DAGA INA MATSALAR TAKE ?(7)
A rubutunmu na baya a wannan matashiya mun yi bayanin yanda Shehu Inyass yake 'kudurta cewa Shehu Tijjani shine Allahnsa kuma shi yake bautamawa ta hanyar kawo maganganunsa daga littattafansa . Ayau kuma zamu yi bayanin yanda yake wuce iyaka matu'ka ta yanda yake 'kudurce cewa Shehu Tijjani yana sauka acikin jikinsa ta yanda shima yake riki'dewa ya zama Shehu Tijjani , da ma 'kudurce cewa komai ma Shehu Tijjani ne , kamar dai yanda suke fa'di dangane ga Allah ; cewa yana sauka acikin jikin halittu , da ma cewa komai ma Allah ne !!
Cikin Sufaye masu a'kidar komai Allah an samu wasu daga cikinsu da suka 'kara zurfafawa cikin wannan kafircin ta kai ga suna ganin Annabi Muhammad yana sauka acikin jikin wasu halittu , ko kuma su halittun suna narkewa da 'karewa acikin jikin Annabi Muhammad , daga nan sai halittan shima ya zama Annabi Muhammad , daga nan kuma sai suka 'karawa 'batar tsawo zuwa 'kudurce cewa : komai Annabi Muhammadu ne !!
wannan mummunan kafirci suna kiransa da "ALHA'KI'KATUL MUHAMMADIYYAH "
Shehu Tijjani ya yi bayanin wannan mataki na Sufanci , inda yake cewa :
" Ka sani lallai cikin abunda Allah yake iya halittawa babu abunda ya fi daraja da 'daukaka da kyawo , da kamalan sura sama da surar da ake gani na surorin halittu dukkansu , kuma duk abunda kake gani na surorin halittu ba komai bane face Annabi Muhammad (s.a.w) , dukkan abunda zaka gani na halittu a duniya , na surori da yanayi wa'danda ma'anoninsu da halittarsu suka banbanta , to dukkansu ba komai bane face Annabi Muhammad ( s.a.w) "
" اعلم أنه ليس في الإمكان أشرف وأعلى وأجمل وأكمل من صورة الكون كله ، ولا صورة الكون كله إلا سيدنا محمد صلى الله عليه وسلم ، كل ما تراه في الكون فالصور والأشكال مختلفة المباني و المعاني ، المتحدة الواقعة في جسم واحد ، ما ثَمَّ إلا هو صلى الله عليه و سلم "
( جواهر المعاني ، ١٥٣/٢)
A wani wurin kuma ya ce : " A wani lokaci kuma Waliyyi Arifi yana nutsewa ya 'kare acikin jikin Annabi (s.a.w) , saboda ya fake daga hararo samuwarsa saboda ya 'kare acikin zatin Annabi , to daga nan sai Annabi ya kwararo masa wasu sirrikansa , idan zatinsa ta samu wa'dannan sirrikan , to daga nan waliyyin ba zai 'kara halarto zatinsa ba , sai dai kawai ya ringa halarto zatin Annabi ( saboda ya riki'de ya zama Annabi Muhammad ) "
" وتارة يكون الاستغراق للعارف و الفناء في ذات النبي صلى الله عليه وسلم ، لغيبته عن ذاته في ذات النبي عليه الصلاة والسلام ، فيتدلى له صلى الله عليه وسلم ببعض أسراره ، فإذا كسبت ذاته ذلك السر فلا يشهد ذاته إلا ذات النبي صلى الله عليه وسلم "
( جواهر المعاني ، ١٥٢/٢)
Shehinnan 'dari'kar Tijjaniyya masu allantar da Tijjani sun 'karawa wannan kafircin tsawo ; sai suka 'kara samar da wani mataki na gaba da wancan mataki na komai Annabi Muhamadu , suka sanya masa suna da " ALHA'KI'KATUL AHMADIYYA" ; wato komai Shehu Tijjani .
Shehu Inyass bayan 'kudurcewassa ga allantakar Tijjani , ya 'kara da cewa shima yana narkewa ya 'kare sai ya zama Shehu Tijjani , kai komai ma Shehu Tijjani ne ; babu wani halitta da ba Shehu Tijjani ba .
Ga maganganunsa nan da yake tabbatar da hakan :
Yana cewa : Shehu Tijjani shine ruhina , shine jikina , shine ni gaba 'dayana , shine mai shiryar dani "
" ذاك روحي ذاك جسمي ## ذاك كلي ذاك هادي "
( تحفة أطايب الأنفاس ، ١٢٥)
A wani wurin kuma ya ce : "babu wasu ababe biyu masu kyawo da za su yi ido hu'du face wa'dannan ababen masoyina ne Shehu Tijjani "
" ما تراءا من جمال ## غير محبوبي التجاني "
( تحفة أطايب الأنفاس ، ١٢٩)
A wani wuri kuma ya ce : Zatin Shehu Tijjani ta shafe zatina , kuma sifofinsa sun zama sifofina , don haka babu ni gaba 'daya na .
Don haka na zama nine wannan masoyin ( Shehu Tijjani ) a duk sanda na 'kare acikin jikinsa , kuma na rantse wannan shine abun nemana .
Don haka sai wannan 'ku'dubi maka'daici ( Shehu Tijjani ) ya bayyana ina ganinsa shine tsantsan zatina , kuma wannan gaskiya ne babu shakka "
" محقت ذات الشيخ ذاتي و أوصا ## ف له أوصافي فكلي عديم
فأنا ذلك الحبيب متى أف ## نيت فيه وذاك عمري المروم
فتبدى القطب الفريد أراه ## عين عيني ، وذاك حق صميم "
( تحفة أطايب الأنفاس ، ١٠١)
A wani wurin kuma ya ce : Masoyina ( Shehu Tijjani ) shine tsantsan zatina , shine abincina , shine abunshana "
"فعيني عين محبوبي ### و مأكولي و مشروبي "
( تحفة أطايب الأنفاس ، ١٢٠)
A wani wurin kuma ya ce : Duk abunda kake gani _ a zahiri _ sa'banin Shehu Tijjani , to Kamar kawalwalniya ne kawai ( a zahiri ne kake ganin ba Shehu Tijjani bane , amma bisa ha'ki'ka Shehu Tijjaninne )
" ما عدا شيخي إمامي ## كسراب الصحصحان "
( تحفة أطايب الأنفاس ، ١٢٩)
A wani wurin kuma ya ce : " Duk abunda kake gani _a zahiri _ sa'banin Shehu Tijjani , to kawalwalniya ne kawai , babu wani mai rayuwa ( sai Shehu Tijjani ) , kubar wannan magana , ni ba wanda ake 'karyatawa bane "
" سراب سوى هذا الإمام بقيعة ## فلا عائش : كلا ولست مفندا "
( تحفة أطايب الأنفاس ، ٧٧)
Wa'danan zantuka na Inyass duka suna nuna yanda yake da guluwwi mai tsanani akan Shehu Tijjani ; ta yanda bayan ya allantar da shi kuma yake 'kudurce cewa ma bisa ha'ki'ka komai ma Shehu Tijjani ne .
A rubutunmu na gaba zamu Kawo zantukan Almajiran Inyass inda suke allantar da shi kamar yanda shima ya allantar da Shehu Tijjani .