Subscribe Our Channel

 Hadisin Muslim a kan Makomar Mahaifin Annabi (saw)


Hadisi ya tabbata cikin Sahihu Muslim kamar haka ya ce:

حدثنا أبو بكر بن أبي شيبة، حدثنا عفان، حدثنا حماد بن سلمة، عن ثابت، عن أنس، أن رجلا قال: يا رسول الله، أين أبي؟ قال: «في النار»، فلما قفى دعاه، فقال: «إن أبي وأباك في النار»

صحيح مسلم (1/ 191)


Daga Anas ɗan Malik (ra) ya ce: Wani mutum ya zo wajen Annabi (saw) ya ce: Ina Babana yake?

Sai Annabi (saw) ya ce: "Yana wuta". Yayin da ya juya baya zai tafi sai Annabi (saw) ya kira shi, ya ce masa: "Babana da babanka suna wuta".


Wannan Hadisi tun zamanin Annabi (saw) ake tabbatar da shi tsawon ƙarni tara, ba a san wani cikin magabata da Malaman Hadisi da ya soki ingancinsa ba, har sai da Hafiz Suyuɗiy ya zo ya soki Hadisin, wanda ya rasu ne a farkon ƙarni na goma bayan hijira. Wannan yake nuna maka cewa; sukar Hadisin wani abu ne fararre.


Waɗanda za a lura da maganarsu cikin waɗanda ba sa yin aiki da wannan Hadisi sun kasu kashi biyu:


1- Masu ƙaryata Hadisin ta hanyar magana a kan Isnadinsa, in da suke raya cewa: -wai- Hammadu bn Salamah mai rauni ne, kuma -wai- yana da wani Agola da yake yi masa cushe a cikin littafinsa. To wannan duka ba gaskiya ba ne. A can baya na taɓa yin tsokaci a kan wannar ƙarya, ga inda za a samu bayani:


https://www.facebook.com/amyuguda/posts/1497871283609897


2- Masu iƙirarin cewa: -wai- Hadisin ya saɓa ma Ayoyin Alƙur'ani, saboda Iyayen Annabi (saw) suna cikin "Ahlul Fatra" (waɗanda ba su riski wani Manzo ko Annabi ba).


To su kashi na farko ba za mu waiwaice su ba, saboda hujjarsu mai matuƙar rauni ce, kai hasali ma maganar Agolan Hammad bn Salama ƙarya ce tsagwaranta.

Don haka za mu yi nazari ne a kan masu kafa hujja da Ayoyin "Ahlul Fatra", don su ture Hadisin daga ma'anarsa.


Lallai ƙa'ida ce tabbatacciya a Shari'a cewa; Azaba ta Duniya ko ta Lahira tana kasancewa bayan aiko Manzanni, bayan tsayar da hujja wa bayi.

To amma inda matsalar take shi ne rashin fahimta da mutane suke yi ga Hadisan da suke raya cewa; sun saɓa wannar ƙa'ida. Duk da cewa; an samu Hadisai da dama da suka zo da tabbatar da yin azaba ga wasu cikin "Ahlul Fatra".


Wannan ya sa Malamai suka yi saɓani a kan "Ahlul Fatra", zuwa ra'ayoyi kamar haka:


1- Waɗanda suka ce kwata - kwata "Ahlul Fatra" ba za a yi musu azaba ba. Su waɗannan sun kasu kashi biyu:


(1) Waɗanda suka ce: za a yi azaba ne kawai ga waɗanda aka ambace su a cikin Hadisai, amma Allah ne kawai ya san dalilin azabtar da su.


(2) Waɗanda suka ce: Hadisan "Ahaad" ne, ba za a kafa hujja da su ba.

To ka ga wannan ra'ayi ne na kuskure, ka ce: Hadisi "Ahaad" ba za a kafa hujja da shi ba. Kuma hasali ma Hadisai a wannan babi na azaba ma wasu daga cikin "Ahlul Fatra", wadanda aka kira sunayensu a cikin Hadisan, sun zo da yawan da sun wuce a kira su da "Ahaad", sai dai "Mustafidhah".


2- Sai kuma Malaman da suka tafi a kan ra'ayin cewa: "Ahlul Fatra" ma za a yi musu azaba. Inda suka bi hanyoyi biyu wajen daidaita tsakanin Hadisan da suka zo da bayanin yin azabar da kuma waccar ƙa'ida da ta gabata, mai cewa: "Allah ba zai yi azaba ta Duniya ko a Lahira ga bawa ba sai ya aiko masa Manzo, bayan ya tsayar masa da hujja". Ga su kamar haka:


A- Suka ce: waɗanda aka ambace su a cikin Hadisan aka ce suna wuta, duk da cewa suna cikin "Ahlul Fatra", to lallai saƙon Allah ya same su, sun ji labarin saƙon da Manzon da ya gabata ya zo da shi. Daga cikin waɗanda suka tabbatar da haka akwai Imam al-Nawawiy inda yake sharhin Hadisin Mahaifin Annabi (saw) a cikin Sharhin Muslim sai ya ce:

"وفيه أن من مات في الفترة على ما كانت عليه العرب من عبادة الأوثان فهو من أهل النار وليس هذا مؤاخذة قبل بلوغ الدعوة فإن هؤلاء كانت قد بلغتهم دعوة إبراهيم وغيره من الأنبياء صلوات الله تعالى وسلامه عليهم".

شرح النووي على مسلم (3/ 79)


"A cikin Hadisin akwai bayanin cewa; duk wanda ya mutu a "Fatra" (tsakanin Manzanni biyu), ya mutu bisa abin da Larabawa suke kai na bautar gumaka to shi yana cikin ƴan wuta. Kuma wannan ba ya nuna Allah ya kama shi ba tare da aiko masa Manzo ba, a'a, lallai waɗannan saƙon Annabi Ibrahim (as) da wasunsa cikin Annabawa (as) ya same su".


To a nan sai Imamu al-Nawawiy ya tabbatar da Hadisin cewa; Mahaifin Annabi (saw) yana wuta, saboda ya mutu a kan Addinin Larabawa a wancan lokacin na bautar gumaka, alhali da'awar Annabi Ibrahim (as) ta riske su.


Kai, har ya kai ga Ibnu Aɗiyya yana ganin cewa; su Ƙuraishawa ba sa cikin "Ahlul Fatra", inda ya faɗi a cikin Tafsirinsa ya ce:

"أما صاحب الفترة فليس ككافر قريش قبل النبي صلى الله عليه وسلم لأن كفار قريش وغيرهم ممن علم وسمع عن نبوة ورسالة في أقطار الأرض فليس بصاحب فترة، والنبي صلى الله عليه وسلم قد قال: "أبي وأبوك في النار"، ورأى عمرو بن لحي في النار إلى غير هذا مما يطول ذكره، وأما صاحب الفترة يفرض أنه آدمي لم يطرأ إليه أن الله تعالى بعث رسولا ولا دعا إلى دين وهذا قليل الوجود".

المحرر الوجيز في تفسير الكتاب العزيز لابن عطية (4/ 72)


A nan sai yake tabbatar da cewa; Ƙuraishawa ba "Ahlul Fatra" ba ne, sai ya kafa hujja da Hadisin Muslim na makomar Mahaifin Annabi (saw), da Amru bn Luhayyi da sauransu. Inda ya nuna cewa: "Ahlul Fatra" su ne waɗanda kwata - kwata ba su san da cewa Allah ya aiko wani Manzo da wani saƙo ba, ba su taɓa jin labarin Addinin Allah ba. Kuma waɗannan mutane ne ƴan kalilan.


B- Wasu Malaman kuma suka ce: waɗannan Hadisai da suka zo da bayanin azaba ma wasu mutane, alahli ana ɗaukarsu a matsayin "Ahlul Fatra", su haka ta faru da su ne saboda ba za su ci jarabawan da za a yi musu a ranar Lahira ba, wanda a dalilin haka za su shiga wuta. Don haka irin waɗannan ne Allah ya sanar da Annabi (saw) su, har ya ambace su cewa; suna wuta.


Lallai akwai Hadisai da suka zo suka tabbatar da cewa; a ranar Lahira a filin hisabi Allah zai yi jarabawa ma wasu mutane, wanda ya ci jarabawan zai shiga Aljanna, wanda kuma bai ci ba zai shiga wuta.


Wannan shi ne ra'ayin Salaf da manyan Malamai masu yawa game da "Ahlul Fatra", cewa; lallai za a yi musu jarabawa a ranar Lahira, wanda ya ci ya tsira, wanda ya fadi kuma sai wuta. Daga cikin Malaman akwai irin su Abul Hassan al-Ash'ariy, Imam al-Baihaƙiy, Ibnu Kasir, Ibnu Hajar da sauransu. Ibnu Hajar ya ce:

"وقد صحت مسألة الامتحان في حق المجنون ومن مات في الفترة من طرق صحيحة".

فتح الباري لابن حجر (3/ 246)


"Mas'alar yin jarabawa ga mahaukata da "Ahlul Fatra" ta inganta, ta zo a Hadisai da suka zo ta hanyoyi ingantattu".


Wannan shi ne bayani a kan hukuncin "Ahlul Fatra".


To a nan akwai kuskuren fahimta da ake yi, inda mutane suke zaton cewa; idan an ce: "Ahlul Fatra" sai su ɗauka su ne kawai waɗanda ba su zo a zamanin wani Manzo ko Annabi ba, alhali akwai waɗanda suka rayu a tsakanin zamunan Manzanni guda biyu, amma kuma sun samu labarin da'awar Manzon da ya gabace su. Gargaɗi da ya zo da shi ya riske su, sun san hujjoji da ya zo da su, to waɗannan fa ba su da wani uzuri, saboda saƙo ya riske su.


Su ne waɗanda Annabi (saw) ya ambaci wasu daga cikinsu a cikin Hadisai, kamar Iyayensa biyu, Kakansa, da irin su Amru bn Luhayyi da sauran waɗanda suke da irin hukuncinsu, duk da cewa sun mutu kafin zuwan Annabi (saw).


Amma akwai waɗanda su kuma ba su riski kowane Annabi ba, kuma ba su ji labarin da'awar kowane Annabi ba, to waɗannan su ne waɗanda suke da uzuri.


Saboda haka, da wannan banbanci ne za ka fahimci cewa; ambaton wane a ce yana wuta to lamari ne na gaibi, ba ka isa ka faɗa ba in ba tare da Nassi ba. Kuma idan Nassi ya zo ba ka isa ka ƙaryata ba, in ka yi haka ka ƙaryata Annabi (saw).


To bayan wannan bayani a kan hukuncin "Ahlul Fatra" sai mu dawo kan Hadisin Muslim na Mahaifin Annabi (saw), sai ya zama cewa: Mahaifin Annabi (saw) yana ɗayan hali biyu:


1) Imma ya zama cewa; labarin saƙon Allah da gargaɗi a kan yi masa shirka ya riske shi.

2) Ko ya zama cewa; lallai gargaɗi da hujja ba su isa gare shi ba.


To a hali na farko, sai ya zama Annabi (saw) ya ba da labarin yana wuta ne saboda rashin karɓan gargaɗi da ƙin bin da'awar Annabi Ibrahim (as) da Manzannin da suka samu labarinsu a bayansa. Kuma wannan shi ne halin da Larabawa a zamanin Jahiliyya, kafin zuwan Annabi (saw) suke ciki.


Miye dalili a kan cewa; hujja ta isa ga Mahaifin Annabi (saw)?

Sai mu ce: Dalili shi ne; wannan Hadisi na Imamu Muslim, kamar yadda Imam al-Nawawiy ya yi bayani a sharhin Hadisin.


Amma in kuma hali na biyu ne to sai ya zama cewa: Allah ya sanar da Annabi (saw) cewa; Mahaifinsa yana wuta ne saboda Allah ya san cewa; a ranar Lahira za a yi masa jarabawa, amma kash! ba zai ci jarabawar ba. A kan haka Ibnu Kasir ya ce:

"قلت: وإخباره صلى الله عليه وسلم عن أبويه وجده عبد المطلب بأنهم من أهل النار، لا ينافي الحديث الوارد عنه من طرق متعددة «أن أهل الفترة والأطفال والمجانين والصم يمتحنون في العرصات يوم القيامة،» كما بسطناه سندا ومتنا في تفسيرنا عند قوله تعالى {وما كنا معذبين حتى نبعث رسولا} [الإسراء: 15] فيكون منهم من يجيب ومنهم من لا يجيب فيكون هؤلاء من جملة من لا يجيب فلا منافاة ولله الحمد والمنة".

البداية والنهاية ط هجر (3/ 429)


"Na ce: Labarin da Annabi (saw) ya bayar game da Iyayensa biyu, da kakansa Abdulmuɗɗalib cewa suna wuta, ba ya kore Hadisin da ya zo ta hanyoyi masu yawa cewa; {"Ahlul Fatra" da yara da mahaukata da kurame za a yi musu jarabawa a filin Ƙiyama}, kamar yadda ya yi bayani a Tafsirinsa a wajen faɗin Allah:

{وما كنا معذبين حتى نبعث رسولا} [الإسراء: 15]

Sai ya kasance a wajen jarabawan a cikinsu akwai waɗanda za su amsa dadai, a cikinsu kuma akwai waɗanda ba za su amsa dadai ba, to waɗannan suna cikin waɗanda ba za su amsa dadai ba, don haka - Alhamdu lillahi - babu cin karo tsakanin Nassoshin".


Saboda haka Hadisan da suka zo da bayanin makomar Mahaifan Annabi (saw) da sauran waɗanda Annabi (saw) ya ambata, waɗanda suka mutu kafin Annabta duka Nassoshi ne, ba za a taɓa gwara su da Ayoyi da suka zo da bayanin cewa; Allah ba ya azaba kafin aiko Manzo da tsayar da hujja ba, saboda asali babu cin karo a tsakaninsu.


Kuma wata ƙa'ida mai muhimmanci da ya kamata mu sani ita ce; duk wanda yake da ilimi da basira a Addini ya san cewa; sharaɗin shiga Aljanna shi ne imani, Allah ya tanadi Aljanna ce kawai ga waɗanda suka yi imani suka yi kyakkyawan aiki. Haka ya tanadi wuta ce ga waɗanda ba su yi imani ba.


Bayan haka ya kamata mu san cewa; lallai Annabi (saw) ya fi mu son iyayensa, saboda son iyaye dabi'a ce da halitta da Allah ya halicci bayi a kanta, don haka ba zai tabbatar wa Mahaifansa abin da Allah bai tabbatar musu ba. Don haka dole mu gaskata Annabi (saw), don ba ya magana da son zuciya. Kuma imani da Annabi (saw) ba ya cika ba tare da gaskata shi ba.


Kuma akwai misalai da a kullum muke ambatawa, musamman Mahaifin Annabi Ibrahim (as), wanda da Nassin Alkur'ani Allah ya tabbatar da cewa yana wuta, duk da cewa Mahaifi ne ga Majidaɗin Allah. Allah ya ce:

{مَا كَانَ لِلنَّبِيِّ وَالَّذِينَ آمَنُوا أَنْ يَسْتَغْفِرُوا لِلْمُشْرِكِينَ وَلَوْ كَانُوا أُولِي قُرْبَى مِنْ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُمْ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ (113) وَمَا كَانَ اسْتِغْفَارُ إِبْرَاهِيمَ لِأَبِيهِ إِلَّا عَنْ مَوْعِدَةٍ وَعَدَهَا إِيَّاهُ فَلَمَّا تَبَيَّنَ لَهُ أَنَّهُ عَدُوٌّ لِلَّهِ تَبَرَّأَ مِنْهُ إِنَّ إِبْرَاهِيمَ لَأَوَّاهٌ حَلِيمٌ (114)} [التوبة: 113، 114]


Ashe kenan dangin Annabawa da zurriyarsu za su iya kasancewa ƴan wuta.


Kuma kasancewar Iyayen Annabi (saw) suna wuta ba za su cutar da Annabi (saw) da komai ba, kamar yadda idan mutum Ubansa kafiri ne ko fasiƙi hakan ba zai cutar da shi komai ba a wajen Allah. A kan haka Imam al-Baihaƙiy yake cewa:

"وكيف لا يكون أبواه وجده بهذه الصفة في الآخرة، وكانوا يعبدون الوثن حتى ماتوا، ولم يدينوا دين عيسى بن مريم عليه السلام؟ وأمرهم لا يقدح في نسب رسول الله، صلى الله عليه وسلم، لأن أنكحة الكفار صحيحة، ألا تراهم يسلمون مع زوجاتهم فلا يلزمهم تجديد العقد، ولا مفارقتهن إذا كان مثله يجوز في الإسلام".

دلائل النبوة للبيهقي محققا (1/ 192 - 193)


"Ta yaya Iyayensa biyu da Kakansa ba za su kasance bisa wannar sifa a Lahira ba, alhali sun kasance suna bauta wa gumaka har suka mutu, kuma ba su bi Addinin Annabi Isa (saw) ba? Lamarinsu (na mutuwa a kan kafirci), ba zai yi suka cikin dangantakar Manzon Allah (saw) ba, saboda auren kafirai ingantacce ne. Shin ba ka gani ba ne, Kafirai suna Muslunta tare da matansu, amma kuma ba a lazimta musu sabunta daura auren, ko a lazimta musu rabuwa da matan nasu, idan irinsa ya halasta a Muslunci".


Saboda haka wajibi ne mu ji tsoron Allah mu bi abin da Annabi (saw) ya zo da shi, mu ajiye soye-soyen zukatanmu.


Daga ƙarshe ina maimaita cewa; Allah ya sani, Ahlus Sunna ba murna ko farin ciki suke yi da wannar mas'ala ba, amma dole ne su yi imani da abin da ya tabbata Annabi (saw) ya faɗe shi. Dole ne su gaskata shi a cikin dukkan maganganunsa.


Kuma duk lokacin da maɓarnata suka tayar da mas'alar, to mu kuma wajibinmu ne mu yi bayani, mu yi musu martani.


Allah ya sa mu dace, ya shiryar da batattu.

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter