar haka : 


_ متن البناء 

_ تلخيص لامية الأفعال

_لامية الأفعال 

_ أرجوزة التصريف 

_ الشافية لابن الحاجب

_ لامية الأفعال مع زيادات البحرق وابن زين 

_ القصيدة السجلماسية ( مبلغ الآمال ) 

_ التسهيل لابن مالك 


Anan mafi 'karancin abunda zaka haddace shine Lamiyyatul Af'aal Mai taushihin Bahraq da Ibnu Zain , sauran kuma sai ka yi it'kaninsu . 


 Fannin Hadisi : dolene ka karanci Alkutubus Sitta a gaban Malami , bayan ka gama da mattanoni na littattafan Hadisan hukunce_ hukunce kamar littafin Umdatul Ahkam 'karamin da babban , da Bulugul Maram , da littafin Almuharrar na Ibnu AbdilHadi ko kuma littafin Al'ilmam na Ibnu Daqiq . 


Shi ilimin Hadisi tekune Wanda bashi da gaci , don haka Shi zaka yita karatune kawai ba ji_ ba gani ; ka sanya aranka cewa sai ka karance dukkan littattafan da suka tattaro Hadisan Annabi daga dukkan nau'ukansu , tun daga kan masanid zuwa Sihah da Sunan da Jawami'u da dai sauran nau'ukan littattafan da suke 'kunshe da Hadisan Annabi . 


Dangane da mus'dalah , kada ka bata lokacinka wurin yawaita karanta littattafansa , ka wadatu kawai da yan kadan wa'danda su ka 'kunshi maqasudin Ilimin , kamar Nukhbatul Fikar , da Ulumul Hadis na Ibnus Salah , da Alfiyyah ta Suyu'dy da Sharhohinta , kamar Sharhin Al'allamah Alwallawy 'karamin Sharhinsa da babban .

Sai kuma Annukah na Ibnu Hajar da Zarkashy ga littafin Ulumul Hadis na Ibnus Salah .


Inda zaka fi bawa 'karfi shine littattafan Rijaal da Ilal na Hadisi , ka yawaita karantasu kwarai da gaske , su caku'de da kai tamkar jini da tsoka ; ya zamana idan ka ga Hadisi da Isnadinsa dukkan mazajen Hadisin ka sansu ba tare da buqatar komawa littattafan Rijaal ba a galibin halinka .


Da shagaltu da littafin Sharhin Ilalut Tirmizy na Ibnu Rajab , idan so samu ne ka haddace nazaminsa na Al'Allamah Wallawy ( ألفية علل الحديث ) 


Idan kanaso ka kware awurin sanin Fiqhun Hadisi da istinbadi acikinsa to ka lazimci littattafai kamar haka : 


 1 .إحكام الأحكام لابن دقيق العيد مع حاشية الصنعاني 

2. نيل الأوطار للشوكاني 

3. الإمام لابن دقيق العيد 

4. شرح الإلمام لابن دقيق 

5. معالم السنن للخطابي 

6. شرح سنن أبي دود لابن القيم 

7. فتح الباري لابن رجب وابن حجر 

8. المنهاج للإمام النووي 

9. شرح مسند الشافعي لابن الأثير 

10. التمهيد والاستذكار لابن عبد البر 

11. الأجوبة عن المسائل المستغربة لابن عبد البر 

12. شرح المصابيح للطيبي .


 Bayan haka , ka yi wa kanka al'kawarin cewa : wajibine ka karance dukkan littattafan Ibnu Hajar da Zahaby acikin Fannin ilimin Hadisi ka bajima ko ba da'de . 


Idan kanaso ka san sa'bani na Magabata acikin mas'aloli na addini tare da sanin madogaran kowane 'bangare daga Hadisan Annabi , to ka karanta wa'dannan Littattafai : 


1. المصنفات 

2. الأوسط لابن المنذر 

3. التمهيد والاستذكار لابن عبد البر 

4. السنن الصغرى والكبرى للبيهقي 

5. الخلافيات للبيهقي 

6. التحقيق لابن الجوزي مع شرحي ابن عبد الهادي والذهبي .


Fannin Qur'ani : ka haddaceshi gaba dayansa , ka karance littattafan da su ka yi bayanin ma'anonin 'dai'daikun ba'kin kalmominsa , kamar wa'dannan littattafai : 


1.غريب القرآن لابن قتيبة 

2.مشكل القرآن لابن قتيبة 

3. معاني القرآن للفراء 

4.معاني القرآن للأخفش 

5.مجاز القرآن لأبي عبيدة 

6. غريب القرآن لغلام ثعلب 


Idan zai yi wu ka haddace manzumar Ibnul Munayyir na Garibul Qur'an ( النظام العجيب في تفسير الغريب )


Daga nan ka kutsa cikin littattafan Attafsiru bil ma'athur gaba dayansu daki_daki .


Fannin Aqidah : ka karance littattafan da suke hikayar mas'alolin da Salaf Su ka hadu akansu daga cikin mas'aloli na Aqidah , kamar Dahawiyyah , da wasi'diyyah , da lum'atu li'itiqad da sauransu .

Sannan ka tsallaka cikin littattafan da suke ruwaito Aqidar Magabata acikin babuka na Aqidah , kamar littafin I'itiqadu Ahlussunnah na Lalika'iy , da Al'ibanah na Ibnu Ba'ddah , da Ashshari'ah ta Al'Ajurry , da Assunnah ta Ibnu Abi Asim da sauransu .


Daga nan kuma sai ka zo ka tare akan littattafan Ibnu Taimiyyah gaba 'dayansu wa'danda suke tattaunawa akan Aqida da ilmul firaq , kamar :


التسعينية

شرح الأصبهانية 

الانتصار لأهل الأثر 

منهاج السنة 

التدمرية

الحموية

الرد على الجهمية 

درء تعارض العقل والنقل 

مجموع الفتاوى 

المستدرك على المجموع الفتاوى 

جامع المسائل والرسائل 


A 'karshe Ina mana nasiha da ababe kamar haka : 


1. Ka sani cewa koyon ilimin Addini ibadane , don haka ka kyautata niyyarka , kuma ka inganta hanyar nemanka gareshi .


2. Ka yi haquri da talauci da fatara a wannan harkar da ka za'bawa kanka ; zaka yi fama da talauci , zaka rasa abokan hul'da , zaka yi fama da 'yan tsurku , duka wannan jarabawace gareka , ka jajirce akan abunda yake gabanka , yin haqurin samun ladane gareka , kuma daukakane gareka awurin wanda kake yi don shi .


3. Ba lallai bane ka samu cikin abokananka Wanda zai kama turba irin wannan ; to ka da ka yarda rashin samun abokin tafiya ya darzar da kai daga kaiwa kamala .


4. Kada ka yarda ka shagaltu da harkan shugabnci ko ya yake , ka haqura da shiga harkoki na jama'a domin ka samu ka tsayarwa da jama'ar wajibin da suka gagara tsayar da shi . 


 5. Kada ka yarda ka kar'bi malumtarwar da mutane suke maka , idan ka ru'du da hakan to lallai ka jahilci kanka , kuma baka cancanci hanyar da kake raya cewa ita kake bi ba .


7 . Ka sanya tsoron Allah ya zama jagoranka , ka zama Mai yawan ibada da 'kas'kantar da kai zuwa ga Allah , ka ke'bewa kanka wani lokaci da zaka ringa ganawa da mahaliccinka kana bijiro masa da buqatunka .


8. Ka zama Mai wadatan zuci , ka ringa yarda da ka'dan , kada ka yarda ka zama makwa'daici , Kada ka bada fuskarka ga masu abun duniya .


9. Ka nisanci alaqa da masu ku'di da 'yan Boko , Kada ka yarda wani mai wadata ya gayyaceka gidansa , ka yi haquri da talaucin da kake ciki Kada ka kuskura ka amshi ku'dinsa . Ka da ka amshi wani abun duniya sai daga hannun Wanda kuke harka iri 'daya . Mai ku'di mara ilimi da addini ko ciki 'daya Ku ka fito da shi to ka tsoraceshi kada ka saki jiki da shi . 


10 . Ka wadatu da kanka wurin neman abun rayuwarka , idan zai yiwu kar ka zama aqarqashin wani awurin samun abun rayuwarka .


11. Idan Al'amura sun yi maka zafi , ka koma cikin littattafan da suka rubuta tarihin Malaman Hadisi , acikinsu akwai lallashi da 'karfafawa ga wanda ya kama wannan hanya . 


12. Kar ka auri mace sai wacce Ku ka dace a manufa da tafarki , ko kuma wacce tafi son wannan tafarki sama da yanda take Sonka .


13. Idan kanaso ka fahimci haqiqanin addinin Musulunci bai 'daya , to ka lazimci Littattafan Shaikhul Muhaqqiqin Ibnu Taimiyyah .

14. Ka zama Mai amfanar da Al'ummar da kake rayuwa acikinta daidai gwargwado , ba tare da ka shagaltu ba da abunda zai raunana ingancin hanyar da kake kanta ba.

15. Ka karance dukkan littattafan Allamah Alwallawy , saboda dukkansu littattafaine na ta'asili daga kowane fanni , Su kuma manya_manyan littattafansa kamar sharhohinsa ga littattafan Hadisi zaka amfana da su wurin fahimtar wasu kura_kurai da Shaukany ya afka acikin wasu mabahis na ilimi , saboda yanda Shi Shaikh Wallawin ya yi ta ta'aqqubin Shaukanin acikin wasu mabahis na ilimi , musamman acikin wagegen Sharhinsa na Sunanun Nasa'iy ( ذخيرة العقبى )


Na rubuta wannan nasiha ne ba don ni na siffantu da dukkan abunda na zayyana ba , a'a na yi hakan ne domin fa'dakarwa gareni a ke'be , da kuma sauran 'yan uwana a game , don haka wannan rubutu da na yi wa'azine gareni wanda duk lokacin da na tuna da Shi zai farkar da ni ya dawo da ni hayyacina . 

Allah ya yafe mana .


 فكن رجلا رجله في الثرى ** وهامة همته في الثريا

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter