Subscribe Our Channel

 DAGA INA MATSALAR TAKE ? (8) 


A rubutunmu na fitowa ta biyar da ta shida da ta bakwai , mun kawo maganganun Shehu Inyass inda yake wuce iyaka akan Shehu Tijjani ta yanda yake allantar da shi , da ma 'kudurta cewa komai ma Shehu Tijjani ne .


A yau zamu kawo maganganun almajiran Shehu Inyass , inda suma suke allantar da shi , har ma wasu suke 'kudurta cewa komai ma Inyass ne ( ALHA'K'KATUL IBRAHIMIYYAH ) , kamar dai yanda shima Inyass 'din ya yi ga Shehu Tijjani .


Shehu Inyass shi dakansa _ kafin almajiransa _ yana 'kudurta cewa halittu gaba'dayansu suna 'kar'kashin gudanarwarsa ne ; shine yake hukuncin da yaga dama acikin halittu , kamar yanda masu zurfafawa suke 'kudurcewa ga waliyyai . 


Yana cewa :


"قد خصني بالعلم و التصريف ## إن قلت كن يكن بلا تسويف " 


"ha'ki'ka Allah ya ke'beni da wani ilimi na musamman , kuma ya ke'beni da ikon gudanar da halittu ; ta yanda duk abunda na ce da shi : ya faru , to zai faru nan take ba tare da 'bata lokaci ba "


( جامع رحلات الشيخ إبراهيم نياس ، الرحلة الكناكرية ) 


Wani sashe na Almajiran Inyass sun 'kudurce dangantamasa allantaka tun yana raye , kuma suka bayyana hakan acikin rubuce_ rubucensu , _ kamar yanda shima ya 'kudurce game Shehu Tijjani _ kuma shi Inyass 'din bai musu inkari ba , a'a sai dai ma ya 'karfafasu akan haka .


Misali akan haka shine ; 'kasidar da almajirin Inyass ya rubuta Shehu Ilyasu Alwaly ,wacce acikinta ya dangantawa Inyass allantaka 'karara ; ta yanda ya jingina masa rainon halittu , da kuma neman kusanci zuwa gareshi da mafi girman nau'uka na bauta , da tabbatar da cewa dukkan halittu shi suke bautamawa a lokacin da suke bauta na neman bu'katu , kuma tabbatar da cewa Allah ya bayyana acikin jikin Inyass . 


Ga nan maganarsa kamar haka :


" فعليك يا برهام ربك قد وفى ## ذاتا و وصفا ثم زاد نعيما 


لولا قيامك عابدا و خليفة ## ليصير هذا الكون منه عديما 


ما إن دعا أحد بأي مكانه ## إلا و كنت مجيبه و عليما 


" Akanka ne Allah ya cika , ya kai Barhama ( Inyass) ta fuskar zati , da sifa , kuma ya 'kara wasu ni'imomi .


Ba don tsayuwarka ba a matsayin mai bauta , kuma wanda yake a madadin Allah , to da wannan duniyar gaba 'dayanta ta rushe an rasata .


Aduk inda wani bawa ya yi addu'a , to kaine mai amsa masa kuma kaine masani akan komai " 


( كشف الغمة بالاستغاثة بصاحب الفيضة ،٦)


Acikin dai wannan 'Kasida wannan Almajiri nasa yake cewa a wani wurin :


" Kaine za'ba'b'be ( Inyass ) , kaine ka kwararo albarkatu wa'danda basu gushe ba suna game dukkan halittu saboda jin'kanka .


Ga ka nan ya kai kundi , ka kai 'ku'dubi mafi rinjaye , kaine ka mallaki komai ta fuskar hukunci da gudanarwa a matsayinka na shugaba .


Shine ( Inyass ) wanda yake tseratar da wanda ya nutse cikin damuwa , kuma bai gusheba yana mai rayar da zuciyoyi kuma yana bada agaji ga wanda aka zalunta " 


" أنت الصفي أفضت فيضا لم تزل ## بركاته عم الورى ترحيما 


ها أنت يا دستور يا قطب الأجل ## حكما و تصريفا ملكت زعيما 


هو من ينجي غريق هم لم يزل ## يحي القلوب و ينجد المظلوما "


 A wani wurin kuma ya ce : Ya kai shugabana ( Inyass ) , dukkan al'amura baki 'dayansu naka ne ; wa'danda ake ganinsu da wa'danda suke fake , kuma dukkan ilmomi daga gareka ake samunsu " 


"لك سيدي كل الأمور جميعها ## عينا و غيبا منك كل فهوما " 


A wani wuri kuma ya ce : Bani da wata dabara ko 'karfi wurin dunku'dewa kaina wata musiba , kaine mai hukunci cikin dukkan abunda nake fata "


"لا حول لي دفعا دفعا ولا لي قوة ## في كل أرجوه كنت حكيما "


(كشف الغمة ، ٧)


Duk irin kalmomi na kafirci da wannan 'kasida ta 'kunsa ; ta yanda marubucinta yake tabbatar da allantakar Inyass ta hanyar danganta masa Ubangijintaka , da ma'anonin allantaka , amma Ibrahim Inyass da yazo ta'karizin 'kasidar bai kushe abunda almajirinsa ya danganta masa ba na allantaka , a'a 'karfafashi ya yi akan ma'ganganunsa na kafirci _ a shari'a _ kuma ya kwa'daitar akan karanta 'kasidar har ma ya yi al'kawari cewa dukkan wanda ya karanta 'kasidar to za'a yafemasa zunubansa , kuma dukkan wanda ya doge akan karantata to zai zama daga cikin ke'bantattunsa .


Ga nan maganarsa daga bakin almajirin nasa mai 'kasidar :


" أول من قرظه حين وقف عليه وتصفحه مولانا و عمدتنا ووسيلتنا إلى الله القطب الرباني والغوث الصمداني الفرد الجامع ما للأنبياء والأولياء من أولهم إلى آخرهم سيدنا و حجتنا الشيخ إبراهيم بن الشيخ الحاج عبد الله الكولخي رضي الله عنه و عنا به ، و أماتنا على عهده و صحبته ، آمين .


فقال : الحمد لله ، من قرأه مرة غفرت ذنوبه ، ومن دام عليه كان أخص الخواص أهل المراقبة ، فشد يدك عليه ، وقد أذنت في استعماله و إعطائه و الظن بالله جميل ، لا أحرمنا الله ، والسلام .

إبراهيم بن الحاج عبد الله التجاني الكولخي " 


( كشف الغمة ، ١٠)


A rubutumu na gaba zamu cigaba da kawo maganganun Almajiransa inda suke allantar da shi kamar yanda shima ya allantar da Tiijani .

 
Follow Admin On Twitter Ibrahim Yunusa Abu-ammar
Subscribed Our Newsletter