Subscribe Our Channel

 DA MA WA YA CE MUKU TAQLIDANCI AKE YI A BABIN AQIDA?


Wani abu da ya ba ni mamakin game da Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi shi ne yadda ake ganinsa a matsayin kwararre a fannin Usulul Fiqh amma yake raya cewa; -wai- "ai ba a Taqlidanci a Aqida, kawai hujja daga Alkur'ani da Sunna ake nema ba wane ya ce ba". Alhali hatta kananan dalibai da suka fahimci Usulul Fiqhi sun san cewa; ana maganar Taqalidanci ne a babin Mas'alolin Ijtihadi kawai, amma mas'alolin da suka tabbata da Nassi ko Ijma'i ba maganar Taqlidanci ake yi a kansu ba, sai dai maganar Bin Nassi ko Ijma'i.


Su kuma Manyan Mas'alolin Addini, musamman na Aqida bin Ijma'in Salaf Magabata ake yi a kansu, ba maganar Taqlidanci ba.


Saboda haka, ya kamata a san cewa; ana Taqlidancin ne a mas'alolin Ijtihadi, wato galibin Mas'alolin Fiqhu, wadanda babu Nassi ko Ijma'i a kansu. Amma mas'alolin Aqida da suke tabbata da Nassi da Ijma'in Salaf biyayya "ITTIBA'IN Salaf" ake yi (bin Mazhabar Salaf), ba maganar Taqlidanci ba.


Wannan ya sa Allah ya yi umurni da bin Salaf Sahabbai ta hanyar yabonsu da yabon wadanda suka bi su da kyautatawa inda ya ce:

{وَالسَّابِقُونَ الْأَوَّلُونَ مِنَ الْمُهَاجِرِينَ وَالْأَنْصَارِ وَالَّذِينَ اتَّبَعُوهُمْ بِإِحْسَانٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ وَأَعَدَّ لَهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي تَحْتَهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ذَلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ } [التوبة: 100]


"Wadanda suka riga yin imani cikin Muhajirun da Ansar, da wadanda suka bi su da kyautatawa, Allah ya yarda da su, su ma sun yarda da shi, kuma ya tanada musu Aljannai da koramai suke gudana a karkashinsu, kuma za su dawwama a cikinsu har abada, wannan rabo ne mai girma". 


Wannar Ayar tana nuni a kan wajabcin bin Sahabbai da kyautatawa.


Haka kuma Annabi (saw) yana magana a kan "Firqatun Najiya" sai ya ce:

إن بني إسرائيل تفرقت على ثنتين وسبعين ملة، وتفترق أمتي على ثلاث وسبعين ملة، كلهم في النار إلا ملة واحدة»، قالوا: ومن هي يا رسول الله؟ قال: «ما أنا عليه وأصحابي»

سنن الترمذي ت شاكر (5/ 26)


"Lallai Banu Isra'ila sun rarrabu zuwa kashi 72, al'ummata kuma za ta rarrabu zuwa kashi 73, dukkansu suna wuta sai kungiya guda daya". Sai suka ce: wacce ce ya Manzon Allah? Sai ya ce: "Abin da nake kai ni da Sahabbaina".


Wannan Hadisi yana nuni a kan bin tafarkin da Annabi (saw) da Sahabbansa suke kai. Binsu ake nufi, kuma ba a kiran hakan da Taqlidanci.


Imamu Abu Hanifa Faqihiy ya ce:

عليك بالأثر وطريقة السلف

ذم الكلام وأهله (5/ 207)


"Ina horonka da bin Hadisai da hanyar Salaf".


Shi ya sa wata magana da ta shahara daga Imamu Malik ya ce:

لن يصلح آخر هذه الأمة إلا بما صلح به أولها


Ma'ana: Abin da ya gyara farkon al'umma shi zai gyara karshenta.

Don haka abin da Salaf suke kai na Aqida shi zai gyara karshen al'umma.


Al- Taimiy ya ce:

وشعار أهل السنة اتباعهم السلف الصالح

الحجة في بيان المحجة (1/ 395)


"Alamar Ahlus Sunna ita ce binsu ga Salaf Magabata na kwarai". 


Saboda haka, Mas'alolin Aqida mas'aloli ne "Thawabit" tabbatattu, wadanda ba sa canzawa, kuma ba sa karban Ijtihadi balle a yi maganar Taqlidanci, saboda mas'aloli ne na imani da kudurtawa, wannan kuwa ba ya canzawa tun farkon al'umma har zuwa karshenta, al'umma (Ahlus Sunnati wal Jama'a) a kan tafarki guda daya take tafiya a Aqida babu canji. Wannan ya sa dukkan manyan mas'alolin Aqida Salaf Magabata farkon al'umma sun yi Ijma'i a kansu, don haka binsu kawai za a yi a kansu ba za a saba musu ba, kuma ba a kiran wannan bin da sunan Taqlidanci ba.


Saboda haka, abin da Ahlus Sunna suke tafiya a kansa game da Aqidar Halittar Alkur'ani, inda suke cewa: ALKUR'ANI MAGANAR ALLAH NE BA HALITTACE BA, bin Ijma'in Salaf suke yi ba magana ce ta Taqlidanci ba.


Imamu Ahmad ya ce:

إجماع العلماء والأئمة المتقدمين على أن القرآن كلام الله غير مخلوق.

طبقات الحنابلة (1/ 172)


"Ijma'in Malamai da A'imma magabata ya kasance a kan cewa; lallai Alkur'ani maganar Allah ne ba halittacce ba".


Wannan Ijma'in Ahlus Sunna suke bi ba Taqlidanci suke yi ma wani ba a kan wannar mas'ala.


Kuma Annabi (saw) ya fadi game da Ijma'in al'umma:

إن الله لا يجمع أمتي - أو قال: أمة محمد صلى الله عليه وسلم - على ضلالة، ويد الله مع الجماعة

سنن الترمذي ت شاكر (4/ 466)


"Lallai Allah ba zai hada al'ummata a kan bata ba, kuma hanun Allah yana kan Jama'a".


Wannan shi yake nuna cewa, duk abin da al'umma ta yi Ijma'i a kansa to ba bata ba ne, gaskiya ne da Shiriya.


Dr. Gumi a matsayinsa na kwararre a fannin Usulul Fiqhi, bai kamata a ce ya manta da matsayin Ijma'i a cikin hujjojin Shari'a ba, da kuma hukuncin wanda ya saba masa. Malaman Usul tun daga kan Imamu Shafi'iy duk sun yi bayanin karfin hujja da Ijma'i yake da shi, inda ya ce:

أمر رسول الله بلزوم جماعة المسلمين مما يحتج به في أن إجماع المسلمين - إن شاء الله - لازم.

الرسالة للشافعي (1/ 403)


"Umurnin da Manzon Allah (saw) ya yi na lazimtar Jama'ar Musulmi yana daga cikin abin da ake kafa hujja da shi a kan cewa; Ijma'in Musulmai yana lazimtar kowa".


Haka Al-Sarakhsiy ya ce:

إن الإجماع موجب للعلم قطعا بمنزلة النص فكما لا يجوز ترك العمل بالنص باعتبار رأي يعترض له لا يجوز مخالفة الإجماع برأي يعترض له بعدما انعقد الإجماع بدليله

أصول السرخسي (1/ 308)


"Lallai Ijma'i yana wajabta ilimi a yanke babu shakka, yana matsayin Nassi ne, kamar yadda bai halasta a bar aiki da Nassi ba, kawai saboda wani ra'ayin da ya saba masa to haka bai halasta a saba ma Ijma'i saboda wani ra'ayi da ya saba masa ba, bayan Ijma'in ya kullu bisa dalilinsa".


Haka Hujjatul Islam ya ce:

إذا اتفقت كلمة الأمة ولو في لحظة انعقد الإجماع ووجبت عصمتهم عن الخطأ.

المستصفى (ص: 152)


"Idan kalmar al'umma ta hadu a kan abu ko da cikin kiftawan ido ne to Ijma'in ya kullu, kuma wajibi ne ya zama sun kubuta daga kuskure".


Allah Madaukaki ya yi gargadi game da mai saba Ijma'in Salaf, inda ya ce:

{ وَمَنْ يُشَاقِقِ الرَّسُولَ مِنْ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُ الْهُدَى وَيَتَّبِعْ غَيْرَ سَبِيلِ الْمُؤْمِنِينَ نُوَلِّهِ مَا تَوَلَّى وَنُصْلِهِ جَهَنَّمَ وَسَاءَتْ مَصِيرًا } [النساء: 115]


"Duk wanda ya saba wa Manzon Allah bayan shiriya ta bayyana gare shi, kuma ya bi wata hanya ba hanyar Muminai ba, to za mu jibintar da shi abin da ya jibinta, kuma za mu shigar da shi Jahannama, kuma makomarsa ta munana".


Wannar Ayar gargadi ce ga wanda ya saba Ijma'in Salaf game da Aqidar Halittar Alkur'ani.


Don haka magana a kan Bin Aqidar Salaf ba magana ce ta Taqlidanci ba, magana ce ta bin hanyar Muminan farko, wadanda Allah ya yi gargadi mai tsanani a kan saba musu, kuma ya yi alkawarin sakamako mai girma ga wanda ya bi su.


Saboda haka da wannan za mu fahimci kuskuren Dr. Gumi na yadda yake kokarin takaice Dalilan Aqida a kan abubuwa guda biyu kawai; Alkur'ani da Sunna (Hadisan Annabi), alhali su uku ne:

1- Alkur'ani.

2- Sunna (Hadisan Annabi).

3- Ijma'in Salaf.

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter