Daga Labarun Khawarijawa
Ibnu Jarir ya ruwaito ta hanyar Abu Mikhnaf, cewa; Khawarijawa sun fito daga Basra, sai suka hadu da wani mutum tare da matarsa tana kan jaki, sai suka isa gare shi, suka tsoratar da shi, suka ce: Waye kai?
Ya ce: Abdullahi bn Khabbab Sahabin Annabi (ra).
Sai suka ce: Ba mu labarin Hadisin da Babanka ya ji daga Annabi (saw), sai ya ce:
Babana ya ba ni labari daga Annabi (saw) ya ce:
[إن فتنة تكون، يموت فيها قلب الرجل كما يموت فيها بدنه، يمسي فيها مؤمنا ويصبح فيها كافرا، ويصبح فيها كافرا ويمسي فيها مؤمنا].
((Lallai Fitina za ta kasance, zuciyar mutum za ta mutu kamar yadda gangar jikinsa yake mutuwa, zai wuni a cikin fitinar yana Mumini ya wayi gari yana kafiri, zai wayi gari yana kafiri a cikinta ya wuni a cikinta yana Mumini)).
Sai suka ce: Me za ka ce game da Abubakar (ra) da Umar (ra)?
Sai ya fadi alheri a kansu.
Suka ce: Me za ka fadi game da Usman (ra) da farkon khalifancinsa da karshensa?
Sai ya ce: Yana kan gaskiya a farko da karshen.
Sai suka ce: Me za ka ce a game da Aliyu (ra) kafin TAHKIMI da bayansa?
Sai ya ce: Ya fi ku sanin Allah, ya fi ku kiyaye Addininsa, ya fi ku Basira.
Sai suka ce: Kai mai bin son zuciya ne, sai mun kashe ka. Sai suka daure hanayensa suka tafi da shi tare da matar tasa, alhali tana da ciki.
Har sai da suka isa wajen wata bishiyar Dabino, sai dan dabino daya ya fado, sai daya daga cikinsu ya dauka ya kai bakinsa. Sai dayansu ya ce: Ka ci Haram. Sai ya tofar da shi.
Sai aladen wani kafirin Amana ya zo wucewa, sai ya sare shi da takwabinsa. Sai suka ce masa wannan barna ne a bayan kasa. Sai suka je wajen mai aladen suka ba shi hakuri ya yafe musu.
Da Abdullahi bn Khabbab (ra) ya ga haka sai ya ce musu: Idan da ku masu gaskiya ne game da abin da na gani a tare da ku na tsantseni game da cin dabinon da ba naku ba, da kuma kashe aladen kafirin amana, to ni ba ni da laifi, saboda ni Musulmi ne, ban taba wani babban laifi a Muslunci ba, kuma kun aminta da ni.
Sai suka ce: Kar ka tsorata.
Sai suka tafi da shi, suka kwantar da shi, suka yi masa yankan rago!
Sai suka nufi matarsa, ta ce: Ni mace ce, ba za ku ji tsoron Allah a kaina ba?!
Sai suka farka cikinta...
Bayan labari ya isa ga Aliyu (ra) sai ya daura damarar yakarsu!
تاريخ الطبري (5/ 81)
Kissa ta biyu:
Quraza bn Ka'ab al-Ansariy ya aika wa Aliyu (ra) wasika, a ciki yake ba shi labarin cewa:
Mayakan Khawarijawa sun fito daga Kufa sun fiskanci wani waje mai suna Nafar, sai Khawarijawan suka hadu da wani Mutum suka ce masa: Kai Musulmi ne ko kafiri?
Sai ya ce: A'a, Ni Musulmi ne.
Sai suka ce: Me za ka ce a game da Aliyu (ra)?
Sai ya ce: Ba komai sai alheri, shi ne Khalifa Amirul Muminina, shugaban al'umma.
Sai suka ce: Ka kafirta ya makiyin Allah!
Sai kuwa wasu gungu daga cikinsu suka yi kansa, suka yi gunduwa-gunduwa da shi.
A tare da shi sun samu wani mutum kafirin Amana, sai suka ce masa: Kai waye?
Sai ya ce: Ni kafirin Amana ne.
Sai suka ce: Wannan kam babu halin mu taba shi.
Sai wannan kafirin Amana ya je ya ba da labarin abin da ya faru.
تاريخ الطبري (5/ 117)
Kissa ta uku:
Mubarrid ya hakaito a cikin "al-Kamil":
Wasil bn Ada'u - shugaban Mu'utazilawa - ya tafo tare da abokan tafiyarsa, sai suka hango Khawarijawa. Sai Wasil ya ce musu: Kar kowa ya yi magana, ku bar ni da su.
Da suka isa wurinsu sai suka tambaye su: Kai da abokanka, su waye?
Sai ya ce: Mushrikai ne masu neman aminci don su ji maganar Allah, don su fahimci dokokinsa.
Sai Khawarijawan suka ce: Mun ba ku amincin.
Sai ya ce: To ku koyar da mu.
Sai suka fara koyar da su hukunce-hukuncensu irin na Khawarijanci.
Shi kuma Wasil sai cewa yake yi: Na fahimta ni da jama'ata.
Sai suka ce: To ku wuce, ku 'yan'uwanmu ne.
Sai ya ce: Amman ba haka ba, ai Allah ya ce:
{وَإِنْ أَحَدٌ مِنَ الْمُشْرِكِينَ اسْتَجَارَكَ فَأَجِرْهُ حَتَّى يَسْمَعَ كَلَامَ اللَّهِ ثُمَّ أَبْلِغْهُ مَأْمَنَهُ} [التوبة: 6]
{Idan wani daga cikin Mushrikai ya nemi amincinka to ka ba shi aminci, don ya ji maganar Allah, sa'annan kuma ka isar da shi wajen da zai tsira ya aminta}.
Don haka sai ku isar da mu har inda za su samu tsaro da aminci.
Sai wannan ya kalli wannan, sai suka ce: Lallai haka ne. Sai suka tafi da su gaba daya har suka wucar da su, suka isa da su inda za su samu tsaro da aminci.
الكامل في اللغة والأدب (3/ 122)
Wadannan wasu kissoshi ne guda uku na labarun Khawarijawa, masu cike da ababen mamaki. Kuma a cikinsu Siffofin Khawarijawan da Annabi (saw) ya ba da labari sun bayyana a fili.
Wadanne Siffofin za ka iya fada mana daga wadannan kissoshi?!