DAGA INA MATSALAR TAKE ?(9)
A rubutunmu fitowa ta takwas , mun fara kawo wani sashe na zantukan almajiran Shehu Inyass , inda wani daga cikin almajiransa ya allantar da shi 'karara , kuma shima Inyass 'din ya tabbatar da shi akan haka .
A yau zamu cigaba da kawo misalai daga bakunan almajiran Inyass , inda suke allantar da shi ta hanyar danganta masa ma'anoni na allantaka da ubangijintaka , har da ma ganin cewa kowa ma Inyass ne ( Alha'ki'katul Ibrahimiyyah ) .
Daga cikin manyan misalai akan wannan kafircin , akwai almajirin Ibrahim Inyass mai suna " Abubakar bun Abdullah Alkaulakhy " , ya tabbatar da allantakar Inyass awurare mabanbanta acikin 'kasidarsa " saba'ikuz zahab " ; ta yanda yake tabbatar masa da ma'anoni na allantaka da ubangijintaka , kamar dai yanda shima Inyass yake 'kudurtawa ga Shehu Tijjani kamar yanda muka gabatar a baya .
Wannan Mutumin yana cewa gameda Inyass :
" Ya kai abokina , idan al'amura masu tsanani sun auko maka zasu halakaka , to ka nemi kariya awurin Halilu ( Inyass ) , lallai yalwa zata zo maka .
Ka baiwa kowa sama da abunda ya ro'keka ( Inyass ) , abun mamaki , ya kai Halilu ( Inyass) kyauta daga gareka take "
"وإذا ما دهتك صاح خطوب ## فاستجر بالخليل يأت الرخاء
كل أحد وهبته فوق سؤل ## عجبا يا خليل منك السخاء "
( سبائك الذهب والفضة ، ٤)
A wani wurin kuma yake cewa : " Ya kai wanda yake nufin samun wasu al'amura wa'danda samunsu ya cutura , ka nemi agaji a wurin baban Isha'ka ( Inyas ) zaka samu bu'katunka "
" يا من يريد أمورا عز مدركها ## فاستنجد بأبي إسحاق تغتنما "
( سبائك الذهب والفضة ، ١١)
A wani wurin kuma yake cewa : " sau dayawa ka bada agaji ( Inyass ) , sau dayawa ka malalo ni'imomi , sau dayawa ka yaye damuwa , sau dayawa ka yi baiwa arzi'ki ga dukkan mai kwa'dayi wanda aka tsorata "
" كم أغثت وكم أفضت وكم كشف ## ت وكم وهبت لكل راج مرعد "
( سبائك الذهب والفضة ، ٢٣)
Wa'dannan maganganu na wannan mutumi suna nuni akan yanda yake 'kudurce allantakar Inyass ; ta yanda yake da'war cewa Inyass shine yake komai , kuma shine bai biyan bu'katun halittu .
A wani wurin ma ya fito 'karara ya tabbar da cewa shi bawan Inyass ne , kuma shi yake bautamawa , ga nan maganarsa kamar haka :
" Ga Abubakar nan ( shine dai mai maganar , ma'abocin 'kasidar )ya kai mai agazawa , yana neman arzi'kinka , don haka kai min baiwa na saduwa da kai , kuma kai min baiwar ni'imominka .
Kaine kake sanin dukkan ababen da nake 'boyewa da wa'danda nake bayyanawa , nine 'dan 'karamin bawanka , wanda ake 'kirgashi daga cikin mahidimta "
" هذا أبوبكر يا غوث بين يدي ## علياك فامنن بالوصل والنعما
وأنت تدري الذي أخفي وأعلنه ## أنا عبيدك معدود من الخدماء
( سبائك الذهب ، ٩)
A wani wurin kuma ya ce : Inyas shine zuciyan halittu , kuma shine hasken halittu , kuma shine samuwar dukkan halittu , albarkatun Inyass sune rayukan da suka bayyana ga jikkuna .
Ga nan maganarsa kamar haka :
" قلب الوجود ونوره ووجوده ## أمداده روح بدت بتجسيم "
( سبائك الذهب والفضة ، ٢٦)
A wani wurin kuma ya tabbatar da cewa Inyass shine wanda yake amsawa masu bauta addu'o'insu , kuma hakan shine sha'aninsa a kowane lokaci ; duk lokacin da wani ya yi addu'a to Inyass yake ro'ko kuma shine zai amsa addu'ar .
Wato ya 'dauke ma'anar fa'din Allah ma'daukaki game da kansa inda yake cewa : shine yake amsa addu'ar mai addu'a a duk sanda ya yi addu'ar :
"و إذا سألك عبادي عني فإني قريب أجيب دعوة الداع إذا دعان . فاليستجيبوا لي وليؤمنوا بي لعلهم يرشدون "
sai wannan mugun mutumin ya jingina ma'anar wannan ayar ga Inyass , saboda shi awurinsa Inyass ne Allah !!
Ga nan maganarsa :
وامدح الكولخي لا تتربص ## ريب دهر فلا خلاه الثناء
وتأمل معناه حتى تراه ## فيك يبدو كما تبدو الذكاء
وادعه يستجب إذ هو دأبا ## سامع ما أتاه منك نداء "
"Ka yabi 'Dan Kaulaha ( Inyass) , kada ka tsaya 'bata lokaci , shi yabo baya rabuwa da shi .
Ka lura da ha'ki'kaninsa har ka ringa ganinsa yana bayyana acikinka kamar yanda rana take haskakawa .
Ka yi addu'a gareshi zai amsa maka , saboda shi a kowane lokaci mai amsa addu'a ne matu'kar ka yi addu'a gareshi "
( سبائك الذهب ، ٤)
Daga cikin wa'danda suke allantar da Inyass cikin almajiransa akwai shehu Ahmad Tijjani Usman Kano ; wannan Mutumin yana allantar da inyass , har ma yana ganin cewa komai ma Inyass ne ( Alha'ki'katul Ibrahimiyyah )
Daga cikin suratansa na yabo da yayi akan Inyaas , Wanda ya cikashi ma'kil da maganganu na zanda'ka da shirka , akwai inda yake cewa :
" Inyas shine yake a sama na , kuma shine a 'kar'kashi na , shine a baya na , kuma shine a gaba na .
Shine mamu na ( masallaci bayan limami ) , kuma shine mai sallah shi ka'daina , shine zakka na , kuma azumina .
Shine ni gaba 'dayana , kuma shine 'bangarorina , shine sallah ta , kuma shine limami na .
Shine ramdana na , kuma shine idi na , kuma shine hajji na .
Babu abunda zaka gani face wannan abun Inyass ne , sawa'un abun yana nesa ne ko yana kusa "
" وهو فوقي وهو تحتي ## وورائي وأمامي
وهو مأمومي وفذي ## وزكاتي وصيامي
وهو كلي وهو جزئي ## وصلاتي وإمامي
وهو رمضاني وعيدي ## وهو حجي في الاحرام
لا ترى شيئا سواه ## في قصي أو لزام "
( مرواق العشاق في مدح أبي إسحاق )
Wa'dannan maganganu na kafirci daga bakunan almajiran Inyass , dukkansu suna nuna yanda su mutanen suke allantar da Inyass , kamar yanda shima Inyass 'din yake allantar da Tijjani .
A rubutunmu na gaba zamu kawo bayani daga malaman Tijjaniyyah inda suke tabbatar fifikon shehinnai akan manzon Allah ( S.a.w )